23

8.7K 931 27
                                    

Kiran taheer ne yashigo wayar aleeya suka saki juna ahankali ta 'dauka ita kuwa fitowa tayi da sauri ta shige kicin tayi bayan fridge ta sulale qasa tareda sakin wani irin kuka tana toshe bakinta.

Kuka take sosai zuciyarta zafi da qunci take Mata Batada damar nunawa har abada haka zata zauna tana 6oyon wannan quncin ita kadai.

Sheshekar kukanta tajawo hankalin Nana data shigo kicin 'din jiki amace ta zauna kusada ita hawayen tausayinta na gangaro Mata ahankali tace,

Kiyi hakuri anty.

Cusa kanta tayi cikin qafafunta tana cigaba da shesheka tareda qanqame jikinta.

Sun Jima ahaka kafin ta 'dago ahankali takalli Nana data dage tana sharbar kuka tasaki murmushi Mai ciwo tareda qurawa sarqar qafarta da dawood yake tsananin so asanyaye tace,

Dawood yayi sa'ar samun matarda ba kamarta gurin kyawawan halaye da kyakkyawar zuciya sbd aleeya nada halayenda bazata ta6a barinsa yayi baqin cikin samunta amatsayin mataba,

Qaruwa kukan Nana yayi sbd tausayi Dan tana iya jiyo damuwa da qunci cikin muryar laylar.

Wani murmushin tasake sake tareda share hawayenta ta miqe ta bar kicin 'din.

Bedroom 'dinsu takoma tana qoqarin danne damuwarta.

Ahankali ta ringa nunawa aleeya Batada damuwar komai saima qoqarin dagewa datake gurin shirye shiryen bikin dake qaratowa
Tun aleeya na baya baya da harkar sbd sanin Dole laylar nada damuwa 6oyewa takeyi harta sake itama ganin da gaske laylar ta sake suka bazama shirinsu
Abinda Bata saniba shine kowace safiya da bikin ke qaratowa tashin hankali da damuwarta qaruwa sukeyi suk lokacinda taji zuciyarta na zafi 'dakin Nana take shiga tayi kuka ta rarrashi kanta tafito Abu 'dayene dayafi gigitata shine aurenta da taheer dahar yanxu ko waya dashi Bata iyawa Shima dayake bamaison hayaniya da takurawa bane saiya qyaleta.

Lokacinda su mum suka kawo lefe naban mamaki sai alokacin siyama tasan abinda ke Shirin faruwa taheer 'dinta da auren Layla.

Toilet tashige ta kunnawa kanta ruwa tana qoqorin Jan numashi da rarrashin zuciyarta kartayi komai cikin garaje Dole tana buqatar rarrashin kanta dantasamu damar tarwatsa komai cikin ruwan sanyi.

Tana cikin toilet 'din taringa jiyo murya na tashi cikin bedroom 'din ta matso kusa tareda kasa kunne sbd Jin kamar fada fada...

Sarah Matsalarki 'daya arayuwa shine you are inpatient nafada Miki Zaki samu dawood idan kin kwantarda hankalinki mun Fara sanin inda wadda yakeson take mun Fara gamawa da ita tukuna Amma yanzu cikin mutane cikin gidansu aleeya kina neman rusa Mana plan meyasa Zaki zubawa aleeya juice nasan you did it on purpose Amma kikace musu ba da ganganba tun farko banmasan me dawood yagani agunkiba yasoki wlh..

Excuse me Mrs Damien idan kina cewa bayada tunanine daya Soni to ya gadane inaga sbd kema gashi yanzu ke Kika nemoni da kanki....

Are you trying to insult me miss?

Kece Kika Fara and....

Jin qarar bude toilet yasasu saurin juyawa afirgice musamman ma mum.

'daure takeda towel ta qaraso gabansu ta tsaya tareda kallonsu Kai tsaye tace,

Naji me kuke fada.

Idanu mum ta qyafta cikin rashin gskia tana qoqarin qaqalo murmushi zatai magana siyama ta katseta Kai tsaye da cewa,

idan nace muku nasan waye dawood yakeso zaku bani nima abinda nakeso?

Kallon tsaf mum tai Mata tagano Babu alkhairi atattareda siyamar tace,

Kinsan abinda kike cewa kuwa?

Qwarai kuwa maganar dr dawood da Nur din dayakeso..

