Kasa zama tayi kodata shiga 'dakin ta tsaya tsakiyar 'dakin tana qoqarin samarwa kanta nutsuwar fahimtar abinda ke tabbatuwa arayuwarsu,
Wasu irin hawayene suka gangaro Mata tana qoqarin danne kukan dakeson biyo bayansu.
Dawood 'dinta shine dawood 'din da aleeyarta keso meyasa takasa fahimta tuntuni daya sanarda ita garinda iyayensa suke.?
Meyasa dawood yaqi fada Mata cewar,
Iyayensa sun nemar Masa Mata...?
Wannen wane irin alamarine ya kusantosu.
Rufe Ido tayi tana tsananin Jin zafi azuciyarta,
Rawa qafafuwanta suka Fara yimata ta sulale tsakiyar 'dakin hawayenta na tsananta gudu sabuwar doyayyar dawood takeji har cikin jininta,
Soyayyar dawood tariga tazamo wani 6ari na jikinta wani irin zafi da nauyi takeji ayanxu data gansa amatsayin na aleeyarts to Yaya aleeya zataji idan taji shine dawood 'dinta.Girgixa Kai tayi hawayenta na qara gudu cikin rawar murya ahankali tace,
Wlh zafi nakeji sosai cikin zuciyana aleeya bazanso kiji wannan zafinba Bazaki iya juresaba.
Ahankali tafara kuka Mai qaramin sauti har lokacin jikinta Bai daina rawaba.
Tunowa da ammy yasa ta tsayarda kukanta tareda tattaro qarfin Hali tasawa zuciyarta ta share fuskarta tareda miqewa da sauri ta fice tana roqon Allah yasa ammy da dawood basuga junaba.
'dakin ammy ta nufa tana qara qoqarin danne halinda take ciki.
Ammy ce kawai a 'dakin itama wayarta tazo 'dauka takoma palon gurinsu Abba.
Ahankali ta qaraso gaban ammy ta riqo hannunta tareda dawowa bakin gado suka zauna.
Sunkuyar dakai tayi hawayen datake qoqarin dannewa sunason fitowa Amma ta 'daure ta mayar dasu Amma idanuwanta sun jajir.
Sanyi jikin ammy yayi ta qura Mata idanuwa ta lurada yanda jikinta ke 'dan rawa ta riqo hannunta da sauri cikin tsananin fargaba tace,
Layla?
'dagowa tayi takalli ammyn Nan take ammy ta qara shiga ru'dani ganin Jan idanuwanta tace,
Layla meke faruwa?
Ammy tunda na taso cikin quncin rayuwa da talauci na taso,
Babu Wanda ya ta6a yimin kallon mutum bare ya bani mutuntawa da darajar da Allah yabawa mutum,
Ni Almajirace 'yar bola Mara asali da gata,
Ammy duk duniya bayan iyayena dasuka haifeni Babu Wanda nake tsananin so da qaunar farin cikinta irin aleeya sbd itace takalleni amatsayin mutum ta miqamin hannu ta cironi daga qanqantacciyar rayuwar titi da bolan danakeyi Wanda da yanxu na zama wata abar qyamar.,Ammy har abada ina roqon Allah daya nesantani da abinda zaisa nakawo damuwa a fuskar aleeya.,.....
Sosai jikin ammy yayi sanyi murya a sanyaye tace,
Layla meyasa kike tado da abinda yazamo tarihi?.....
Dr Dawood ne Wanda aleeya zata aura..
Yawu ammy ta ha'diye sbd gudun garajen fahimta tace,
Banganeba Layla sakemin bayani.
Ammy dr dawood shine 'dan abokin Abba dasukazo yanxu.
Mummunan fa'duwa gaban ammy yayi ta lashi busasshen bakinta sai alokacin tasake qurawa layla Ido taqara hango mummunan halinda take ciki tana qoqarin dannewa.
Layla wannan ba abun damuwa bane tunda ba auren aka 'dauraba zanyiwasu abbanku bayani yanxu..
Miqewa tayi laylar ta riqo hannunta tareda dawowa gabanta ta sunkuyar dakai cikeda qarfin Hali tace,
Ammy ke uwace dabakyason kan 'yayanki ya rabu,
Kin manta nayi Miki alqawarin toshe duk wata hanya dazata kawo 6araka atsakaninmu,
Ammy wannan shine alqawarina dazan cika bazan ta6a Bari hawaye yasauka kan fuskar aleeya ba ta hanyata,
Ammy kiyimin alqawarin har abada Bazaki ta6a fadawa kowa wannan maganarba...Girgixa Kai ammy tayi cikin tsananin tashin hankali da damuwa tace,
Wannan shirme ne kikeyi layla sbd bazai ta6a yiyuwaba,
Idan har farin ciki kikesowa aleeya to Bazaki Bari ta auri Wanda baya sonta yanada wadda yakeso wace irin rayuwar aure zatayi da Wanda keson wata mace ba itaba...Hawaye ta goge da bayan hannu tace,
Ammy shine farin cikinta,shitakeso bazata ta6a iyason waniba bayansa....
