🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕Gaskiya dayace 🖕🏼
( daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Umm Iman
TUNATARWA!!!
ADDU'A AKAN ABOKAN GABA
ALLAHUMMA MUNXILIL KITABA SARI'UL HISABA IHZAMUL AHAZABA ALLAHUMMA IHZAMHU WA ZULZULUHUM.
Kuna heart dina yan dakina💙❤💛
Sameera muhammed
Mrs sulaiman
Aishatu Halilu
Mrs Abubakar
Allah ya bar kauna 💞💞💞💞💞
11
Kan ubancan!
Furucin yaana kenan,
Yaa kime duk iya kokarin ta cije abu ya faskara, tace durun uwata inji matsoraci.
Nan Alh Umar yace ya zaku mayar mana da gida kamar na maguzawa,
Yaa kime tace sam bazai yiwu ba,
Kanwartawa guda daya,
Ina!
Adda Aisha tace yanxu ke kime a gaban hajja kakar kike wadannan zage zage idan baki ji kunyar idon mazajenku ba , ai gyaji kunyarta,
Yaa kime ta rasa abin yi,
Nasan wannan duk munafurcinki ne, ta nuna kaltum,
Yau mi zan gani Bukar? A gabana iyalanka suke haka,
Ya rasa yadda zaiyi don kullum Kime ta mishi rashin mutum ci idan ya fadawa hajja kaka sai tace yayi hakuri,
Kafin ya bude baki yayi magana tuni ta ja hannun kanwarta yaana da fuskar tai chaba chaba da hawaye, zo mutafi ayi mugani.
Alheri zamu ga inji umaru,Yaya wai dama matar nan ba rusuna tayi ba ai ni nayi tsammanin yanzu tayi hankali,
Saudat tace tana nan yadda ka santa a baya,
Kaltum ce bata biye ma ta amma idan son ranta ne kullum ana cikin tashin hankali da hayaniya,
Yaya Allah ya kara maka hakuri!
Hajja kaka tace ka cigaba da hakuri kema kaltum Allah ya kara miki hakuri,
Ita ko kyallu da yake tafi yaa kime hikima da wayo sam bata nuna abin ya dame ta ba,
Allah kadai ne masanin sirri, masanin gaibu amma da zata amayar da kunci da takaicin da take ji a zuciyarta kai da sai tafi yaa kime rashin hankali.Aisah kuwa da kyar take futar da numfashi.saboda bata taba kawo haisam A ranta ba, domin tana daga cikin wanda suke tsammanin binazir yake so,
Binazir kuwa sai washi bake take, tuwonta manta,'Ya'yan kyallu kuwa sai harare harare suke yi kana ganinsu kasan hassada suke muraran,
Can hajja kaka ta numfasa tace,
Kai mai zamfara yaya za'ayi kenan?
Umaru inaga zamu nemi Adire shinsu sai kaje neman auren .Nan Adda Aisha ta fara barkwanci.
Umaru kasani gidana zaka xo neman Auren chiwu na, kuma ban dauke maka, komai ba da ake yi na Al'adah
Kaltum ta lura da yanayin da Aisah take ciki.
Tana Allah -Allah kar a gane,
Saboda tasan za'a rina tunda ba dama ai mata zancen aure sai ka ga nan da nan tayi kicin kicin da fuska.Binazir kuwa ta fara cewa yauwa Aunty yaakurah mu kuma sai mu fara zancen fidda anko. Ko bintu? Yaa kura? yaakura yar Adda Aisha ce, ita bare take aure
tace eh sosai ma inada kawa a england a kamfanin sheraton inaga zam mata waya ta turo mana latest din AURA WAX.eh
Aunty harda lace zamuyi fah,
Nan suraj yace ke gandoki ba'a sa rana ba har kuna shirin anko,rashin hankalinki.Yayi yawa, saudat tace kul daina taba min 'ya kasan zan saba maka, nan ta jawo binazir ta kwantar da kanta a kafadar ummi saudat
ke kuma Yaa kurah harda daurewa karya gindi.
Bintu kuwa kamar basu wurin,
Nan aka cigaba da tattauna lamurra, Aisah kuwa Allah -Allah take a watse ta zubar da kwallan da ya taru mata,Wallahi da ba don cin fuska bai da amfani ba, da ta disga shi,
Kuma ta kara daurewa ne, saboda makiya tasan tana cewa uhm, sun samu nayi,
Kuma mahaifiyarta bazata taba jin dadi ba, uwa uba ummi tana son su tsakani da Allah,
Bazata taba bari a fahimci halin da take ciki ba.Saboda kullum a cikin gwasale ta yake,
Shiko haisam satar kallonta yake,
Yana tunanin ko zaata ki amincewa.
Ya dai kasa gane miye a fuskarta,
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.