🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi:Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa;
أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
بسم الله الرحمن الرحيم
37
MAIDUGURI
Amarya ta koma gidan chuwunta anan za tai zaman Amarci ita da kawayenta sai masu mata hidima na katsina sholi itama tazo bikin
Angwaye sun kai musu kayan tea manyan gidajen milo ovaltine madara suger
Lemuka na kwali dana robobi katan katan na entertainment din kawayen Amarya ,
Ranar farko an gasa musu TANDERON RAGO ,
Sai HALEEB na Amarya
waashe gari kuma kaji aka gasa musu amma gashin indiyawa da ake yi da madara TANDUURI CHICKEN
sunji dadinshi sosai Haisam ne ya bawa SULAIM ta musu
Wannan dawainiyar duk ta Angwaye ce,
Abin ya gayatar sosai
Dr Aminu shine Alwalin ango haisam
Anyi waleema an debo masu wa'azi mata sun yi fadakarwa mai ratsa jiki musamman wa Amarya,
Tayi shigan Alfarma lace ne mai dandashe shen tsada sky blue an mata Buba tayi kyau ba'a mata heavy make up na haukan nan ba an nade mata jiki da liyyafa pusher pink
Takalminta madaidaici na kamfanin CK da purse dinshi shima pusher pink wara waran zinari ne da sarkatar harda zobben yatsu sai sarka kafa wanda ya kara fidda kunshi nata walima tayi armashi, hujin kunnenta kuma yasha barema duk na zinari
Dayan hannun kuma fashion ne na hannu sky blue Amarya ta fito sai sheke takeyi Allah yasa taaji abinda ake fada kawayenta sun kewayeta akan carpet yayinda mai wa'azi da iyayenta suna zaune akan rantsatsun kujeru
Idan zaka shiga harabar za'a mika maka jakar sevenoir da take kunshe da hijabs dasu turamen zannuwa,
Anyi an watse lafiya,
Waashe gari daurin aure
Matar Dr Aminu sun zo da tawagarta sun kaddamar da kayan wushe wushe
Shanu guda uku buhun chin chin da randuna shake da dublan Alkaki geriba, nakiya dakuwar gyada,
Kayan miya kwando kwando buhunnan shinkafa da jarkokin mangyada gishiri maggi katan katan kai harda omo na wanki wanki bayan su daro fulatai
Wannan al'ada ce da akeyi a maiduguri gidan maza ne suke kaiwa gidansu Amarya domin sune suke dauke dawainiyar abinda za'a ci ranar daurin auren duk dai abinda ake bukata an kai wa Adda Aishatu sun bada tukwici mai tsoka,
Da daddare kuma sun dan shirya kwarya kwaryan WUSHE WUSHE Amarya da kannenta da yayyenta ne nan ma tayi matukar fituwa Shaddace dinkin yan MALI zinare kam har ta gaji da sashi
Anyi kade kaden da bushe bushe haka zalika an kawo kayan WUSHE WUSHE na biyu su BISCUIT SOYAYYEN KAJI,
CHEWING GUM,
CHOCOLATE MASU TSADA,
GORO SAI ZANNUWA A AKWATI SET UKU,
ZAMFARA
Anata sherin ARABEYAN EVE Amarya tasha wata After dress mai matukar tsada yar kasar oman duk hajiya kyauta ce ta sayo mata Tare da wasu set din AZURFA WARWARO YAN KUNNE ZOBBA
SARKAR KAFA ZOBBAN KAFA,
JAKA DA TAKALMI SUMA SILVER
kawayenta kuma ankon After dress ne da sky blue din gyale ,Yayi Armashi sosai AN CASHE DA NANCY AKRAAM
Amarya kugunta kamar zai karye saboda rawa musamman da D.J yasa wakar nancy akram cikin EL DONIA HELWA an mata barin kudin musamman wanda ya wakilci ango da ya shigo,
Nehal da menal sunsha rawa sosai RAGO NE A KAFE ANYI BARBIQUE
masu sha'awa suje a yanka musu
Abin ya kayatar matuka.
RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA,
AN saba lokacin daurin aure HAISAM ne babba shi za'a fara daura auren shi a fadar mai martaba SHEHUN BORNO,
abin sha'awa sadaki dubu ASHIRIN,
ANGWAYE sunyi anko, ana gamawa suka dunguma Airport MALAH AIR LINE masu daukar mutane 550 aka nufi. Zamfara an daura auren a babban masallacin zamfara itama sadakin dubu ASHIRIN,
anci an sha
Amarya sai da la'asar za'a kaita,
Angwaye da wasu abokansu sun shiga MALAH PRIVATE JET,
sun nufi YAANKARI GAMES RESERVE BAUCHI,
za'ayi RECEPTION turawa abokan haisam sunji dadin abin sosai sunyi kalle kalle namun daji,
Can maiduguri kuma an debo yan rawan Al'ada GANGA KURAH,
sun zo suna rawar Al'ada kaimin bare bari ne yake tashi,
Kaltum da da ummi sauda kaya iri daya suke sawa tunda aka fara bikin
Yaana tayi kuka har ta gaji,
yaa kime ta kira Aminiyarta ta mata kwatancen wani matsafi a nijer yaana taje insha Allahu zai mata aiki ba sanya taje kuwa ta mishi bayani yace za'a dace amma yarinyar tana da Addini mijin ne boko ya ratsa shi zaiyi aiki amma ta zuba ido sun sake mashi kudi sosai
Yace ke dole ma ya aureki ya furta hakan ne lokacin da yaga zunzurutun kudi ,
Tayi mishi Alkawarin dawowa,
To ya kime da taji sakon malami ta sake kamar babu abinda yake damunta
ana hidima da ita ta kira kawayenta yan bariki marassa da'a ,
La'asariya tayi anyi shirin yin KALABTU
An fiddo da Amarya ansa mata zanen Alwali UMAIR NE Alwalinta an shimfida tabarmai a tsakar gidan Adda Aishatu an nemo bahu an daka karkashi an kwaba shi a baho aka Ajiye,
limamin masallacin MALAH ESTATE ya iso za'a fara KAULIli KAULILi ya kewaye ta da qur'ani har sau uku ya mata Addu'oi ya tofah ,
Sai Adda Aishatu tazo ta daago kanta tace mata cikin barbarci
AISAH MAIDA MAIDA KAMUWAYE,
WAI Aisah sarauniyar mata
KO MARI DANE
FANUM MARO MUWAN
KANADI GONE,
wai ki zama kurma ,
Ki zama makahuwa
Sai HAKURI, nan baba kyallu ta zo ta shafi wannan ruwan karkashin ta mika wa kaltum kudin
Haka dai yan uwa suka zo suna shafan karkashi suna mikawa uwar Amarya
Kannen sauda da yayunta mata suka kawo goro chingom alawa turamen zannuwa a cikin daro.
Aka tayar da Amarya aka daurata akan turmi baba kyallu da matar muhammadu sune BABANAI KANNEN UBA,Suka zo da kwabeben lalle da aka kwaba da ruwan turare sai kuma wani lallen a daron silver an kama hannun ta an shafa mata,
zabiya kalala ta rangada guuda
AYURURII
yan biki sunata waka KARUMBO KARUMBO KALABAIYE
aka matso da lallen da
Yake cikin daron silver aka tsoma mata kafa
A zaamanin da wanka ake yiwa Amarya amma yanzu kai ya waye ba'a wanka sai a tsoma kafa,
Aka hau kewayeta da turaren wuta a cikin manyan kasake
An gwaye sun dawo ana shirin tafiya dauko Amaryar Badaraldeen Yaa kime sauda matar usman sai yayar kaltum mamansu neehal sune zasu tafi suma PRIVATE JET
suka shiga sun isa 6 dai dai na yaamma Amarya tasha kukan rabuwa da iyayenta aka sako ta a jirgi tare da kawayenta sai kanwar inno daya da kanwar gwoggo mairo matan Alwalinta na KAURAN NAMUDA
Su haj kyauta Amarori kirjin biki,
Da kawayenta, suka lula sai birnin shehu.
Takwas sun isa Angwaye kuwa suna can suna ta hada hada sun sauya shiga zuwa sky blue din shadda sai sheki take yi anyi shawaran a hada amare a waje guda kafin kowa a mikata gidanta,
Sashen kakanunsu aka kaisu wurin shatu domin. Ba karamin kara akai mata ba,
Anfara shigowa da AISAH isowarsu shafa kuma akai can da ita,
Sun sanar musu za'a hadasu da matar yayan muhammdu haisam za'a musu maraba lale na Al'ada shafa'atu liffayar da aka nada mata ya ishe ta,
Aka zaunar da ita akan KILISHI mai dankaren taushi
Sai taji kamar murya Aisah na ce mata AHALAN WA SAHALAN WA MARHABAN BIK ILA USRATI MALAH ZAUJATU BAANZIYEEINA MIKI MARABA DA SHIGOWA MALAH FAMILY
MRS BAANZIYE
kawai ta dago kanta AISHA ABUBAKAR SHAREEF!!!!!