Kallonta mum tasakeyi sbd jin sunan yarinyar abakinta ya tabbatarma da tasanta da gske.

Kifada zamu Baki ku'di iya adadin dabazaki iya kashewa ba.

Murmushi tasaki tace,

Nida nake hangen injimin ku'din gaba 'daya Mai zanyi da Wainda zakuban??
'danki nakeso taheer.

Wani irin mugun kallo mum ta watsa Mata baqin ciki da takaici na taso tace,

'dana yafi qarfinki kifada wani abun bayan wannan.

Inada asali cikakke Dan haka nafi sadaka ayalla da ba'asan asalintaba ita meyasa baifi qarfintaba.?

Kidaina sako wannan sbd itama bawai tasamesa bane zanyi lokacinta idan muka gama da matsalar dawood tukuna.

Kar6e zancen saraah tayi da saurin cewa,

Mum ki amince kawai da buqatarta Dan musamu Musan abinda mukeson sani afterall Naga wannan 'din dazai aura ba sonta kikeba.

Shiru mum tayi cikin tunani sbd har abada bazata ta6a Bari 'yayanta su auri wainnan biyun dake gabantaba Dan kuwa data Bari taheer 'dinta ya auri wannan ba gara tabari ya auri Laylanba tayita gana Mata wulaqanci da azaba tasan zata 'dauka akan tasa ya auri wannan da zata iya korota daga gidan wata Rana..

Murmushin Dole tasaki tana cewa,

Shinkenan tunda kince haka na amince zansa ya aureki Amma da sharadin sai bayan aurensu na yanzu Kuma sai kunyi narasar raba 'yayana dasu Kuma ba.....

Sallamar Nanace tasa mum 'din yin shiru tareda sakin yaqe
Nana tace,

Ammy na magana.

Ok ganinan muje.

Bin Nana tayi tana watsawa gefensu wani mugun kallon qyama.

Bayanta sukabi da kallo saraah harda qaramin tsaki kafin ta juyo ta kalli siyama up and down tace,

Zan fada Miki gaskia wannan matar qarya take Miki bazata ta6a barin ki auri 'dantaba zatayi amfani dakene kamar yanda take tunanin tanayi Dani batasan Nice zanyi amfani da itaba Dan haka just name any price zan biyaki kifadamin komai gameda yarinyar.

Kallon saraah 'din tayi koba komai maqiyin maqiyinka abokinka ne koba komai mace ' dayace suke Hari kuma dole dama wasu ayukan datake planning Saida cash gashi saraah nadasu Dan haka komai zaizo musu asauqi dan haka ta matsa jikin qofa tasaka key tareda dawowa ta zayyanewa saraah komai ta 'dora da cewa,
garaje ba naki bane kibini kiga yanda asannu zamu tarwatsa rayuwarta da duk wani munafukin dake binta idan mun gama dasu saimu koma kan yanda zamu samu mazajen burinmu.

Wani irin murmushin Jin Dadi saraah tasaki tana jinjina shawarar siyama aranta Dan kuwa siyama itace irin mutanen datakeso arayuwarta wainda zasu iyayin komai dansu samu abinda sukeso at long last tasamu qawar dasuke ra'ayi guda.

Zama tayi bakin gadon dakin tana cewa,

Zan nunawa mrs Damien kuskuren data tafka na tunanin zata yaudareni sbd bayan zuwana Nan gidan ayau na fahimci komai wato itakeson dawood ya auri aleeya nikuma tayi amfani Dani gurin rabasa da wadda yakeso hmmm dukkaninsu saisunyi danasanin cin amanata harshi dawood 'din su maska kuwa saina hargitsa rayuwarsu 'daya bayan 'daya Susan wa suka taru suka hainta,
Mum kuwa bamu Bari tasan Layla bace sbd zata iya canza ra'ayi idan dataga 'danta na Shirin mutuwa
Baqin cikina 'daya Dole zan hkr Ina kallo dawood yafara auren wata kafin Ni.

Cikeda murmushin farin ciki itama siyama ta jawo doguwar Riga ta zura tasamu wadda zata tayata aiwatar da aikinta cikin sauqi....
Hmmmnnnn Layla tashin hankalinki ya qarato kekuma aleeya saikinyi danasanin fifita bare akaina.
#mamuhgee
#vote
#comment.

DAWOOD✅Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora