Jingina jikin qofar toilet 'din ta jingina tareda zamewa ta durqusa tareda sakin kukan datake dannewa gaban ammy ahankali,
Shesheka takeyi sosai tasa hannu ta rufe bakinta kukan na tsananta.Rarrashin kanta tayi ta miqe ta tsaya gaban mirror tareda kallon fuskarta taga yanda lokaci 'daya tayi jajir.
Wanke fuskar tayi jiki ba qwari ta goge fuskar da towel tareda qara tattaro juriya ta fito.
Har lokacin ammy na zaune bakin gadon ta rafka tagumi da hannuwa biyu takasa miqewa bare ta fita takoma Palo.
Fitowarta yasa ammy 'dagowa ta qura Mata ido ta yanda fuskarta tayi jajir lokaci 'daya har wani fa'dawa fuskarta tayi.
Qofa ta nufa zata fice ganin kallon da ammy ke Mata taji tace,
Layla matuqar Bazaki auri dawood ba aleeya ma bazata auresaba.
Da sauri ta juyo tana kallon ammyn.
Eh wannan nawa hukuncin ne sbd Babu dalilin dazaisa ta auri Wanda baya sonta ko ka'dan 'yar uwarta yakeso.
Dawowa tayi ta zauna murya a karye tace,
Ammy kenan niba 'yar uwar aleeya bace.
Me kike fada layla??har abada aleeya Yar uwarkice.
Idan har 'yar uwatace Ni 'yarkice to ammy bazaki hanata samun abinda takesoba sbd ni bansamu ba.,
Ammy mezamu fadawa su Abba idan kikace aleeya bazata auri dawood ba?
Kowa zaisan abinda yake faruwa daganan za'a iya samun rashin fahimta daga wasu Kinga qarshe dai abinda ake gujewar zai faru Kuma dukkanin 'yayanki zasu rasa farin cikinsu hakan zai ta6a zuciyarki da kwanciyar hankalin gidannan,
Ina roqonki ammy daki Bari aleeya tasamu farin ciki da Wanda takeso.....Katseta tayi cikin 'dan 'daga murya da cewa,
Layla kin kasa ganewa farin cikin ne bazata samuba har abada idan ta auresa.,Kuma me zai faru idan dawood ya ganki amatsayin 'yar uwarta kina tunanin zaiyi shiru ne?
Numfashi Mai ciwo ta sauke murya a karye tace,
Bazai qara ganinaba ammy sbd na yanke duk wata alaqa dashi saita wadda zamu Fara yanxu bayan aurnsa da aleeya amatsayin 'yar uwar matarsa.
Ammy kiyimin wannan alqawarin na bazaki fadawa aleeya ba.
Me kike cewane Layla?""sukaji anfada daga bakin qofa.
Itakadaice ta juya da sauri tana qoqarin danne halinda dake ciki ganin aleeya a tsaye bakin qofa.
Ammy kuwa miqewa tayi ta fice batareda takalli su duka biyunba sbd zuciyarta na ingizatane ga fadar gskia saidai Kuma fadar gskiar zai iya kawo rashin fahimta sbd shaidan zai iya saka musu kishin juna ko yayane sbd za'a iya cewa ya auresu duka Wanda kwata kwata har abada bazataso hakanba Dan Dole watarana za'a samu sa6ani.
Qarasowa tayi jikinta amatuqar sanyaye,
Da sanyin jikin abinda dawood yayi Mata ta shigo Amma Jin abinda Layla ke fada ya qara sanyaya jikinta.Zama tayi kusada laylar tana kallonta cikeda mamaki da fargabar ganin sauyi sosai atareda ita,
Idanuwanta dasukai jajir da fuskartama gaba 'daya takalla tuni kafin taji koma meyene idanuwanta suka cicciko Nan take damuwar datake ciki ta dawood ta 6ace asanyaye tace,Dama Layla akwai abinda harzaki saka wani alqawarin kar afadamin??
Wane irin sirrine da Ni bazan iya 6oye mikiba har kike guduna dashi....Jin muryar aleeyar tafara rawa yasa tayi saurin riqo hannunta tana qoqarin Hana hawayenta fitowa Amma Saida suka gangaro tace,
Har abada Babu wani sirri dazan 6oye Miki idanma akwai to kisaka aranki Dan ciganki da farin cikinki ne...
Inason sanin koma menene Layla kifadamin tun kafin zuciyata ta buga da fargaba.
Share hawayenta tayi ahankali tace,
Dawood iyayensa sun Masa Mata har antsayar da ranar aurensu bazai ta6a aurena......
Tun kafin laylar takai qarshe kukan datake riqewane ya kubce Mata tayi saurin rungume laylar cikeda wani irin tausayinta dama tanason yin Kuka Dan rage zugin zuciyarta na tsantsar qiyayyarta data hango a idanuwan dawood idan ba kuskuren gani tayiba.
