Tana Isa Bata tsaya tunanin komaiba tafara qoqarin kutsawa ciki mutanen dake gurin suka rirriqeta suna cewa Batada hankaline tana ganin gini na zubewa zatashiga...
Qwacewa tayi cikin tsananin kuka tana Kiran baabanta jikinta ba inda baya rawa..
Cikin zafin nama dahiru ya damqota tareda riqeta da qarfi
Ihu take da kuka sosai tanason qwacewa Amma ba qaramin riqo yayi mataba Dan kuwa ayanda take ba cikin hayyacinta ba idan aka saketa zata iya shiga ginin Wanda tuni ya qarasa rugujewa....Ihu tasaki Mai qarfi ganin yanda gaba daya ya qarasa rugujewa kamar ba'ataba dogon giniba agurin.,,
Arikice dahiru ya girgixata Yana Kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali sbd ganin kamar Bata numfashin..
Layla... Layla..ke tashi karki mutu ahannuna..innalillahi
Arikice Raheenatu tafara jijjigata tana Kiran sunanta cikin tsananin kuka Amma Sam ba alamar tanada sauran numfashi...
Cicci6arta sukayi suka koma gefe sbd ruwan saman ya 'dauke mutane sun qara taruwa agurin ana kallon yanda ginin ya zube...
Kallon Raheenatu yayi cikin tsoro yace,
Ke kamata muje chemist idan Bata tashiba to tafiyata zanyi wlh ba ruwana.
Cikin tsananin kuka ta Mike suka kamata suna Isa chemist din hamisu Mai chemist na ganinta yace,
Aa wannan tafi qarfin chemist asibitin zakuje Dan da alama kamar bugawar zuciya ne kamarma ta Dade da mutuwa..
Ehhh,,, dahiru yafada cikin tsananin tashin hankali da tsoro Yana zaro jajayen idanuwansa
Nan Take jikinsa yadau rawa ya kalli Raheenatu Yana cewa,Nayi iya yina saiki 'dora Kuma wlh ka sunana yafito ciki.
Ficewa yayi jiki na rawa Yana sharce gumi duk da sanyin ruwan da aka gama.
Kallon Nur din tayi cikin sabon kuka tace,
Kiyi hakuri Layla nima bansan ya zanyi Miki ba Dan banida wata taimako Kuma.
Miqewa tayi ta fice batareda tabari hamisu Mai chemist ya luraba.
Wani mugun ashar ya sako lokacinda yagama sallamar wani yaga sun gudu sun bar Masa gawa
Ai nantake 'yan hanjinsa suka ka'da Bai tsaya wata wata ba jiki na rawa ya zagayo yasa qarfi ya cicci6eta ya lalla6a yakaita gefen gininsu daya zube sbd duhun magrib yariga yagabato yadawo ya cicci6i Bilal yakai gefenta ya aje yadawowarsa ya rufe chemist dinsa yayi gida.Babu Wanda yakuma kawosu arai sai tsakar dare guraren qarfe uku suka farfado kusan atare sbd sanyin asuba daya sawo Kai dakuma sanyin ruwan da'akayi.
Daqyar ta iya lalabawa ta tashi zaune ta bude idanuwanta da sauri ta rufe sbd ganin a inda suke yashe kan hanya kusada bola.
Da hannu ta lalabo Bilal dake kukan azabar ciwo ahankali ta rungumesa tareda sakin qaramin kuka ahankali tana kiran sunan mahaifinsu,
Sun zama marayu basuda uwa basuda uba basuda kowa dazasu gani ko sukira nasu
Tun adaren da mahaifinsu ya rasu sun Fara shiga garari tunda gasu da kwana gefen bola.Jin kukan azabar da Bilal keyi yasata bude ido ta sake qanqamesa tana basa haquri Dan kuwa raunika ne sosai a jikinsa duk saiya qara 'daga Mata hankali ta birkice.,
Daqyar taga lokacin sallar asuba yayi anyi gari ya 'dan Fara haske takamasa daqyar suka 'dan matsa daga kusada bolar ta samo wani jikakken kwali ta shimfida Masa ta kwantar dashi.
Rawar sanyi yakeyi sosai ta rasa ya zatayi cikin hawaye ta kalli lifayarta data gama tsufa da faffashewa tasa hannu ya farketa biyu ta lullu6esa sauran ta 'dan budeta ta rufe jikinta Wanda Bata rufe dukaba saima taqara fitowa datayi a sadaka yallah dinta.