Kidaina fadamin haka sbd wannan ba sacrifice bane Layla rayuwarku ce ku uku zata lalace,
Kalli halinda kike ciki yanxu,
Ji yanda kike qowarin danne quncin dake ranki Amma ina iya ganinsa,Dawood ke yakeso bazai ta6a son aleeya ba sbd tun farko ba ita yakesoba.
Tsananta hawayenta sukayi tace,
Ammy Koda Baki yardaba na yafe dawood har abada sbd bazan iya cigaba dason abinda aleeya kesoba,
Wannan alqawarina ne duk ranarda aleeya taji zancen Nan zan tafi tafiya ta har abada ammy sbd bazan iya hada Ido da itaba nayi tarayya da ita akan abinda takeso nakasa cirewa zuciyata cewa hakan ba laifina bane.Tsananta tashin hankalin ammy yayi tace,
Layla meyasa zakiyi haka Dan kuwa hakan shine babban kuskuren dazaki tafka wannan ba mafita bace.
Kuka tasake ahankali ammyn tayi saurin rungumeta tana danne nata hawayen sbd Laylan tasakata a tsaka Mai wuya sbd rayuwarsu duka su biyun ne zata lalace garin toshe 6araka za'ayi gaba Mara da'di.
Jin motsin shigowa yasa laylar zamewa ta miqe ta shige toilet 'din ammy.
Siyama dake jinsu tun farko ta gyara tsayuwarta tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,
Hmmnn dagani abubuwa zasu zomin yanda suka Dace,
Dawood sukeso dukkaninsu hmmm,
I will make this my mission matuqar inada Rai da lafiya bazan ta6a Bari aleeya tasan da wannan zancenba sbd dataji kamar koyaushe Layla xata samesa hakan na nufin koyaushe itace a gabanta..
Duk Wanda yayi qoqarin ha'dasu kuwa saita 'dorasa adaidai inda bazai qara kallon matsalar waniba tasama tafi qarfinsa.
Mission 'dinta na biyu kuwa taheer,
Kallo 'daya tayi Masa ya tafi da zuciyarta Dan haka kuwa duk duniya batasaran zata zauna ta huta batareda burinta na aurensa ya cikaba.Daki takoma tana zuba murmushin farin cikin samun sauqin abunda yakawota.
Aleeya kuwa tunda sukaje palon taheer kawai suka tarar suka gaisa siyama kallo 'daya tai Masa tasaki Baki tuni tafara tunanin yanda rayuwarta zata canza idan ta auresa.
Ganin zata zubarwa da kanta aji gurin kallonsa yasa tamiqe takoma 'daki anan kunnuwanta sukayo Mata farin ji.Fira suke hankalinsu kwance akai akai saiya Fadi sunan Layla saidai kawai tayi Masa dariya sbd tun acan tafada Masa akwai Wanda Laylar keso.
Daqyar taheer yaje yashigo dashi sbd lokaci 'daya ya burkice sbd rashin Jin Nur gashi yanxu ta kashe wayar gabaki 'daya ma.
Kodaya shigo Sam mantawa yayi da maganar inda yake daqyar taheer yayita basa Baki yadan sassauto ya nutsu.Kallon inda take yayi fuska a ha'de..
Lumshe Ido yayi cikin tsananin takaici,
Mum Sam batamasan abinda zai iya soba,.Fa'duwa gabanta yayi ganin irin kallon daya jefeta dashi amma duk da haka zuciyarta cike take fal da farin cikin ganinsa Wanda tuni sonsa yaci gaba da ninkuwa a zuciyarta.
Kasa magana yayi sbd yanda nutsuwarsa ke qara hautsinewa ya miqe tareda fiddo wayarsa ya fice Yana cigabada Kiran Nur.
Taheer ne yabiyosa da nufin fada Masa abinda yayi Bai daceba Amma ganin yanayinsa sai jikinsa yayi sanyi yace,
Dawood please relax kabari zuwa anjima saika sake Kira yanxu bakaga muna gidan kunya bane.
Wani mugun kallo ya watsa Masa tareda juyawa ya tada motar dasukazo da ita daga gidansu nanan yabar gidan gaba 'daya.
#mamuhgee.
Vote
Comment.
