41

385 24 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
          [ JIRE TILO]

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Zikiri in an zauna a wani Majalisi

Ibn Umar ya ce; an kasance ana kirgawa ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majalisi guda kafin ya tashi, yana cewa sau dari.
رَبِّ اغْفِرْ لِي، وَتُبْ عَلَيَّ، إِنَّكَ أَنْتَ التَّوَّابُ الغَفُورُ.
Rabbigh-fir lee watub 'alay, innaka antat-tawwabul-ghafoor.
بسم الله الرحمن الرحيم

41

Shafa a zuciyarta tana tunanin miye a jikin mazan da suke kamun baki ita dama ranta yafi son mata sai gashi Allah ya dubeta
  Ludiyar da ta haifa kuwa kamar su daya Binazir haba rawar kai ba'a magana yar kullum tana like da ita Aisah sanda tayi dabaran da NAAZNEEN ta koma hannunta wow kunga yadda ta koma diyar gayu komai too match ake mata rebbons takalma komai iri daya 
Haisam na matukar son ta
Inama ace yarshi ce,
Ana haka tafiya Russia ta taso suka tattara suka tafi da Aisah kafin su tafi Bautar kasa,
Ba abinda yake damunshi yawn ciwon ciki Aisah tace ya kamata kaje Asibiti,mana,
Ya  koma wajen likita yace shi duk iya duben da zaiyi ya duba lafiyarshi kalau
Amma aure kusan shekara hudu abin ma yana bashi mamaki ,
Yace wa likitan gashi Allah jarrabeni da son yara
Abinka da bature yace mai sauki ne ai ko ka manta da *ARTIFICIAL*  *INSEMINATION*miye haka ai *terms* din kune na likitoci
Ya mishi bayani dalla dalla yadda abin yake nan da nan yace ya amince yazo da matarshi,
Amma yayiwa likitan bayani kar ya yarda ya fada mata abinda za'ayi saboda bazata yarda ba,
Ai kuwa ya shammaceta
Ya mata dabara yace suje za'a duba lafiyarsu ne check up aka je akai iya abinda za'a mata suka narka mata Alluran bacci aka gama duk abinda aka mata tsakanin kwana daya an gama,
Ta dawo gida,
Bata san mi ake ciki ba
Tana russia akai sunan shafa  ansa auren husna da taheer   ,
Ana gama nasu BINAZIR da wata guda
Shirye shirye ya kankama domin suna son suyi biki na yan karya ba irin nasu Aisah ba domin Aisah dama ita ba mai son hayaniya bace balle ta tara kawaye,
Itako binazir yar harka ce kawaye kam ba adadi kuma Abin mamaki duk yayan wasu ne saboda haka auren ba karamin shiri za'ayi ba uwa uba angon shima duk irinsu ne,
Lefen binazir da aka kawo ma abin ya wuce fadi inaga ko yar gidan ~INDIMI~iya kaci su ummi sauda za'ayi bikin daughter shiga da fita kam babu kama hannun yaro ga yar dakinta shafa tana tayata kanzagi,
Haka zalika Aunty hafseen Alhajijo gashi dai ba'a kawo kayan jidda ba amma kyallu ta fara yada habaice wa hafsee,
Su irinsu ba irin tsiya bace,
Gwanda ku shirya baza'a kawo mana akwatin da zamu boye mu kasa nunawa ba
Ayya Aunty kyallu ai  kinsan karamin karfe ne dashi bai isa ya hada kai da ku ba,
Kyallu tayi tsuka idan banda rashin ji irin na Jidda ma mi zatayi da zubair,
Aunty kenan ita kuwa ta gani,
  yaro tamkar Balarabe,
Kyawun banza kyawun wofi,
A'a ma'u banda kyawun banza kyawun wofi kam,
Vari na tuno miki kyawun kika gani kema har kika aure ne kika samu su jiddan
Fada mata kam yaya Alhajijo mu fulani ai ba baya ba musamman na yola,
Aunty hafsee tace nayi nan yaya tunda ka karba min,
Ita kuwa hafsee tunda ta fahimci jidda da zubair suna soyayya ta fara tanadi,
Abin mamaki da yake Alhajijo yasan halin mutanen shi suka hada hannu suka fita kunya,
An kawo lefen amma ya hadu domin a boye sauda da hafsee sukayi sayayyar,
An zuba latest abubuwa sai dai bai kai na Binazir ba
Jidda kuwa murna take bata yi tsammanin zata samu hakan bama ,
An kashe bakin kyallu kam batayi tsammanin hakan ba,
An kai na suraj ma ,
Abin ya kara bawa kyallu haushi ,
Sai dai yara suna auren bari,
Ga na gida bazasu aura ba,
Ran wata friday da akaxo meeting din karshen wata
Kyallu ne take wannan maganar bai kamata ace a kyali yaran nan suna haka ba,
Kamata yayi tunda akwai yan mata a zuriar su daina fita suna aurowa bare,
Ana kaiwa wasu Arziki,
Nan yaakime tace gaskiya ne ina bayanki,
Yanzu kinga kamar ke Bintu da falmata suna nan bai kamata ace suraj ya fita ya nemo bari ba
Haka ne kam,
Sanda suka gama Alhaji umaru yace kun gama,
Suka ce eh
Bamu tare daku kyallu saboda banga amfanin hakan ba da ace sunga junan su suna so to da sauki zamu goyu baya mu karva amma dai ace hadi a'a
Munyi auren hadin bai mana dadi ba saboda haka ku bar ma maganar,
A tafo wani maganar ,

Badar kuwa kala bai ce musu ba  balle muhammadu da dama ba shiga shirginsu yake ba

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now