na'am
Aisah ta kyalkyale da dariya,
Shafa ta nunata da yatsa dama muhammadu yayanki ne
Kwarai kuwa
Kin tuna jallabiyar da mukai anko kikace wani ne ya saya miki a oman
Tundaga nan nasan YA BADARALDEEN ne
SUka rungumi juna amma kin shammaceni,
Alhamdulillah naji dadi yanzu Ammi ce sahratee ( inlawa ta) eh
Haba har na tsorata yana ce min wai shi dan wani kauye ne kusa da SAMBISA FOREST
Eh yayi ne don ya batar dake baya son kisan inada hannu a aurenki saboda nasan ra'ayinki nason karatu da kin aure sai kin gama karatu,
Tana kokarin cire lifayyar
Aisah ta hanata cirewan tace za'aita shigowa kuma za'a kaimu wurin iyayenmu maza su mana fada tace to na nutsu kenan?
eh
An musu nasiha sosai akan yadda zasu kula da mazajensu da kuma yi musu gargadi duk dai akan HAKURI
Dr Aminu yace SOYAYYA TA KARE
DAGA YAU KUSA A RANKU RAYUWAR AURE GABA DAYANTA
HAKURI CE, KUMA IBADA CE,
IBADA KUWA BA'A SAMUNTA DA DADI.Allah ya tabbatar daku akan da'a da hakuri kowa yayi nashi
Can mazan suka shigo HAISAM DA BADARALDEEN,
AN musu wa'azi sosai tare da sanar dasu nauyukan da ya rataya a wuyansu,
Iyayen sukai maza suka shafa Addu'ar domin sun lura yaran zamani ne, sun kurawa matayensu ido haisam kam da yake yafi rashin kunya ko kifta idon baiyi
Aka nemo hajja ta kama kowaccensu ta kaita sashinta tare da rakiyar Alawali hakan ma wai bidia ce anfi son wacce zata kaika daki ta kasance mai hakuri wacce bata taba yaji ba,
Nan kawayensu suka Shiga aka fara hidiman kwanan Amare
An shigo musu da kayan sauka na Al'ada
Abokan angwaye sunje anata tsiya duka ga dukkan Alamu babban Aminin Ango ya kyasa husna sai zolayarta yake yi ,
Rabin kwana akai ana hidima,
Washe garin ya kama ranar da Angwaye zasu je gaisuwaR TASANI gidajen Amare na haisam aka fara shine babba sunkai kayan Al'ada da akeyi
Sannan suka karisa inda aka sauke yan zamfara an kai musu kayan Al'ada iri iri bayan angwaye sun fita ne haj kyauta ta jagorancin umominta da matan yayunta wurin kaiwa DOKKE,
DOKKE al'ada ce da fulani suke yi YAYIN BIKIN AUREN YAYANSU MATA, sunje anyi gaisuwar mutumci yaa kime ba laifi ta karbesu a sashinta za'a yi akwatuna biyar na shaddodi na iyayen baanziye dr Aminu zuwa Alh umar da muhammadu,
Set din gadaje uku uku da fridge gas cooker kayan kitchin kwachokam kwanukam abincin su sallaya bargo duk uku uku na iyayen ango mata
Yaa kime duk da hasidin iza hasada taji dadi saboda karan da sukai mata gashi dai ba danta bane amma sun mata komai na uwa sai turamen zannunwa da kwanukam cin Abinci ataimaki mai gadi set dari da hamsin kowa nata hamsin hamsin,
Da su chin chin dubulan sai jarkoki na man shanu,
Mama sauda ma taji dadin karansu na fulani,
Nan hajita kyauta tace akwai trailer a waje kayan gara ne da akwatin shaddodi na Ango ta ciro takardar banki na kudin chefani. Miliyan biyar ne akai ta mikawa yaa kime sukai ta godia lalle EFCC BOSS YA FIDDA kanwarshi kunya,
Kuma a yau zasu koma an basu nasu tsarabar sun bar Amarya cikin kuka
An bada amana wa sauda itace uwar dakinta,
Abin yazo inji mai tsoron wanka,
Ana sallar isha Abokan angwaye suka raka su,
Abin mamaki yaane ce labe tana jira Haisam ya fito raka abbokanshi, sun fito kenan tai wuf ta watsa wani abu a kasan kofar yadda dole sai ya tsallake kafin ya wuce ba bata lokaci ta juya ta fice tana dariyar keta
Bawan Allah yazo zuciyar shi daya ya wuce sai jiri ya kamashi............Ta'aliki
Zaba
Watsa
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.