🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'ar Bude Sallah (watau Bayan An yi Kabbarar Harama)اَللَّهُـمَّ باعِـدْ بَيـنِي وَبَيْنَ خَطـايايَ كَما باعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبْ ، اَللَّهُـمَّ نَقِّنِـي مِنْ خَطايايَ كَمـا يُـنَقَّى الثَّـوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسْ ، اَللَّهُـمَّ اغْسِلْنِـي مِنْ خَطَايَـايَ بِالثَّلـجِ وَالمـاءِ وَالْبَرَدْ .
Allahumma ba'id baynee wabayna khatayaya kama ba'adta baynal-mashriki walmaghrib, allahumma nakkinee min khatayaya kama yunakkath-thawbul-abyadu minad-danas, allahummagh-silnee min khatayaya biththalji walma'i walbarad
بسم الله الرحمن الرحيم
Ina son ku har raina
Mutanen garin katagum Azare
24
RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA
duk da yadda auren yazo amma bai hana tumbatsar jama'a ba,
dubban mutane ne suka shaida daurin Auren Asma'u muhammed malah sharif
Da
Angonta,
Abdulhakeem sulaiman jada,
Sai fatan Allah ya kama auren,
Kyallu kuwa ko gezau batai yiba saboda tana tunanin irin rashin mutunci da zata mishi don anata Alwashin bazata kai wata 1 bama zai gaji ya sakota,
Shatu tace haba 'yata kuyi wata 2 mana
Tab nifa wata dayan ma da kyar ya kai,
Aka fara shirye shiryen tafiya da Amarya yola,
Yaa kime kuwa sun hade kai da dangin shatu suna tanadin yiwa saudat rashin arziki idan sun tafi yola, ta shirya kenan sai take tajin kamar tashin zuciya haba sai amai nan aka fadawa hajja abinda ke faruwa da sauda suka shiga itada Aisha yaakurah don fanna kam ko sashen hajja bata lekawaa
Yaa kurah tace mi yake samunki,tace wallahi tashin zuciya take ji,
Tun yaushe kenan inji Aishatu,
Kwana kusan 3 ayya sannu inji hajja maida jakar ki ciki ki taho mu taho sashi na,
Suka tallafota saboda jiri take ji suna fituwa sai ga shatu tace yaya dai miye hakan
Yaa kurah ta rangada guuda tace
Abim arxiki ya samu
Tai sakarai tana jiran karin bayani,
Sauda zamu kai Asibiti bata ji dadi ba amai take ta kelawa tun dazu,
A dari da sittin yaa kime ta fito amai kuma mi kika ci
Ko kinsha mangoro ne?
Yaa kurah tace a'a ba abinda kike tsammani bani juna ta samu sai ki tayata fatan Allah ya raba su lafiya,
Amin cewar Aishatu syka karasa daki aka kira umar suna can suna fama da jama'a ,
Ya shigo yaga sauda a kwance aka mishi bayani
Yaa kurah tace ka kwantar da hankalinka, abin farin ciki ne,
Ayya baba An taba farin ciki da ciwo,
Tace to karuwa aka samu, ai ina nufin lififi ne yake wahal da ita,
Miye lififi?
Hajja tace kai sai ta maka dalla dalla ne,
Yaa kurah dake bata gajiya da bayani tace to ciki ne da ita ta fara laulayi sunkwi da kanshi yayi,
Yana jin kunyar maganar a gaban hajja,
Aisha dauko kyale mu tafi Asibiti,
Suka fito nan shatu take cewa Aisha kina nufin bazaki kai yar uwar taki dakinta ba.
Eh zamu kaita muna dawowa ta kara gaba abinta saboda itama ba son shiga zuriar su shatu take so ba,
Tunda suka zo zai filatanci da uwar bakar harara suke watsawa mutane,
Balle kuma sunje muhallinsu,
Ba dama ta zille ne saiga dalili ya taso,
Da yake mai aikin hajja ta taba zaman aure a gombe tana jin duk tijarar da suke yi,
Sunje asibiti yadda suka ga jikinta yayi laushi suka fara saka mata ruwa,
Umar ya koma dauko kayan zama a gida nan hajja tace mishi yaa kurah ta dawo sune babanai masu kaiwa Amarya dakinta,
To zan kawota yanzu insha Allah
Tare da bukar suka koma,Asibiti,
Sun samu an kawo takardun magungunan da za'a sayo bukar ya karba ya sayo shi kuna umar ya juya da yaa kurah aka dau hanya sai yolah, birnin BARKINDO LAMIDO,
BA laifi sun tana da mishi muhalli mai kyau fanna yaa kurah yaa kime sunyi nadamar zuwa domin saukar su keda wuya aka share su ruwan sha babu balle abinci suka zo suka jaa kyallu wani daki wai za'a fara tsimata kafin kaita gidanta ayi mata jire,
su fanna kuwa jira suke shiru sai akai shawaran tura yaa kime ta musu magana zasu je gidan Amarya su fara kintsawa,
Tace kai a su wa ,kana dan hajja kaka kace zaka je gidan mau aiki babu danginta karya ne wallahi,
Yaa kime tai sakarai don ta gane abinds take fadi duk da cewar hausar da kyar yake fusgota,
Ta lallaba ta koma ta fadawa su fanna,
Fanna tace bari naje tunda sun san ke matar bukar ne,
Ai ni babanin ta ce kanwar ubanta
Yaa kurah tace na kusan damar shatu ba,
Hmmmmm ita dai yaa kime yadda taga abinda suka mata tace to Allah yasa adace
Fanna ta shiga tana wani marairaita ina yar tawa?
