NOT EDITED
kallonsa tayi da sauri taga ya daure fuska sosai sai jikinta yaqara yin sanyi tafara qoqarin dagasa tana kallon fuskarsa koxai sassauto saima kawai ya dauke kai ya qarasa janyeta ya miqe ahankali daidai shigowar little dataga shigar layla dakin ta biyota,
ummy''''ta furta da qaramar muryarta
da sauri ya juyo tareda aje spray din hannunsa ya zubawa little din idanuwansa ko qyaftawa bayayi
wani sanyi da farin ciki yakeji yana sauka cikin zuciyarsa har baisan sanda ya matso gaban yarinyarba ya durqusa ya cirata sama murya na rawa yace,alhamdulillah ya Allah da wannan niima da kyautar taka.
kallonsa take sosai itama duk da tana yarinya sosai haka takejin qaunarsa na yawo cikin jininta,
layla dake tsaye jiki amace ta matso tana satar kallonsa ganin yanda yake murmushi yana kallon 'yarsa duk saita qarajin tausayinsa tana satar kallonsa ta shafo fuskar little cikeda tsananin qaunar yarta tace,
little ga big daddynki nan dakike nema kullum da muna gidansu mumy raheenat.
da sauri little ta kallesa tareda washe bakinta ta qanqamesa tana cewa,
my big daddy.
rumgumeta yayi qamqam yana cewa,
i love you,i love you my sweet sweet angel 'din daddy.
rintse idanuwansa yayi tsananin soyayyar 'yarsa da mahaifiyarta na sake ratsa koina ajini da jikinsa saidai yanxuma yana qarajin zafin NUR din data nesantasa da 'yarsa tsawon lokaci.
daqyar ya ajeta tayi waje da gudu tana kuran mummynta tazo taga big dady dinta.
cikin wani irin farin ciki da kuzarinda baisan yanadashiba ya shirya batareda ko gefenta yasake kalloba yasaka kayan shan iska wannan karon da kansa yafito palon.
share siririyar qwallarta tayi tareda biyo bayansa ta fito itama.
aleeya kuwa ganin jass na qoqarin matseta da bango yasa tayi saurin zubewa kan sofa tana fitarda numfashi da sauri sam ko kanta takasa dagowa tasake kallonsa sbd qirar qaqqarfansa kayar mata da gaba takeyi tanaji yazauna kusada ita tayi saurin juyowa takallesa ya kashe mata ido daya da sauri ta miqe tareda hade fuska zata fara zuba masa ruwan masifa ya ruqo hannunta tareda dawo da ita inda ta tashi ta fixge hannunta zatai masifa little ta fito da gudu tana kiranta dole ta hadiye tareda watsa masa wani mugun kallo kafin tajawo little din jikinta tana tambayarta ya akayi.
yana fitowa palon a dining idanuwansa suka fara sauka
mamaki yakamasa ganin yanda sufyaan ya shagala sosai yanacin abinci yana firarsa hankali kwance da Nana sam ya manta da sauran mutanen dake palon.kallonsu jass yayi shima nan take ya harbo jirginsa akan aleeyar duk saiyaji jikinsa yayi sanyi daya kasa takura zuciyarsa akan yasota kodan soyayyar datake masa sbd allah saidai yafi farin cikin kasancewarta da jass sbd duk cikinsu yafi iya tallalin mace da nuna tsananin kulawa sannan duk da kasancewarsa ba musulmi ba daga farko yanxu yafisu riqo da addini sbd kullum cikin tsayuwar dare da ibada yake har abada yasan shikadaine wanda zai qaunaci aleeya ya tarairayeta sbd ta cancanci fiyeda hakan.
qarasowa yayi yana kallon aleeya dake ce masa ya jiki yace,
alhmdllh,
nagode sosai aleeya.murmushi tayi tana kallon nur data fito jiki sanyaye tace masa,
babu godiya tsakaninmu karka manta kaifa mijin yar uwatane kuma mahaifin princess din dan haka kadaina godemin akomaima please.
thank you''''yasake cewa kafin yace,
zanyi breakfast idan akwai luquid abu.
miqewa sukayi suka nufi dining sai alokacin oga sufyaan ya ankara banxan kallo dawood ya watsa masa yana cewa,
