28

10.6K 1K 106
                                    

NOT EDITED

Ana magrib suka sauka abuja nan motoci sukazo daukarsu suka nufi gidan,
mum cikin farin ciki take sosai nan gidan yaqara hargitsewa da hayaniyar farin ciki,
layla kuwa tsabar tashin hankali da mugun ciwon da zuciyarta keyi tun amota ta sume musu hankali tashe suka qaraso gidan nan mum takira taheer yazo da dr cikin tashin hankali dan sosai ya damu da jin ciwon amaryar tasa,

ruwa da allurai dr ya daura mata kafin aka barta tadan samu hutu,

kukan da aleeya tasha alokacin saidata bawa kowa tausayi dan kwata kwata batajin farin ciki ko wata walwala duk da kuwa tasamu ta mallaki dawood din datake so,

siyama da saraah kuwa daki suka shige cikin tsananin farin cikin ganin burinsu na gaf da cikewa.

daqyar aka lalla6ata aka kaita sashen mijinta suka dawo sashen mum aka baro acan,

tagumi ta rafka da hannu biyu hawaye na tsiyayowa daga kumburariyar fuskarta da tuni ta sauya sbd kuka.

tsakiyar dare ya dawo gidan guraren biyu saura,
tunda motarsa tashigo harabar gidan mum dake zaune tsakiyar gadon dakin dad tana jiran dawowarsa sbd dad baidawoba daga gurin daurin aure ya tsaya acan sai anwatse zuwa jibi zai dawo,

saukowa tayi ta fito fuskarta adaure ta fito harabar gidan ta tsaya gaban motarsa tana jiran yafito,

taheer ma jin dawowar dawood din yasashi fitowa dama baiyi bacciba sbd tunanin ya jikin layla yake yanxu,

yana fitowa ko gefensu bai kallaba ya wucewarsa riqe da kwalbarsa dama su keys jikin mota yake barinsu,

kiran sunansa mum tayi baiko sauraretaba ya wuce ya shige palonsa,

daga kwalbar hannunsa yayi ya buga da qasa lokacinda yaga komai na sashen an sauya ansaka sabbi,

qarar fashewar kwalbar tasa mum da taheer qarasowa palon da sauri,

wani kallo ya watsa musu murya a sama yace,

meye wannan?

daure fuska mum tayi tareda gyara tsayuwa tace,

aure akayi maka kuma matarka nanan ciki tana jiranka,
me kakeson mayar da kankane dawood for god sake ace yau kwananka biyu rabonka da gidannan sbd kawai banxar mace.......

tsawar daya daka matane yasa aleeya dake la6e fitowa,

ja sosai idanuwansa suka sakeyi yace,

har abada nur itace rayuwata idan kin daukeni amatsayin 'danki haryanxu to dole zaki kira sunanta da respect,
banida mata aduniya idanba nur ba,
na tsani duk wata mace dazata soni matuqar ba nur ba,
wannan dakike magana akanta itace macen danafi tsana fiyeda mutuwar data rabani da maska,
wlh mum danki zai mutu babu mata idan har ba nur bace....

shut up'''''tace da qarfi cikin takaici da zafin zancensa takallesa cikin kakkausar murya tace,

Nikuma idan nice mahaifiyarka bazaka wulaqanta wannan auren na aleeyaba,
ta wace hanya zanyi maka bayani ka gane auren nan is for your own gud mekakeso bayan wannan fadamin......

NA SAKETA.....shine zancen daya katseta dashi batasan sanda ta 'daukesa da wani mahaukacin mariba saida ya sakashi zubewaba kasancewarsa abuge,

cikin kwalbar gurin ya fadi nan take duka hannuwansa biyu suka fara futarda jini sosai ya dago jajayen idanuwansa dasuka cika taf da hawaye ya miqe
taheer yayi saurin matsowa zai riqosa ya daga masa hannu tareda shigewa daki ya bugo qofa,

tsakiyar dakin ya zube tareda dunqulewa hawayen idanuwansa na gangarowa ahankali yakira sunan NUR dasu MASKA jini nacigaba da zubowa daga hannuwansa.

DAWOOD✅Where stories live. Discover now