'daure fuska siyama tayi sosai tana kallon aleeya tace,
Wat do you think you're doing aleeya?
Abinda Yakamata nayi tun ranar farko banyi shi zanyi yanxu.
'dari biyu siyama ta Ciro cikin school bag dinta ta jefawasu Layla tareda Jan hannun aleeya tace,
Let's go zuciyana tafara tashi da warin dau'darsu.
Fizgewa tayi cikin 'daga murya tace,
Dasu zan tafi so gwara ki dauki 'dari biyunki zatai Miki amfani gurin Hawa taxi kar kafin mukai warin dau'darsu yasaki amaye kayan cikinki..
Wat?,,,,siyamar ta fada tareda matsowa gabanta tana rage murya tace,
Karma kifara tunanin 'daukar wainnan sadaka yallah din Dan haka salin alin kibasu sadakar dazaki Basu mutafi coz wannan abin dakikeyima you're disgracing your self.
Hannu ta qara miqawa Layla akaro na biyu laylar taqara qanqame Bilal har lokacin kuka sukeyi.
Tsaki siyama taji cikin tsawa tace,
Kubar Nan shegu matsiyata.
Miqewa sukayi aleeya ta damqo hannun Layla tareda kallonta Ido cikin Ido tace,
Zan taimakeku zaku bini?
Qura Mata ido Layla tayi akaro na farko,
Sake tambayarta aleeya tayi tana kallonta tace eh zasu bita.Murmushin farin ciki tasaki tareda qara riqe hannun laylar suka nufi mota batareda taqara waiwayar siyama ba ta sakasu mota tacewa driver sutafi.
Wani mugun huci siyama ta furzar tana cewa,
Allah yasa wannan taimakon yazamo muguwar qaddarar rayuwarku ta har abada,
Ina muku baqin bakin Allah yasa wannan shegiyar sadaka yallar tazamo babban bala'in dazai wargaza rayuwarku gabaki 'daya atare...Idan ita Bata zamo muguwar qaddararki ba Toni zanzamo muku muguwar gobarar dazata qone farin cikinku da rayuwarku duka.
Tunda suka shiga motar tayi shiru tana kallon Layla itakuwa Bilal daketa farin ciki ta qurawa ido yaune karo na farko dasuka ta6a shiga mota arayuwarsu.
Babban gidan dasuka shiga yasa ta qanqame hannun Bilal harsuka fito motar.
Kallonta aleeya tasakeyi tareda qara riqo hannunta suka nufi cikin palon gidan.
Ammy da abbanta na zaune apalon suna magana tashigo da sallama hannunta na riqe qam da hannun Layla dake biyeda ita kamar raqumi da akala.
Tsaye ammy ta miqe tana kallonsu Layla dasukafi Mata Kama da mahaukata arikice tace,
Aleeya suwaye wainnan?
Ahankali tasaki hannun Layla ta matso gaban abbanta ta durqusa murya a sanyaye tace,
Abba ina qaunarta tun ranar farko Dana ganta ranar da mahaifinsu ya rasu mukaje Dan Allah Abba ka taimakesu.,
Kallonta yayi cikin kulawa ya tayarda ita ya jawota kusadashi yace,
Aleeya ai nabasu taimako tun.....
Girgixa Kai tayi tace,
Abba sonake kazama uba agaresu inason sudawo Nan taredamu ingantacciyar rayuwar dakake bani nakeso kabasu.
Kallonsu Laylar ammy tayi taga yanda sukayi wani iri kalar tausayi saitaji jikinta yayi sanyi Nan take wata zuciyar ta ingizata data kar6esu matsayin 'yaya kodan 'yarsu qwaya 'daya tal data nuna son hakan.
Shiru Abba yayi ganin tafara hawaye yace,
Shikenan yanxu dai zasu zauna kafin gaba zansan abinyi.
![](https://img.wattpad.com/cover/158188301-288-k195557.jpg)