not edited.
wani irin mahaukacin gudu yakeyi yana duba gabansa sosai sbd sosai motarsu tayi masa nisa yana kaiwa round trafficlight ta tsayar dashi kota kanta baibiba ya wuce da gudu daidai lokacinda aka sako wasu motocin nantake sukai wani irin karo kankace me tuni gurin ya rikice da holdup wasu nata zaginsa bai tsaya sauraronsuba ya bude motar da sauri yafito yana kukkutsasu harya fice cikinsu yaga ko alamar motarsu laylan ya dafe goshinsa tareda rufe ido cikin wani irin mugun yanayi na tsoro da fargaba.
wani police ne yazo ya tsaya agabansa yanata faman zuba masa fada akan holdup daya hada ahankali ya juya yashigar motar yafara matsawa har hanya tafara samuwa nan gurin yafara sakewa yasamu hanya ya dauki hanyar gidansu da gudu,
yana isa su sufyaan na harabar gidan sunata faman kiransa,
yanayin shigowarsa da parking dinsa yatabbatar musu da babu lafiya nufarsa sukayi kowanne na qoqarin tambayarsa amma baimasan sunayiba saidai ya nufi flat dinsu ahargitse ya dudduba koina bata nan yafito harabar gidan yana qoqarin sake fita jass ya riqesa cikin daga murya yace,
wai bakajine,menene yake faruwa ka kasa fadamana duk kasa hankalinmu yatashi?
kallonsu yayi da jajayen idanuwansa wani irin zafi na tasowa daga zuciyarsa yace,
akaro na biyu aleeya tasake shiga tsakanina da farin cikina sbd jikina nabani NUR barina zatayi sbd aleeya,,,,,aleeya itace babbar matsalata arayuwa kaji yanda take yiwa matata ihu kuwa,she even slapt her bayan tasan she's pregnant and now nur left sbd gudun 6acin ran aleeya ya zanyi da rayuwatane?
bansan meyasa tunfarko ba nafara soyayya now i'm stuck wit this two best friends zance ko sisters.dafe goshinsa yayi yana sakejin ciwo cikin ransa,
ganin kamar yana buqatar taimakonsune yasa suka dunguma yawon duk wani motopark da stations nemanta amma babuta babu mai kamada ita nan hankali ya qara tashi mum tun tana daurewa kasawa tayi ta miqe ta fita nema itama sbd harga allah tasamo danta ya daidaitu daqyar bata fatar akoma inda aka fito,
ta yarda tabi sai layla.har dare suna abu daya amma babu alamar zaa ganta,
hankalinsu bai qara tashiba saida sukaga dawood na neman shiga wani hali babban abinda yafi jijjiga duniyarsa shine sabon sonta da dansa ko yarsa dake cikinta,duk yanda sukaso dawowa gida har gobe qiyayi haka suka raba tsakiyar dare suna nema shiga tashin hankali,
asubar fari dole suka dawo gida jiran kira daga stations dinda suka bayarda reports reports,
duk yanda mum taso ko ruwan coffee yasha yakasa sha gashi har wani jiri jiri yake gani daqyar yayi sallar asuba ya sulale yaqara ficewa basu saniba.
duk yanda taso bawa zuciyarta dangana da rarrashi saitaji takasa sbd mutane biyune data fifita qaunarsu fiyeda komai suka taru suka karya zuciyarta da yardarta akansu,
tanason dawood so mai tsanani data za6i zaman rayuwar qunci agidansa sbd sonsa kuma ta shirya hakan har qarshen rayuwarta saidai duk sonda take masa tafison laylanta fiyedashi meyasa layla taza6i 6oye mata komai?
zata iya bawa layla jininta da qodarta bare abinda takeso amma suka za6i baqanta mata fiyeda fada mata komai tun farko,dafe zuciyarta tayi tana cigaba da rero kukanta sbd qunci da zafi takeji sosai cikin ranta idan har haka ake sadaukarwa to itakam tata batazo mata a dadiba don kuwa nata cutatarwane,ancuceta anbarta tana jinyar banza abanxa.
tun tana kukan da qarfi harta koma ta lafe saidai hawaye,
abba daya dawo yana fada sosai akan sunbarosa asibiti batareda anyi abinda akaje yiba cikin sanyin murya da fargabar yanda zai dauki zancen ta zayyane masa komai,
shiru yayi yana jujjuya zancen cikin zuciyarsa kafin yasake ajiyar zuciya yakalli ammy cikin sanyin murya yace,
wannan alamari tabbas qaddarane sbd matar mutum hausawa sunxe kabarinsa ce saidai duk muduka amatsayinmu na iyaye munyi kuskure musamman keda kike uwa mace kuma kinsan komai amma kika qyale,
datun farko kin fadamin koda baki fadawa aleeyarba saimu samu mafitarda zata 6ulle bakamar irin wannanba,
