Washe gari qarfe takwas na dare jirginda tashigo ya sauka a Nigeria mum da kanta taje airport ta daukota
Sosai saraah ke respecting Mrs Damien ta fannin gayu da iya shiga sbd qaryane tayi dressing Bata burgeka ba gata kyakkyawa kamar ba ita ta haifi manyan zaratan samariba.Sarah nada manyan boutiques na manyan designers acan new Jersey Amma Kuma tanason ne tazama queen of the fashion empire Amma haryanxu Bata kamo mum ba a harkar shiyasa wani fannin take jin kishinta saidai ba damar nunawa ya ta iya tunda ta haifi Wanda takeso.
Rungume juna sukayi mum na cewa,
There you are,,,welcome sweetheart.
Thank you mum"""tace tana breaking hug 'din kafin suka nufi mota sukai gida.
Lafiyayyan bedroom 'din dake cikin 'dakunan palon mum din aka sauketa saidatai wanka ta saka black jeans da red loose armless top hankalinta ya kwanta sbd Sam batason wahala tanason hutu.
Zaune suke dining sunacin abinci Kai tsaye mum tace,
Sarah dawood nason wata dabam bakeba.
Qwarewa tayi da mugun qarfi cikin sauri mum din ta miqa Mata ruwa tana cewa,
Sorry sweetheart.
Kasa wucewama ruwan sukai tsabar toshewar da maqoshinta yayi ta ture plate 'din gabanta gefe tareda zubawa mum duka idanuwanta Allah kadai yasan dauriya da haqurin datake bawa kanta da zuciyarta na hanawa kanta shararawa mum Marinda saita kifa na abinda ta fada dawood nasan wata ba itaba.
Tsananin fushi da tsantsar kishinda mum ta hango a fuskar saraah 'din yasata Jin Dadi aranta taci gaba da cewa,
Yes saraah nayi iya qoqarin ganin na rabasu na kasa saima wani sabon problem 'din ya 6ullo,
CJ yazabawa mi'amor wata matar har anyi fixing date saidai Ni ke nakeso shiyasa nakiraki kiraba dawood da waccar yarinyar nikuma na Miki alqawarin bayan aurensa da wannan da dadynsa keso zan aura muku juna.Wani murmushin baqin ciki da takaici tasaki na yanda tazama wawuya tanacan tana bugun gaban bamai dawood sai ita ashe ananan ana Mata yankar baya.
Mrs Damien I love your son to the core extent dazan yi fiyeda abinda tunaninki zai 'dauka.,
Me kike cewa?na zauna ina kallo harsai wata ta auresa kafin Ni na auresa,,no no that is impossible..
Hakan shine bazai ta6a yiyuwaba bare yafaru dukkaninsu su biyun zan nuna musu babban kuskuren dasuka tafka nason abinda nakeso.Murmushin qarfin Hali mum tayi ta kwantarda murya tace,
Calm your self down saraah
Dole zamu Bari bayan auren idan ya aureki saimu Kori waccan sbd idan har dawood Bai auretaba har abada cj bazai ta6a barin ya aurekiba so Dole Zaki zage dantse kema kitayani muga wannan auren ya yiyu Dan musamu cikar burinmu.Shiru tayi tana nazarin maganar mum saidai har lokacin zuciyarta tiriri takeyi takuma kasa yarda da mum ba yaudararta takeyiba sbd she knows how cunning she is a harkar business ma bare tun da da'dewa tanada labarin mum batasonta da dawood meyasa yanxu takesonta dashi.??
Kallonta mum tayi tana yamutsa fuska cikeda baqin cikin kallon saraah 'din sbd batajin har abada zata iya Bari 'danta ya aureta sbd she will never have the respect she deserves as a mother of the man she's marrying Dan haka kawai zataci moriyar gangane ta yada korenta.
******
Kwana biyu sosai layla tadawo itake tausayin aleeyar sbd yanayin data shiga na ciwon dataga layla ta kwanta kwana biyun.
Sam aleeyar Batada walwala Wanda layla tafara zargin kamar akwai abinda ke damunta bayan damuwar ciwonta saidai batasan menene ba.Sbd sauqaqawa aleeyar yasa ta saki jiki sosai ta nuna ta warke ba sauran abinda ke damunta duk da kuwa wani irin ciwo da damuwa takeji cikin ranta.
Zaune suke a bedroom din ammy sbd basa sakewa sosai acan sbd siyama data kasa ta tsare
dukkaninsu sunyi shiru
Dawowa tayi kusada aleeya ta zauna tareda qurawa madubin da aleeya ta qurawa Ido itama murya a sanyaye tace,Na Dade da sawa zuciyana dangana Zaki iya cire damuwar hakanan..
