Daga umrah Dubai suka wuce acan sukayi siyayyar sabbin kayan sawa sbd Fara rayuwar University dazasu shiga.
Satinsu 'daya a dubai suka dawo gida dawowarsu da kwana biyu sukaje adamawa Basu wani dadeba suka dawo sbd hutun Bilal daya qare nakomawa school.
Aiki suke akicin na abincin dare itada ammy da shafa'atu aleeya na 'dauka tana jerawa a dining sbd yau Abba zai dawo daga tafiyar dayayi zuwa Miami gurin tsohon babban amininsa former CJ ASSIDDEEQ DAUDA.
Suna gamawa ana fara Kiran sallar magrib suka nufi bedroom 'dinsu da yanxu aka sauya musu komai zuwa na matured 'yan Mata.
Tubewa tayi tareda 'daura coffee brown towel Mai girma ta fada toilet tana cewa aleeya data kwanta agado tana browsing sbd ita tana cikin period Bata sallah...
Aleeya kamar naji shigowan motan Abba.
Da sauri ta aje wayarta ta sauka gadon tayi palour.
Girgixa Kai tayi tana murmushi kafin tashige toilet 'din.
Wanka tayo tareda alwala tafito tashafa mai tasaka doguwar rigar yadi Mara nauyi tasaka hijab ta tayarda sallah.
Tana gamawa ta cire hijabin sallar ta saka hula ta rufe gashinta ta fito direct palon Abba datake jiyo hayaniyarsu ta nufa fuskarta 'daukeda farin ciki a ladafce tace,
Abba sannu da dawowa.
Yauwa Laylan ammy zance Kota aleeya??? Yafada da sigar tsokana.
Aleeya ta kalla tana murmushi tace,
Laylan ammy...Bata qarasaba tace Aa Abba Laylan aleeya sbd ganin kallonda aleeyar ke Mata.
Dariya dukkaninsu sukayi ammy tace,
Damacan ba wani gulma Dan nasa baza'ace niba ko ance Ni na gulma ne.
Ammy qyalesu Allah ina gani lokacinda aleeya ta harareta shine za'a wani ce ke Dan kawai 6arnar suna.
Jifansa laylar da aleeya sukayi lokaci 'daya da pillow yayi saurin kaucewa Yana cewa,
Eh ai gskia nafada ko ammy.
Sosaima kuwa 'dan ammy barni dasu inanan zasu sameni neman wani Abu.
Abinci sukaci a dining gabaki 'dayansu cikin Raha harsuka gama Basu wani jimaba apalo kowa yayi 'dakinsa sbd kowa da abinda yakesonyi.
Lokacinda results dinsu yafito yayi kyau sosai amma wannan shekarar basuyi jamb ba sai next year duk da ammy sosai taso ache anfara yimusu aure kafin su wuce University Amma Abba Sam baiyi na'am da hakanba kasancewarsa riqaqqen 'dan boko dakeson 'yayansa subi sahunsa Koda zai musu aure saisun gama University sun Fara aiki sun zamo independent.
Kamar dai yanda aka sani Lagos garine da mutanen cikinsa sukeda tsananin wayewa Wanda wata wayewar harta zarta tunanin Mai hankali tazama iskanci tsagwaro,
Duk iya inda wayewar Masu ilimi take sun waye ga uwa uba hutu daya gama ratsasu da gata,
Ayanzune suka shiga University Kuma ayanzu shekarunsu na haihuwa suke ashirin da uku uku zuwa da hu'du.,
Zuwa lokacin sunyi friends tsirara wayayyu Yan gata irinsu Kuma zuwa lokacin kowacce da motarta saidai hakan baida amfani Dan kuwa basa ta6a fita dabam dabam.Layla tafi aleeya haske da tsawo tareda bajewar mazaunai ma'ana hips.,
Duk da tsawonta tayiwa kanta mugun sabon koyaushe heels ne takalmanta sbd sabawa datayi dasu sa6anin aleeya datafison wedges.Gagayen turkey gowns da Kuwait gowns sune suturar Layla sbd sune sukefi komai yimata kyawu sbd full package shape dinta Sam jeans ko native wears Basu dameta ba saidai can ba'a rasaba take sawa musamman jeans dayafi komai fitarda full package 'dinta sbd hips din gske takedasu.