Kuka take sosai na tausayin Layla da kanta saidai tafasa fadawa Layla damuwarta Akan qiyayyarta data gani a idon dawood sbd karta qara Mata damuwa ko ammy bazata fadawa ba zata bar maganar aranta ta Taya 'yar uwarta jimamin abinda yasameta..
Sosai tayi qarfin Hali ta nunawa aleeya ta rumgumi hakan amatsayin dama bashine mijinta ba.
Girgixa Kai aleeya tayi tana fitarda sabbin hawaye tace,
Yanda kikesonsa har abada bazaki daina sonsaba,
Tun zamana dake akwai wasu farin ciki da annashuwa dashine kadai yake sakiyinsu koni bana sakaki duk kuwa danasan babbn matsayin danake dashi agunki,
Layla bazaki iya babushi ba Ni zanje har gurinsa na roqesa yadawo gareki zan qasqantar da kaina na roqesa qasqantarwa ta qarshe Dan yadawo gareki..Share hawayenta tayi tana qaqalo murmushin qarfin Hali sbd so take arufe maganar dawood da ita gaba 'daya ayau basai ankwanaba ga kanta dake tsananta ciwo zazza6i Mai zafi takeji sosai.
Aleeya na dangana nabarsa har abada Dan haka daki tayani nemosa gwara kitayani mantawa dashi.
Sake rungumeta aleeya tayi cikin tsananin tausayinta da Jin zafin dawood 'din daya za6i wata yabar Layla Nan take taji ta tsanesa Koda zai dawo bazata ta6a barinsa ya auri Laylan ba sbd Bai cancancetaba
Laylanta ta cancanci Wanda yasan darajarta fiyeda komai.Jin jikin laylar da zafi yasa ta ja hannunta suka koma bedroom 'dinsu ta kwantarda ita tareda ja Mata bargo cikeda kulawa tace,
Have some rest zakiji qarfi zuwa anjima.
Miqewa tayi ta zame kayanta tasa jeans da vest tadawo bakin gadon da laylar ke kwance ta rafka tagumi cikeda tunani da damuwar kanta data laylar.
Itama Layla rufe idanuwan kawai tayi.
Daqyar ammy ke sakin murmushin yaqe hardai Abba ya tambayeta maganar iyayen manemin Layla kawai suke jira su qaraso yanxu.
Rufe idanuwa tayi tareda ha'diye wani 'daci a maqoshinta cikeda damuwar abinda zata fada tace,
Saidai ayi hkr akwai wadda iyayensa keso ya aura Dan haka sun fasa zuwa saidai zuwa gaba idan ansamu fahimta.
Fada Abba yahauyi Rai a6ace yace,
Dama dai bada gskia yakeyiba Dan da bazai Raina Mana hankaliba yace zasuzo.
Hakuqi CJ yabawa abban Yana cewa,
Agodewa Allah bama Saida akazo 'daurin aure yace yafasaba.
Exactly fa ai gwara da tun yanxu akasan stand nasu""""mum ce tafada hakan tana nuna tausawarta ga ammy datayi nisa a tunani ko abinda suke fada bataji.
Zuciya ba da'di hakanan Abba da dad suka tsayar da bikin wata biyu Masu zuwa hakanan mum ta haqura badan tasoba sbd da wuri taso ayi.
Koda suka koma gida dawood bayanan Kota kansa batabiba tayita harkokinta cikin farin ciki.
Baidawo gidanba sai dare sosai kallo 'daya zakai Masa yabaka tausayi sbd kwata kwata Bai saba da wahala ba Amma yau ko ruwa baisawa cikinsaba haukacewane kawai baiyiba gurin Kiran layinta yakira yakira,yayi yawo agarin harya 6ata saidaya Kira taheer yaje yadawo gida dashi.
Ganin yanda daqyar yake bude bakinsa daya bushe yasa mum da taheer hankalinsu Fara tashi Nan tahau lallashinsa akan yasha Koda juice ne Amma yaqi.
Wasa wasa saiga zazza6i Mai qarfi ya kwantar dashi adaren Babu Wanda ya rintsa cj cikin tashin hankali yasa sukabi jirgin safe suka dawo Abuja.
Koda suka dawo babu abinda yayi sauqi gashi yahanawa kansa sukuni da daina Kiran layinta.
Da daddare Dr dayazo tasashi yayi mixing alluransa Dana bacci yayi Masa Nan take bacci yayi gaba dashi.
Dr na fita ta 'dauki wayarsa ta duba numbern datake nema ta goge tareda duk wasu massages daga gareta duk wani Abu daya danganceta saidata goge ta 'daga wayar sama ta sakota qasa tareda ficewa daga bedroom 'din.
#mamuhgee
Vote,
Comment,
Follow and share.
