🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'o'in Tashi daga Barci.
"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"
Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.
بسم الله الرحمن الرحيم35
Alhamdulillah gida yayi kyau da kyar iyayen Alhajijo suka yadda suka koma sabon gida,
Hafsee an mata sabon kayayyaki sunyi kyau sosai ta sa a ranta cewa zata zauna da kyallu tsakani da Allah duk abinda zata mata,zata kyaleta ko don Albarkacin iyayenta da mutuncinsu,
Kyallu kam tana kallon tarairaya iri iri a wurin hafsi cikin tana ganin iyaye ne har ta fara sha'awar ina ma itace sai dai kamar bazata iya ba take gani.
Kuma fah da gangan suke mata hakan don ta ankara itama Alhamdulillah
Alllah ya taimaketa ta fara tsinta itama tunda kinsan duk maccen da tasan kanta macece idan kuma mai hankalice zata so ace ba'a barta a baya ba
Kwance tashi
Hafsee ta haifo danta namiji,
Kyallu kuma tana kunshe da cikinta gashi wannan bai zo mata da laulayi ba
Alhajijo ya daina mata tsiya sai jifa jifa idan tsiyar shi ta motsaMAIDUGURI
lokaci na tafiya daukaka da Albarka na kara shiga Ahalin gidan Alhaji malah sharif umar ya ci gaba da rike dawainiyar gidan shi kuma Bukar kullum na zirga zirgan kasashe harkar mai da kasuwanci,
Bukar ne da umar da muhammed ,suke shawara a falon Alhaji sukan saka muhammad ne a ciki saboda ya koya shima ,
Shawara suke yi akan suna so su yalwata gidan su kara fadadashi amma wani Architecture yace musu kawai su nemi fili a wani wuri su saya sai su shata estate kawai amma miye ra'ayinka Alhaji,
Don muna son duk zuriarmu ace suna zaune wuri guda mazan mu da matanmu Alhaji idan son samu ne har ma'aikatanmu ace suna kusa damu. Saboda inaga hakan sauki ne a garesu,
Alhaji ya numfasa ya fesar da iska Alhamdulillah ko yanzu akace babu ne nasan zuriata bazata tagayyara,ba
Naji dadi na gode muku da hadin kan da kuke dashi,
Muhammad kaini karami kaga abinda yayunka suke yi don Allah ku cigaba da hade kawunanku
Insha Allahu Alhaji,
Allah ya yarda yanzu abinda ya saura maka kawai ka ajiyi iyali.
Umar yace da naso ace sai ya kammala karatun shi,
Eh ba lalle ba indai yana da matar da yake so ai zai iya fada ayi magana saboda ai dama sisin shi bazai shiga ba,
Kune masu auren
Haka ne
Akwai ne kayi shiru
Eh akwai kanwar mijin kyallu a yola,
Masha Allah
Abu yayi kyau
Yanzu kai umar tunda kaine zaunanne ka wuce gaba Allah ya sanya Alheri
Suka amsa amin
To Alhaji inaga zamu samu fili a fara zuba tubali
Eh akwai wani fili a can gaba da GRA kadan inaga kai umar zaka san filin
Eh nagane shi
To na bar muku shi ku gina don wannan filin inaga zai yi gida a kalla Arba'in ko ma fin hakan
To Alhaji mun gode Allah ya kara lafiya,Allah ya jikan mahaifa,
Yace Amin
Allah ya muku Albarka,
An dasa tubalin gini an fara kewaye filin ma'aikata ne kashi kashi ana ta faman aiki an fidda zanen yadda nasun zai kasan ce,
Alhaji malah aka zuba mishi manya falo har guda 3 daya na shi ne na kanshi wanda zai na ganawa da iyalanshi zallah,
Daya kuma a ta farkon nanne wanda zai na ganawa da talakawanshi,
Sai kuma wani babba wanda a kalla zai ci setin kujeru biyar ,
Wannan sunyi ne saboda ana haduwa duk karshen wata ana tattauna abinda yake wakana da kuma warware matsaloli
Aiki na ta cigaba
Sauda ta kara haihuwa ta kara samun namiji yaci sunan kakan Alhaji mala suraj
Kaltum ta huta sosai sai bayan shekara 5 da ikon Allah ta samu ciki ta haifi mace Aishatu sunan Adda Aishatu ake ce mata Aisah tabarakallah akwai kyau kam sosai Allah yasa ta sami sirkin jinin larabawa ita ba irin BADARALDEEN BANE
Da ya dauko bakin kanurai,
Aisah ta kasance wankan tarwada ce sai tsayi bisa ga dukkan Alamu zatai gashi
Acan yola ma kyallu Allah ya Albarkaceta da 'ya'ya uku duk mata
Hafsee ma ta kara namiji daya
Abin duniya ya damu kyallu itama dai ace ta samu namijin nan ko daya ne,
Ita kuma hafsee Allah ya zuba mata son 'yaya matan gashi Allah da yaso yaran kyallun sunyi kama da ubansu,
Amma fa yana mata tsiya yace Allah ya soni baki haifo mai kama da ke ba,
Yaa kime ma ta dauko kanwarta yaana shekarar 3 da kadan ta darawa Aisah ba tare da bata lokaci ba kaltum ta samu wani cikin macen ta sake haifa yaa kime kamar zata kona kaltum gashi yanzu ta fara jin hausa tana iyawa kadan kadan
Binazir ta haifa sunan mahaifiyarta
Tab baba Aishatu ashe kunsha kallo
Ina kika ga kallo
Ai kishi mun ganshi iri iri yaa kime kamar tayi hauka ai yanzu da kuka girma abin yayi sauki,
A hakan baba Aisha kinsan fah wani sain idan muka gaisheta da kyar take amsawa
Ai da sauki yanzu bude kafadarki nagani inaga ta dama ne,
Kinga wannan tabon Allah ne yaso ki,
miya mai zafi ta watsa miki a fuska taso ta watso miki saboda so tayi ta lalata miki fuska,
Kin gane kin shiga kicin dinta ne ita kuma tana girki sai kiga je kina ta mata surutu da gwalabe tana ta miki
Tsawa kika ki tafiya sai ta debo miya mai xafi zata watsa miki kenan maman ki ta shigo tana daga miyar ta kira ki kenan sai kika juya to juyawar yayi dai dai da watsanwan
Kuma taci gaba da tauna chingom wai kadan kenan indai baki hana yarki shigowa ba,
Ta kama ki tana fituwa ni kuma sai gani tana gani na maman kin tasa kuka
Tace wannan wace irin kiyayya ce Adda?
