17

362 20 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com

اللهم اجرنا من النار 🔥
Allahumma Ajirna minan-nar 🔥

17
   Dukkansu ukun sun fidda matan aure,
Malah kam bai tsallaka ya fita ko ina ba anan cikin gidan ya zaba kanwar matar Alh Bukar maina mai suna hajja kaka ya aura,
  Suna zaman lafiyarsu babu abinda yake kade musi hankali, engr usman yana yola da amaryarshi yayinda Dr Aminu ke zaune cikin maiduguri cikin jerin gidajen da mahaifinshi ya gina,
Musu, gida ne mai zubin gidajen gwamnati na masu kananan hali,STATE LOW COST,
    Zamansu Abin birgewa ne tunda idan Dr ya tafi Asibiti suwaiba takan shiga wurin hajja kaka su sha sharholiyarsu ta yarinta,ya kasance ko Dr yana da night duty a wurin hajja kaka take kwana,
Ita kuwa tsabar yarinta kin zuwa dakin malah take,
Tace mishi yau tana da bakuwa,
     Hajja kaka bata samu ciki ba, wanda ko a jikinta bata damu ba,
   Suwaiba ta haifu danta namiji yace sunan mahaifinta,usman
Tana ce mishi Abba,bata shekara uku ba ta kara haifan namiji suka sa mishi Abubakar inkiyar shi masdooq, sai rikon Abba ya koma hannun hajja kaka kwaco kam,itama suwaiba taci gaba da kulawa da masdooq, cikin Ikon Allah sai lokacin hajja kaka ta samu ciki, suna murna matuka don har ta fadawa suwaibaa,
Ranar wata Asabr da ba'a kawo musu ruwan famfo ba bukar ya turo mai kus kus din ruwa ta dauki jarka wai zata shiga dashi makewaye nan taji wani lema lema a kamfai dinta amma bata damu ba sanda ta cika musu randar makewayen,
  Tofah nan da nan taji jikan na karuwa ji take zut zut a kawai sai tai tsammanin ko fitsari ne yake bin kafarta,
   Maza ta shiga kewaye ta duba sai ga jini nan ta kidima ta hau goge jikin amma abu sai karuwa yake yi bul bul yake ta fituwa sai azababben ciwon mara ya daNno kai,
Ta nemo wani zaninta ta kunzugu dashi,
Dabara ta fado mata ta kira suwaiba ta land line dinsu.
Lafiya kike yaya?
Shigo ki gani,
Nan ta shigo taga jini guda guda a kewaye, nan hankalinta ya tashi tace kin fadawa yaya?
Tace a'a yaya  bai sani ba ya tafi dikwa zancen gidan mannan da yake ginawa,
To bari na kira Dr,
To nan da nan ya garzayo gida ya shiga wurin ya tadda suwaiba na goye da massooq tana  aikin jinin da hajja kaka ta zubar yace kawai su tafi Asibiti yana tsammanin bari ne,
Ai kuwa ta kintsa jikinta sukai teaching hospital inda Dr Aminu yake aiki aka wuce da ita gynea suka tabbatar bari tai aka mata wankin ciki suka dawo gida nan suka sanar dasu haj bintu matar Alh Bukar.
Kan kace kwabo sun iso gida ya dau harami wai sai tayi wanka da ruwan zafi. Suwaiba kuwa tuni ta dora ruwan tare da yi  mata farfesun kaji da yasha kayan qamshi,
Hajja bintu kuma ta dama mata kunun tsamiya,
Saboda sauran jinin da bai fita ba, ya samu ya tsinke, malah kuwa bai dawo gida ba sai bayan magariba ya samu gidan nashi cike da yan uwa,
Nan Dr ya kwanatar  mishi da hankali, sanar dashi hajja kaka tai bari ina dai lafiyarta kalau itan?
Eh tana ciki tune inaga ta samu bacci ma.
Alhamdulillah na gode da dawainiya Allah ya saka da Alheri,
Ba komai yiwa kai ne wannan.
    Bayan ta wartsake ne suka dunguma sai yola domin matar Engr ta haihu itama namiji ta samu  ansa mishi Aminu sunan uban goyonta suka sha bidiri suka dawo,
Ba dade ba hajja kaka ta ta maida gurbi,
Ashe suwaiba ma da nata a makale,
Cikin hajja ya kai wata 9 kar ku ga doki wurin malah duk inda yaji maganin saukaka nakuda sai ya karbo mata,har lokacin yayi ,ta santalo yarta mace mai kama da ubanta suka sa mata Aishatu,
Bata sake haihuwa ba sanda ta shekara biyar a dunia don Aisha nada saurin girma da wayo kasancewar
  tana samun kula sosai  a wurin iyayenta dama yan uwanta su usman da masdooq,
Ta haifi danta namiji shima Abubakar yace wato sunan Alh Bukar maina,
Kunsan bare bari da girmama masu suna hajja kaka ta samu abin arziki iri iri,
     Bukar bai shekara biyu ba aka samu cikin umaru ta haihu cikin koshin lafiya ta cigaba da kula da yaranta
Zuwa lokacin kasuwancin Alh malah ya bunkasa sosai don har sun fara shahara ta fannin kasuwancin man fetur,
   Sun gina maka makan gidaje sun koma ciki  kannensu da suka tashi aure suka gyara musu tsohon gidajen da suka tashi akai kwaskwarima suka  koma dai dai dana zamani,

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now