🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Zikiri in an zauna a wani MajalisiIbn Umar ya ce; an kasance ana kirgawa ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majalisi guda kafin ya tashi, yana cewa sau dari.
رَبِّ اغْفِرْ لِي، وَتُبْ عَلَيَّ، إِنَّكَ أَنْتَ التَّوَّابُ الغَفُورُ.
Rabbigh-fir lee watub 'alay, innaka antat-tawwabul-ghafoor.Ina kuke
Saratu Ibrahim
Matar Iro
Hauwa kiman hasan
Haufi
Nakune wannan shafin
Allah ya bar kauna32
Allah kenan fa'allul lima yurid a duk lokacin da yaso,yaga dama,
Aishatu bana son ki ringa shiga hidimar su yaa kimen nan duk abinda zatayi ki sa mata ido ki barta da bakin cikin da ya isheta domin kinsan idan hankalinta dubu yake yanzu ya tashi,
To amma hajja idan fa ba'a taka musu burki fa iskancin gaba zai nayi,
Shine daga karshe zasu zama CIWON IDO sai hakuri,
Allah yasa ta gane,
Yauwa Amin
Yanzu mu nawa zamu tafi,
Yaa kurah kyallu inaga shatu ya kamata ace ta je,
Eh inaga hakan
Kinga sauda kam bazata samu damar zuwa ba,
Eh wallahi babu dama,
Ai na manta shekaranjiya surkayenki sun zo godia wa Alhaji,
Ayyah ai sunji dadin biyawa baban hajir makkan nan da akayi,
Ah toh ai shima dan mune,
Eh haka ne hajja ai ba kowa ne yake da wannan karar ba,
Da wannan.
Suna tattaunawa sai ga saudatu ta shigo
Nikam Adda yaya kike ganin zamuyi da gudumawar nan ne?
Eh gaskiya kinga ko mun tafi dashi kaya zai zame mata idan suka zo dawowa,
Haka ne Adda,Hajja tace to mi zai hana idan kun sayan ku barshi anan in yaso idan tazo ta taradda abinta,
Yauwa haka za'ayi to.
Amma fah gaskiya idan suka dawofa zamuyi sabon suna,
Haba ku kuwa miye sai kun sake yin suna ai tunda mai haihuwar ce, zata haihu anan dinma,
Sauda tace a'a hajja mukam zamu yi suna ko Adda?
Tabbas suna ya zama dole,
Ku kareta can!
Ai kune iyayen sai yadda kuka yi,
Sauda tace Adda ya kamata a fito mana da Anko
insha Allah,
Kafin ku dawo zan sa kanin Baban hajir ya kawo mana daga shagonshi sai mu zaba,
Tafiya ta kasance ranar Laraba suka gama shirye shiryensu
Yan uwa da abokan Arxiki suna ta zuwa musu barka,
Ba anan akai haihuwar ba Amma abin Arzikin da suka tara na barka bazai kir gu ba,
Saudat ma keken tafiya da gadon jarirai ta saya nata kenan,
Umar kuwa Akwati Biyu yayi,
dayan kayan jarirai ne haddadu masu rai da lafiya,
Daya akwatin kuma dogayen riguna ne
Da shaddodi sanegalise,
Adda Aishatu ma wasu kayan wasan jarirai ta saya mishi,
Hajja dai full set na Daham ta saya mata sai Awarwaro da zobba daban suma, yaron shima akwati aka shake da kayan shi,
Ba laifi shatu da yaranta sun hada nasu suma kyallu turmi uku ta sayo,hajja tai akwati itama da atampopi da kayan jariri tace a sawa maigidanta,
Dai dai da muhammadu da yake dan makaranta sanda ya sayo wa dan shin riguna hajja taji dadin hakan domin tasan muhammad zai bi sahun yan uwanshi,Alhaji kuwa nashi daban ne,
Ku san yan maiduguri da girmama mai suna,
Ya bashi gidan mai irin na haisam,
Filaye guda 2 shi da uwar shi
Banda sutura kuma akwati hudu ya musu kar kuga dai abin arziki da MUHAMMADU BADARALDEEN YA SAMU
Kunsan kowani yaro da Arzikin shi yake zuwa,Fanna da yakurah sai kanwar hajja guda daya da matar Dr Aminu kyallu Aishatu sai kanwar saudat yasmeen ta wakilci yarta da kuma shatu,
Sune suka lula zuwa oman
Yaa kime kuwa tsinke bata bayar ba,
Kuma ko ajikinta
AN TSABIRI KAKKAUSA
Gashi duk abinda aka bayar sanda aka nunawa Alhaji yasa Albarka tare da godiya aka ajiye a sashin maigidan
Nan yake cewa hajja bai ga na uwar da ba,
Wa kenan?
Matar Bukar.
Bata yiba,
Akanmi?
Kawai ra'ayi,
Amma ya kamata kina nuna mata irin wadannan abubuwan saboda kinsan ta fito gidan kananan mutane ba lalle tasan ana hakan ba,
Alhaji tasan anayi kishi ne kawai yake damunta,ta kwashi yadda sukai da akace ta haihu,
Allah ya shiryeta wato dalilin da kika ga bana son ya sauta,
Bana son ace ya saba da sakin ba girman shi bane ba kuma mutumcin mu bane,kuma kowa da kika gani da mummunan halinshi ake zama dashi tunda ba'a taba canza halittar mutum da Allah ya halicce shi dashi ba,
Haka ne,
Allah ya ganar damu gaba daya,
Amin.
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
DiversosLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.