🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼(Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.comRABBANA HABLANA MIN AZWAJINA WA XURIYYA TUNA QURRATAL A'AYUN WAJA'ALNA LIL MUTTAQINA IMAMAH
بنتم وبنا فمبتلت جوانحنا ## شوكا اليكم ولاجفت ماقينا
18
OMAN ( MUSCAT)
BUKAR ya zama dan gari sai dai yana shan wahala kafin ya sake, kasancewar ba taba zuwa yayi ba uwa uba kuma bai iya yaren da suke yiba,
Sai ya zama yana rakube rakube,
An sashi a school na wasu mutanen india WADI ALKHABIR SECONDARY SCHOOL.
inaga shi kadai ne baki a cikinsu baya um baya um um,
Daga baya ya fara picking shikenan sai ya zama idan suna magana yana ji amma mayarwan ne yake mishi wahala,
Bai dai yi shekaru biyu ba ya zama yana jin komai,
suka mai da hankalinsu akan karatun sanda yayi Jsce kafin yakai ziyara nigeria,
Bayan dawowar shi kuwa sanda ya shiga jamia kafin ya kara ziyar tan nigeria,
akwai tsaranshi a gidan wanda kusan kansu daya ne sai dai bukar ya dan fishi a shekare sun fantsama jamiar SULTAN QABOOS suKA FARA karatun cikin nasara,
Duk da haka umair bai barsu kara zube ba yana gwada musu hanyar kasuwanci musamman idan akai hutu,
Bukar da suwailim sun fara nisa cikin kasuwanci sai ya zama Bukar idan akai hutu ko nigeria bai faye zuwa ba,Gashi yayi dace Ahalin gidan gaba daya suna son shi, koda yake shima hakan ya faru ne sakamakon kyawawan halayyarshi bai da raini, babu tashin hankali,tunda yaje gidan bai taba fada da wani ba dai dai da masu gadin gidan yana girmamasu,
Shakuwa mai karfi ya shiga tsakanin su,
Musamman umm kulsoom wacce ta kasance yar autar gidan ya shaku da ita sosai,
Haka kawai idan bashi da abinyi yafi kaunar ya kasance da ita, tai ta mishi shirme da shagwaba
Sun kammala jamia da sakamako mafi kyau har jamiar ta bawa Bukar Appointment As GRADUATE ASSISTANCE,
Amma yaki fir yace kasar su zai koma, fir umair ya hanashi komawa,
Shi kuwa Alh Malah so yayi danshi ya dawo yayi aure a cikin dangi amma sai ya kau da kanshi akan Bukar,
Wani abin mamakin kuma Bukar bai taba yin budurwa ba,
Don shi ana shi tunanin so yake ya jira ummkulsuum,,Kuma bai taba fadawa kowa abinda yake ranshi ba,
Hatta suwailim da suke tare bai sani ba,
Sai dai mahaifiyar su suwailim ta gane hakan,
Dayake dai umm kulsuum din yarinya ce shiyasa tabar abin ,Alh malah yasa ido
yana jira yaga gudun ruwan su,Ana haka umar ya samu mata course mate dinshi ce tare sukai UNIMAID ya girme mata amma ,yana 300level ita tana rems yana 500 level ta shiga 200 level, sanadin Assighment suka hadu,
mai suna saudat, yar wani hamshakin maikudi ne, ubanta yayi commisioner na power supply & technology,
Manya suka je suka hada gemu da gemu akai zancen neman aure, da adadin sadakin da suke so kasancewar yar babban gida ce,
Amma ko a jikinsu, tunda dama ita dukiya ana nemanta don rufin Asiri ne,
Sunyi duk abinda ya dace amma gidan maza sun nemi a dan tsagaita saboda Bukar ,
Suna so su sa su a lalle rana daya,
Sun yarda sun aminci da hakan, hakan ma ya musu dai dai domin saura kwanaki kadan a tura su Bautar kasa,
Zaifi kyau ace kafin auren ta kammala komai,
Iya kaci idan ta shiga sai zama idan mijinta ya yarda zatayi aiki to, idan bai bari ba to shikenan duk daya,
Nan hajja kaka ta fara damun maigidanta akan ya kamata Bukar ya dawo yayi aure shima,
Dan halak kunsan duk inda dan halak yake ana fara maganar shi zai ji Alama,
Kamar wasa sai gashi ya diro nigeria da maraicen ranar Alhamis,
Murna ba kama hannun yaro a wurin iyayenshi musamman hajja kaka
Akai ta nan nan da shi duk abinda yake so sanda hajja kaka ta tanada mishi, yayi sallar magariba da isha'i sannan yazo ya zauna yaci ya koshi ya bata tsaraban ta dana mutanen gidan,
Nan ta suko mishi zancen zuwa neman auren umar, nan gaban shi ya fadi don ya lurah hajja kaka tana son taji daga bakin shi, bai san mai zaice ba, yayi shiru yana nazari,
Kulsuum dinshi dai tayi yarinta....