Aleeya kuwa qananun Kaya Amma irin loose dinnan Masu shegiyar tsada sai native itama sai can ba'a rasaba.
Kallo 'daya zakayiwa Layla ta'dau hankalinka sbd wani irin kwarjini da fuzgar hankali datake dashi uwa uba sarqar qafarta da ita kadaice abinda suke gani na mahaifiyarsu dake tsananin qara sa ta'dau hankalinka,
A ra'ayi kwalliya Bata damu Layla ba saidai tsadaddiyar oriflame powder da lips balm 'dinta take amfani dasu suke qarawa fuskarta kyau da kwarjini sabanin aleeya dake makeup Koda yaushe.
Lokacinda Abba yabasu admission letter dinsu suka bude atare sukace ABUJA...
Yes...yace Yana cigaba da duba saqon email daya shigo laptop dinsa yace,
Kufara shiru end of this month zaku wuce.
Cikin tsananin farin ciki suka nufi bedroom din ammy
Koda sukaje waya suka tarar tanayi da umman siyam Bilal kuma na kwance kan gadonta Yana karatun wani Islamic book a laptop dinsa.Sallama tayi da umman siyama tana cewa lafiyarku kuwa wannan ihu hardai ke aleeya sarkin harshe Kin girma bakisan kin girmaba.
Layla ce ta miqa Mata takardar hannunta tareda zama kusada ita aleeya kuwa gurin Bilal tayi.
Tana karantawa fuskarta ya canza sbd har cikin ranta tana tsananin Jin damuwar karatunsu hankalinta zaifi kwanciya idan akai musu aure kowacce tayi karatun a gidan mijinta sbd hakanan takejin fargaba da tashin hankali ga karatun nasu koyaushe itadai Bata fatan abinda zai shiga tsakani ya raba kan yayanta.
Ganin yanda fuskarta ya canza yasa jikin layla Jin sanyi sbd Sam ta tsani ganin damuwa a fuskar ammy,
Lokuta da dama idan taga ammy cikin tunani ko damuwa hankalinta tashi yakeyi saitayita rarrashinta tana nuna damuwarta Akan koma menene yake damun ammin harsai tafada mata shiyasa koyaushe sukafi kusanci yanxu sosai akan aleeya,
Tazamo ita kadai ammy kefadawa sirrinta da damuwarta amatsayinta na yarta.Dafa ammyn tayi cikin sanyin murya tace,
Ammy Dan Allah karkisa damuwa aranki.
Riqo hannunta ammyn tayi tareda kallon aleeya dake dukan Bilal suna wasa da dariya murya a mace tace,
Layla kinfi aleeya nutsuwa da sanin yakamata Dan Allah kiyimin alqawarin toshe duk wata ga6a ko mafakar daxata shigo da tashin hankali ko rashin fahimta tsakaninku inason nacigaba da ganinku cikin farin ciki haka ko bayan Raina.
Hawayene suka ciko idanuwanta ta riqe hannun ammyn murya na rawa tace,
Ammy karki saka damuwa aranki komai zai zauna ayanda yake insha Allah na Miki wannan alqawarin.
Thank you my daughter Allah yayi muku albarka.
Amin ammy.
Aleeya ce matso tana cewa,
Sirrin me akeyi mommy and daughter wai Bilal bakaga yanxu gidannan ana Mana banbanci ba.
Nasoo oo my sister na 'dauka nikadai nake lure.
Hararsa layla tayi tana cewa,
See his big coconut head.
Eh naji ai gskia muka fada Abi my sister.
Hararsa ammy tayi tana sake saka musu albarka gabaki 'dayansu.
Anan 'dakin sukai sallar Isha kafin suka nufi dining sukai dinner kowa yakama hanyar bedroom'dinsa.
#mamuhgee.
