🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya Daya ce🖕🏼
( Daga kinta sai bata)
✍🏽✍🏽✍🏽
Kulsum Bappah
Umm ImanSadaukarwa ga Ahalin gidan Alh Bappah Azare.
بسم الله الرحمن الرحيم
04
BUNGUDU ( ZAMFARA)Bungudu daya ce daga cikin kananan hukumomin zamfara gusau wacce ta samu yancin zama jiha a 1996.
Mazauna garin Allah ya Albarkace su da noma kiwo da kasuwanci, dai dai da matansu a cikin gida ba'a barsu a baya ba, suna sana'o'in hannu wasu kuma zaka same su suna dinka riga gare ta maza wacce ake kira da y'ar Bungudu zai yi wiya kasamu matar da take zaman banza, gasu sunyi nisa wajen karrama bako basu taba nuna banbanci tsakanin bako da d'an gida.Haka ya kasance akan dattijo mai yakana hakuri da sanin ya kamata, marigayi malam Lawwali da yake zaune a unguwar yamma kusa da gulbi, marigayi mal lawwali yana da mata biyu gwoggo mero da inno Allah ya azurtashi da 'ya'ya shida: hudu daga wurin uwargida Alhaji Bishir Ummaru da kuma shehu, bayan tsawon shekaro masu yawa,domin har sun fidda rai Allah ya Azurtasu da diya mace aka sa mata suna fatima suna kiranta da kyauta,
Bayan shekaru kamar goma sha biyar mal lawalli ya karo aure anashi dalilin yana so ya samu kananan yara atare dashi, gwoggo mero ko sam bata damu ba ta rike girmanta ta yadda da kaddara Abinda ya kwantar wa mal lawwali hankali kinan, nan ya auro inno daga ruwan dorawa, inno yar babban gidace, abin nufi yar gidan malamai ce ta taso cikin tarbiya ta rungumi gwoggo mero a matsayin uwa domin da kadan inno ta girmewa kyauta, shiyasa inno bata faye ma zaman dakinta ba kullum suna tare da kyauta, har Allah ya bata nata rabon ta haifi lubabatu ana ce mata luba,
Lokacin ne akai auren kyauta inda ta aure abokin wasanta sagiru ma'aikacin Asibiti, daga nan haihuwa ta dauki domin har sun fidda rai Da haihuwar nan Allah ya kara bata ciki ta haifo diya mace aka sama ta suna shafa"atu ana kiran ta shafa sunan mahaifiyar gwoggo mero, ba da dadewa ba mal lawalli ya fara ciwo ashe na Ajali ne, Allah ya mishi wafati, abinda ya girgixa iyalan gidan,cikin ikon Allah basu tagayyara ba saboda yadda mal ya jajirce wa yaransa ya hada akwai da babunshi ya biya musu kudin makaranta, wani sain ma kiwo yake sayarwa ya biya musu kudin karatu , Allah kuma ya nufa masu hazakar karatun ne, bishir ya zama dan sanda saboda kishin kasar sa, aka turaashi kaduna, ummaru kuma lawyer ne mai zaman kansa yana birnin tarayya , shehu kuwa lecturer ne a usman dan fodio university, muradin shi daya ne ya zama prof.
Sun cigaba da rike ragamar gidan, ko kadan basu ware inno ba dai dai da sabulu suka sai wa mahaifiyarsu sai sun saya mata, kai ba itaba hatta danginta da suke ruwan dorawa suna cin Albarkacin gwoggo mero,
Rikon shafa kwachukam ya koma hannun Alh Bishir, daga nan ya samu sauyin wajen aiki inda aka mai dashi birnin tarayyaa, tare da matar shi yar kaunar babanshi sadiya, da zaran anyi hutu kuma takan ziyarci sauran 'yan uwanta,
shafa ta tashi cikin kulawa saboda kowa yana son ya faranta wa gwoggo mero rai saboda tace duk mai son ta to ya kyautatawa uwarta ,Luba kuwa babbar 'yar inno tana aure a bagodo dan sarkin bagodon take aure, itace matar shi ta biyu suna zauni cikin rufin asiri.
wacece shafa'atu Lawal bungudu?????
Siririyace lamba ta daya, baza'a sata a layin dogi ba haka zalika bata daga cin layin gajeru, yar das da ita, fara ce ma'abociyar fararen idanu Idan ka kalli idonta zakai tsammanin ta fito daga jinsin larabawan ethopia ne, gashin idonta gazar gazar, da hancinta madai dai ce wanda yai dai dai da doguwar fuskarta, Allah, ya mata Arzikin gashi har gadon baya, kirar jikinta kuwa na kalangu ne, wato tana da fad'i daga tsakiya, kirjinta kuwa a cike suke masha Allah.Allah yayi ta mai son karatu Alhamdulillah lillah domin ilimi kam akwai shi, son karatu kuwa ko Alhuda huda yasan da zamanta,, akwai surutu kam ga sabo tana da fara'a sosai
ma'abociyar son karance karance, idan tana kira'a kuwa ka ce yar sudais ce ko shuraim, ba daga nan ta tsaya ba, hausa novel mujallu kannywood, hint na bollywood,littafan hausa kuwa irinsu magana jari ce, kulba na barna , jatau na kyallu. Duk babu wanda bata haddace ba , shiyasa bata rabo da karin magana azanci zaurance da sauransu..............🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.