Ana haka Alh malah ya shigo yace ya same shi a falo nan gaban shi ya kara faduwa to,
Shi kuma minene, amma dai yasan LABARIN GIXO BAI WUCE KOKI,
YA isa ya dukad da kanshi a kasa sukai sabuwar gaisuwa tare da tambayan iyayenshi na can yace duk suna lafiya,
To nasan mahaifiyarka ta fara maka magana ko,
Eh,
Hakane to mi ake ciki?
To A halin yanzu dai babu akasa tunda kasan ba anan nake ba, amma idan akwai wacce kake gani ta dace sai a mata magana,
Alh Malah ya numfasa yace naji Allah ya maka Albarka, zan tattauna da iyayenka mata musan abinyi,
Shigar shi daki ke da wuya yace umar yana waya da saudaT tana ce mishi anyi posting dinta GOMBE
yace ina bazai yuwuba ,dole za'a canza kinsan mazan gombe kuwa da son mata ina! Bazai yuwu wani yaje ya sace min keba,
Yanzu gobe zanzo na karbi call up lettern ki zan shiga NYSC SECRETERIAT A canza ko kuma muje kotu ayi miki MARRIED CERTIFICATE,
ba damuwa Allah ya kaimu, owk zan kira ki anjima ga yayana Bukar ya shigo ,ka gaida shi,
Zai ji
Umar ya akai kasan yan GOMBE suna da neman matan?
Yaya na zauna dasu ne a school idan kaga yan off camp yadda suke abin ba dadi,
to kwantar da hankalinka,
badai an yi maganar aure ba inaga bazata bari wani ya shiga gonar da ba tasa ba,Haka ne.
Amma dai ta dawo nan din yafi.
Ni gashi ma ka ballo min ruwa hajja kaka ta daqa hankalinta na samu mata wai za'a hadamu rana daya,
Mtwsssss.
To kai Yaya baka da tsayayya har yanzu?Umar bazaka gane ba, yaushe nake zuwa nigeriar ma balle har naci zan ajiye budurwa,
Nikam na bar musu zabi,
Kai yaya!
Kafin son a zaba maka mata kenan,
To yaya zanyi umar?
Haka ne,
~~~~~~~~~~~~~~
Washe gari Alh Malah ya sanar da matanshi,abinda ake ciki gameda Bukar, hajja kaka tace ai auren zabin ne wani sain akwai matsala, to amma kai yaya ka gani?
Shatu tai tsagal tace dama akwai wata kawar kyallu da ta dadi tana kaunar shi tun wani zuwa hutu da yayi ta ganshi anan ta fadawa kyallu,
An takura mata ta fidda miji amma taki don ita tace idan ba Bukar yayan kyallu ba bata ga mijin aure ba,
Ikon Allah inji Alh Malah.
Yanzu kira kyallun ki tuntube ta muji,Ita dai hajja kaka bata so hakan ba amma don kar ace tace wani abu tai shiru, indai kawar kyallun da ta sani ce ai bata da halin da za'a so ta saboda tsabagen ji da kai da fadin rai, ta kanzo gidan amma gaisuwar kirki bata hada mu, amma daga baya nan idan tazo bata samen a tsakar gida ba takan shigo da niyyar tazo gaishe ni ta zubawa hoton Bukar ido wanda ya dauka ranar matriculation din shi,ohoo dalili kenan,
Ba jimawa shatu da kyallau suka shigo,
Alh malah yake tambayarta ina labarin kawarta mai son Bukar tace tana nan.
Ina dai ba'ai mata miji ba ?
Ko kadan amma inaga ya kamata naje wurinta naji mi ake ciki,
Eh yakamata.