na bata hakuri amma ta hada ni da Allah kar na fadawa kowa,
Amma kinsan mi Ammi tace min
Wai miya ce ta zube min a kafa,
Hmmmm
Ingaya miki
Dagangan da ganganci take lalata abinta a daki tunda tace bata haihuwa balle tana cin moriyar shi saboda idan abu za'ayi zai ninkawa kaltume saboda yara,
Akwai ranar da ta fita taje gidan kawarta sai ta dawo tace an sace mata mota kuma hada baki sukai da kawartata,
Kanin kawarta ta ya dauki motar yaje ya boye sai an kwana biyu su canza mata fenti su sayar,
Kinsan Allah ranar har tv dinta ta fasa da gangan lokacin yaana tana karama ina jinsu tana tade wa sulaim wai Auntynta ta fasa tvin fallonta amma tsabar karya sai tace wa Bukar tana zaune a daki taji karan faduwar shi,
Anan ne ma yake mata magana yace abin na ban mamaki kime ba yara kike dashi ba amma kullum abun kine yake fara lalacewa,
eh ban dasu ko gori zaka min
Ina ruwa na nine mai bayarwa da zan miki gori koda yake ba Allah ne bai baki ba kime kice kika lalata mahaifarki da kanki,
Bata son a tuno mata wannan maganar saboda ranta bace yake,
Sai dai har yanzu bai isheta ishara ba,.
Gashi ba dama wani daga dakinku yayi ciwo itama sai ta kirkiri ciwon,
Ta tafi asibiti likita ya karbi kudi a banza,
Haka dai rayuwa tai ta kasancewa,
Binazir xaki tuna lokacin da Alhaji ya rasu?
Eh ina dai tuno wani abin amma ai ba'a nan bane
Ashe da wayonki lokacin?
Kinsan fah har gobe gani nake yi kamar bai rasu ba,
Ko dan saboda ba'a nan ya rasu ba,
Amma ai yayi kyakyawar cikawa,
Daren Ashirin da bakwai ranar juma'a hakan ma a dakin ka'aba yana dawafi kuma ciwon ciki,
Baba Aisha da'ace ana murna wa mutuwa da an mishi shikam saboda irin wannan mutuwar ba kowa ke yinta ba,
Sai bawan da Allah ya zaba,
Baba Aisha ta goge hawayenta,
Allah ya jikan shi bda rahama,
Allah yasa idan tamu tazo mu samu irin kwatankwacin shi
Amin Binazir,
To mama shatu fah ?
Kamar yadda kiga tana yola mahaifiyarta ce ba lafiya ta samu ciwon shanyewar bangare ya kasance su biyu ne daga inna danejo sai ita,
Inna danejo kuma tana dakin mijinta sai dai taje yini ta koma abun har ya zama musu jiki,
Shine mama shatu ta koma,
Amma zaki ga tana zuwa ai jifah jifah tunda akwai mai aikin da take kula da innar,
Allah ya bata lafiya,
Amin
Idan kukai halin mahaifiyarku kun huta tana da kawaici sosai takwarata Aisah halinta ta debo ,
To nifah
Ke kam ai Baffanki umar ne kika debo,
Baku da hakuri sha yanzu magani yanzu,
Shiyasa yaa kime tafi wasarki ai,
Dadin dadawa tace kina kama da kaltum shiyasa idan ta ganki take kara jin zafin ki,
Ah toh ba yadda ta iya dani kuwa,
Ai baba da ba don kuna taka min birki ba da nayi maganinsu ita da kanwarta mummunan nan
Kinsan wai ita Ala tilas yaya haisam take so,
Kai ina!
Amma ni kaina fah nayi tsammanin Ibraheem ke yake so
A=a shakuwa ce kawai wallahi Baba
Eh na yarda shakuwarci tunda dama ke kam ai yar gidan sauda ce,
Tana matukar kaunarki ban sani ba ko don bata da mace ce ,
Allah ne yake hada kauna baba a zuciyar dan Adam
Haka ne Allah ya hada mu da masoyanmu,
Amin summa Amin
Bari na tafi wurin ummina dare yayi,
Oh tunda kin gama jin abinda ya kawo ki zaki kara wuta kenan,
Ai na manta ban tambaye ki yaya akai uncle Abdulhakeem ya yarda ya dawo gidan nan da zama,
An dawo dashi garin nan ne a matsayin mataimaki ga babanku umar saboda yadda Allah yake sanya mishi Albarka a harkar shi indai akace shine mai lura da wuri to da ikon Allah sai abin ya kara bunkasa,
Ayyah
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.