🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
( ÀDDU'AR Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin)A'isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi.
سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.
Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk
بسم الله الرحمن الرحيم44
Masu neman Auren falmata sun zo sun kawo abin da ya dace ba laifi sunyi kokari
A matsayinsu na masu karamin karfi
Sunyi bazata
Ammafa kyallu bata yaba ba saboda ita anata ganin bai yiba,
Falmata kuwa godia tai ta yiwa ÀBDULJABBAR,
Yaji dadi a ranshi,.
Alhajijo ya zauna yaga kayan ,
Ya cewa hafsee ta rubuta abin da babu zai bada kudi a sayo mata wasu,
Bintu kuwa sai iyaye take zuba wa wai wannan kayan bai kyau ba sam 'ya za'ayi ace sun kawo wannan kayan tsabar renin hankali ai ko rabin rabin na jidda bai kaiba,
Ki saurara idan ke bai miki ba ni yamin,
Saboda kuntun gatarinka yafi sari ka bane,
Ke rufa min baki banza kawai,
Niba banza bace,
Kyallu ta katse su,
Bana son shashanci
Yo mama akan mi zata raina min kaya ai shi arziki na Allah ne
Kuma bai zama dole don mun taso a cikin gata ba ace dole mu samu yadda muke so ba
Ki karata ni dai nafi karfin wadan nan
Falmata ta tashi ta tafi wurin
Aunty hafsee suka cigaba da tsare tseren su ansa biki wata daya kacal
A ka cigaba da shirye shirye
Alhaji Bukar ne ya dau dawainiyar gado
Mahaifinta ma ya mata gadon ta tashi da gadaje biyu
Jiran rana kawai ake yi,
Alhajijo kuwa yayi bakam abinshi ya zuba ido wa bintu,Aisah dai yanzu ta faso gari itama
Tasan miye aure
Nan da nan ta murje tai kyau
Idan aka ga ISLAM da MUSLIM za'ayi tsammanin yan wata uku uku ne tsabar girma,
Gashi Allah ya taimaketa basu da riki ci kullum tare dasu safiya suke kwana,
Ta fara samu chanji a jikinta amma batayi tunanin komai ba,
Yaana kwananta biyu a wurin kaltume
Suka maidata wurin yaakime
Tana ta yatsina ita zamanta da yaana bazai yiwu ba ,
Yarinyar da ba mutunci ne da ita ba har yaana zatai magana kaltum ta hanata suka dai lallaba suka bada hakuri,
suka tashi suka tafi,
Tun daga nan dai kowa harkar gabanshi yake ,
KARE BANI KORAR KA BANI BAKA ABINCI NA
Jidda ta sauka lafiya sauran BINAZIR domin itama ta dawo gida haihuwa
Ba yadda mijin baiyi ba ta zauna acan Abuja ta haihu tunda gashi ga iyayenshi,
Fir take domin BINAZIR
Tana matukar kiyaye abinda zai hadata dasu balle ta haihu ta koma cikin gidansu ta zauna ,
Duk da cewa familyn yan boko ne amma suna fama da matsalar tsegumi ko don mata sunfi yawa ne,
Abu na faruwa fah zaki ga
Wannan ta kira wannan wannan fadawa wancan ,sai kiga abu ya karade kan yan uwa abin takaicin basu tabbatar da abu suke dorar wa,
Shiyasa ita kuwa tace ina!
Gwanda ta dawo wurin iyayenta ta haihu a gaban su duk runtsi zata samu kula
Saboda ta lura uwarmijin nata macece mai kishi bata kaunar taga BINAZIR da danta suna wasa suna dariya nan da nan sai tayi kicin kicin ta bata rai tun basu fahimta ba har suka fara fahimta
Wurin ummi sauda ta zauna
Kudi ya tura mata ta Account dinta na sayayyar kayan baby domin tun kafin ta taho ya bukaci yayi shawara da maman nashi akan ya kamata fara sayayyar kayan haihuwa,
Budar bakinta sai tace wani kayan haihuwa kuma ba gashi ko na kayan auren bata gama dinkawa ba,
A'a ba kayan uwar ba kayan jariri fah nake fada
Owo to ka bari zan kira hajara sai tayi list din da kayan da ya dace a saya,
Yace to yana zaune ta kira hajaran sukai magana tace zata tambayi mijin ta idan yaso ko wuse market ne ta shiga,
Tunda yaji an anbaci wuse market yaji ranshi bai kwanta ba maimakon ace su shiga shoprite ko silver bird,
Bayan kwana biyu da maganar ne suka nemi ya basu dubu dari biyu,
Abin mamaki gaba daya local kaya suka sayo kuma bai kai na kudin ba
Tsabar bakin ciki cewa yayi su ajiye a wurin idab haihuwar tazo sa karba
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
De TodoLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.