Shatu sai murna take. Yi, dama zancen auren UMAR ya tsaya mata a rai tana ganin hajja kaka zata samu nutsatstsiyar surka, kunsan KISHIYA duk zaman lafiyan da ake yi bata son taga KISHIYA ta fita,
Ya sallame su yasa driver din shi yakai kyallu gidansu kawarta
~~~~~~~~~~~~~~
Isarta ke da wuya ta sameta a daki kananan idon nan suyi jazir sun kara shigewa ciki,
Daga gani kasan ta sha kuka,
Kyallu na banko kofar tace ke lafiya kin takura kanki kina kuka?
Ba dole ba,
Wai sun damen na fidda miji ni na gaya musu ba yanzu zanyi aure ba,
Babanmu bai yarda ba, wai bazai asaran kudin makaranta ba,saboda wai yaga grade two dina bai yi kyau ba,
Da wace kwakwalwar zanyi karatu?
Sha kuruminki, Albishir!!!
Miye ???
Bani goron Albishir,
Ki fada min miye?
Kinsan mi ya kawo ni gidanku?
Tace zumunci,
Sam ina!
Koda yake zumuncinn ne,
Amma daina kuka bukatar ki zata biya
Baba ne yace nazo naji ko an miki miji,
Mutuminki ya dawo ana son yayi aure yace bai da budurwa a zaba mishi ,
Don Allah!
Da gaske!
Suka rungumi juna,
Na taba miki wasa makamancin haka?
A'a
Kodai kina son kwantar min da hankali ne,
Tasa ihuuu da har sanda mahaifiyarta ta fito a guje,
Lafiya kuke,
Umma lafiya Alhamdulillah.
Bukar din da nake baki labari ya dawo,
Sai akai yaya kenan?
Nan kyallu ta kwashe ta mayar mata yadda akai da shatu,
Da daga hannu tai murna tayi gud'a
Ayuururiiiiiiiii,
Ina mahassada? yar nan nasan sai kin debo farin jini na, badai ansa miki ido aga wanda zaki aura ba?
Yanzu ne lokacin mai da martani,
Goge hawayenki,
Kyallu kice ko yanzu su zo an basu.
Ki gaida mahaifiyarki zan zo da kaina godia.
Ba komai driver yana jira na a waje zan je na fadi sakon,
Maza tashi ki je
( wohoho kunga uwa kenan Allah yasa mu dace)
Zancen yama shatu dadi, kanta tsaye taje tasamu Alh ta sanar dashi,
Ko takan hajja kaka bata bi ba,
Shi anashi tunanin yana ganin gwaninta take yi,
Bai san da wata manufa ba a zuciyarta,
To kiran hajja kakan, tazo tare da Bukar din,
Suka same shi a kishingide yayi kwanciyar magirbi, sukai sallama.
Shatu kuwa sai farin ciki da washe baki take yi,
Alhaji yayi gyaran murya ya soma fadin to Abu ma yazo gidan sauki hajja, yarinya dai an binciko bata da manemi saboda haka,Bukar yace na'am
Ka ne mi kyallu zata kaika wurin matan
To nagode.
Yace nine da godia da ka bani matsayina na uba,
Allah ya maka Albarka
Yasa ka gama da dunia lafia.
Amin Baba
Yasa kai ya fita.
Ya juya wurin shatu yana tambayarta yar wace unguwace , tace suna london ciki ne,
Amma asalinsu yan KUKAWA ne,kai to ma ashe duk daya ne,
Ina dikwa ina kukawa?
Haka ne Alh
Hajja kaka dai tana ganin ikon Allah,
Karshe tai Addu'ar zabin Allah,
Domin yanzu tasan idan tai magana Alh, bazai gane ba,
Bukar kuwa ko a jiginshi,
Suka je ya ganta,ya kaddamar da kanshi gareta sai wani yauki take yi, shi kuwa da yake ba sanin hidimar mata yayi ba ko a jikinshi,
Yasan dai bata da kyau ga kananan ido daya karewa kafarta kallo kuwa yasan tana samun jin dadi zata narka qiba,
Tofah.
Gemu da gemu sun hadu an yake shawarar biki nan da wata tara bayan saudat ta gama bautar kasa.
Ya fara shirye shiryen komawa oman, cigaba da kasuwancin shi,
Yabar mutanen gida da fara shirye shiryen biki,
Shatu itace kan gaba ta kane kane komai a wajen malah shi kuma dadi yake ji,
Saboda yana ganin kansu a hade yake da hajja kaka,
Hajja kaka tana kawaici,
Ita ko hajja ko a jikin ta🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.