Juyowa gefenta tayi ta kalleta ahankali kafin ta maida kallonta cikin madubin tace,
Kina 6oyemini ne Amma inajin ciwonki da damuwarki azuciyata,
Ina tsananin Jin zafi da haushin dr daya kawo damuwa da kuka akan fuskar danake tsananin baqin cikin Naga ko damuwa akai....Riqo hannunta layla tayi tana kallonta ta cikin madubin idanuwanta na cikowa da hawaye,
Aleeya meyasa kike tunanin nima banajin zafin ganin wannan damuwar a fuskarki,
Na cire damuwarsa.....Ina Miki sha'awar samun rayuwar farin ciki atareda Taheer.
Fa'duwa gabanta yayi da qarfin ta juyo da jajayen idanuwanta takalli aleeyar numfashinta na fita da sauri.
Yes layla,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba da sukuni ko natafi Dan nasan kinada damuwa aranki.,
Meyasa abubuwa suka Fara canzawane da wuri haka,?Bazan takuraki ba Amma nasan taheer zai maye Miki gurbin Dr,zaisaki farin ciki sbd yasan darajarki Yana tsananin qaunarki zai soki yanda har abada bazakiyi danasanin kasancewa dashi......
Aleeyaaa""""ammy dake tsaye bakin qofa takira sunanta da 'dan qarfi sbd ganin Bata lura da halinda Laylan tashigaba,
Rawa jikinta keyi sosai idanuwanta sunyi jajir takasa 'dauke idanuwanta daga bakin aleeyar.
Da sauri ta miqe kafin ammy ta qaraso Bakin gadon ta fice da sauri tana toshe bakinta sbd kukan dakeson kubce Mata.
Qofar 'dakin ta jingina tana shesheka ahankali Dan bazata dakinsuba sbd siyama na dakin.
Cikin zafi ammy tace,
Me kike fada ne?meyasa zakiyi Mata maganar wani ayanzu bayan bakisan zafin datake ciki ba azuciyarta,
Duka duka yaushe maganar dr tabarta dazaki Fara Mata wannan maganar Dame kikeson taji???Kallon mamaki aleeya kewa ammy jiki amatuqar sanyaye sbd ganin yanda ta 'dau zafi akan maganar.
Ammy bazan ta6a takurata ba kinsani kawai inaganin idan anbawa taheer 'din dama zai Bata farin ciki Sosai nasani sbd nasan waye taheer koba komai inaga Bai kamataba ta zauna cikin damuwar Wanda baidamu da halinda zata shigaba ya tsallake yabarta.
Ya isa haka banason sakejin maganar taheer insha Allah zansamo mafita komai zai daidaita Layla zata auri Wanda takeso...
Jin furucin ammy yasa laylar tayi saurin juyowa tana kallonta da ajajayen idanuwanta ta dawo cikin dakin
Matsowa tayi tareda share hawayenta murya na rawa zuciyarta na nauyi sbd da abinda zata fada tana kallon tace,Banason Dr na haqura dashi nabarsa har abada,
Girgixa Kai ammy tayi tace,
Wannan zancene kike fada na harantawa kanki abinda Bai haramta agarekiba.
Idan hakane na amince da auren taheer sbd haramtawa kaina auren dawood.
Kallonta ammy tayi da sauri cikin tashin hankali sbd Bata taba tunanin abinda laylar zata fadaba kenan tace,
Kinada hankali kuwa,
Abin naki yafara yawa wannan karon bazan bariba abin yayi yawa ga Mari ga tsinka jaka.Murmushi Mai ciwo tasaki tace tareda juyowa ta fuskanci aleeya da idanuwanta suka cicciko sbd tausayin layla tareda Dana sanin Fara maganar taheer saidai Batada za6i taheer shine Wanda takeda tabbacin zai goge damuwa da hawayen laylarta.
Share Mata hawaye Layla tayi tace,
Zan auresa ne kawai Dan Kece Kika za6arminshi,
Zan auresa ne kawai sbd nasan bazaki ta6a zabarmin cutaba Koda shi cutane agareni na yarda na auresa sbd kince kinamin sha'awar aurensa...Rufe Mata Baki aleeya tayi tana girgixa Kai da sauri hawaye na sauko Mata tace,
Bazanso ki auri Wanda bakyasoba zamu hakura da auren gabaki 'daya sai ranarda Kika samu Wanda kikeso.
Murmushin tasaki tareda share hawayenta tace,
Hakan bazata ta6a faruwa ba.
Rungumeta aleeya tayi tareda sakin kuka ahankali.
Hawayen da ammy ke riqewane suka gangaro tayi saurin juyawa ta shige toilet sbd sun karyar Mata da zuciya tana fatar Allah yasa hakan shine mafitar wannan masifar data kunno musu Kai.
#mamuhgee
#vote
#comment.
![](https://img.wattpad.com/cover/158188301-288-k195557.jpg)