yarki? yanzu tabar hanunki ta dawo kasan ikon mu dangin uwarta mi za'ayi da dangin uba ina duk bakin ku daya zaku bayarta a maigadi to ga mai sonta nan,
Aka sille fanna sikal da soso da sabulu tace zanyi sallah ina buta,
Ta koma tana Allah wadarai da marassa mutunci,
Taja bakinta ta kunshi saboda kar ayi mata dariya yaa kurah kuwa ta fahimci hakan
To akwai cigaba ne,
Nan ta fara dibi dibi,
Can yaa kurah tace akwai wata kanwar maigidana marigayi da muka taba kawo ta nan inaga zan gani ku tashi mu tafi,
Yaa kime ce ta fara suran jaka
Fanna ta biyo bayanta ranta a bace gashi ba zamanin waya bane balle ta kira dan uwanta suka fito ransu idan miliyan ne ya baci nan DANIJO ta ga fitowarsu da yake nata rashin mutuncin bai yi nisah ba kuma tana ganin ai surkayen danta ne, ina zaku ?
Fanna a hasale tace inda za'a mutunta mu?
Ban gane ba ?
Tsabar rashin mutunci tunda muka zo ruwan sha kun gagara bamu ba dole muje inda za:a bamu ba
Ashe Alhajijo yana bayan uwar domin ta kira shi tana mishi nasiha, da ya rike yar uwar shi
Karyar banza karyar wofi waye zaku ce basu baku ruwan ba,
Iyayen nawa danejo ta juya tace bace min daga nan surkan naka kake cewa karya,
Nan yaa kurah tace eyyeh surki lalle anyi dace kenan ashe iri daya kuke,
Suka sa kai suka fice danijo ta yo cikin gida ta samu anata maganar ta tambayesu suka fada mata abinda suka musu ,,
Da gangan muka musu ceku kawai
Danijo tace da ba'ai hakan ba ai wurin mu suka zo,
To sallamammiya anyin,
inji inna kenan
Yaa kura tace Allah ya hutar da Aisha da sauda
Fanna kunga irin sirikin naku ko?
Hmmmmm
Yaa kime tai tsagal tace ai wurin suka xo indao kyallu ce inaga tafi su rashin mutunci fanna tace ai yamin dai dai sun gamu da sun dace shegiya ni ai da maigadin aka bata ma hala sa girmama mu,
Yaa kura mi take yi banda dariya wanda ya kawosu suka dauka,
Motar kaya kuwa suka barta a wurin yaa kura tace baza'ayi haka ba ta musu magana tace ku shiga anjima zasu kai ku wurin da zaku ajiye kayan ta dauko kudin tafiya da Alhaji ya bata ta basu suka ce yau zasu juya ma saboda sun lura babu mutumci a harkan.
Sun samu tarban mutumci da mutuntawa aka kaisu daki nan da nan aka kawo abinci a hakan ma tace bari masu aiki su daura musu,
Sukai ta mayar da zance
Yaa kurah tana ta mamakin yaa kime da fanna yadda suke cin fiskar shatu da kyallu wato haka duniya take baza'a fada maka gaskiya ba kuma komai tarayyarka da mutum bai wuce ka aiban ta shi a bayan idon sh ba dunia kenan INA ZAKI DAMU
kowa ya zama ZULWAJHAIN, ma'a bota fuska biyu,Allah ya kyauta,
Washe gari kuwa sukai maiduguri ko komawa gidan basuyi ba balle su san muhallin da za'a ajiye yarsu,
Hamdulillah tafiya tai kyau suka sauka a mota, sun iske gida an watse sai sauran mutane kalilan,
LALE WO USHE ,
USHE KANDARO,
Ai Allah Allah fanna take tayi arba da shatu ta zazzage mata rashin mutuncin da danginta sukai musu,
Sai sukai karo da Alhaji yana sallaman mutanen dikwa nan yaa kurah tace su jira suyi mishi bayanin komai,
Suka kaisa da Alhaji yaa kime ta shige ciki wurin shatu ta shiga ta gansu kwatsam yaya na ganku yanzu,
Eh ina sauran suna wurin babah,
Alhaji malah ya jinjina sosai yace to yarsu ce koma minene amma ke fanna harda ke suka miki haka duk yadda kuke ,
Ni waye yaya ai zan samu shatu yanzu,
A'a akan mi, keda mutanenki,ta rasa bakin magana Allah yasa adace amma ban son hayaniya kin sani ki kyaleta ai wulakanci kam wa kansu suka yi bana ma wa kyallu fata amma haka ta zaba,
Yaya abinda ya bani mamaki fah angon ko gaisuwa babu wai mune makaryata,
Hakuri zakuyi
Yaa kurah tace bai san itace a madadin uwaba,
Sukai murmushi,
Ba kunya ba tsoron Allah fanna ta shiga dakin hajja kunsan haka masu fuska biyu suke, da zaran an samu sabani baza su iya daurewa su danne ba a'a sai sun canza sheka musamman akwai mata sama da biyu a gida
Hajja tasha mamakin ganin su tace har kun dawo,
Nan fanna ta fara cewa Aisha kinyi sa'a munga gata'i mukam,Yadda ta burge ni tace Allah ya rufah Asiri sannun ku da hanya nan ta kawo musu ruwa da Abinci,
Yaa kura kuwa ta shiga ciki wurin sauda ta kama hannunta sannu saudatu yaya jikin yaya kika kara ji,
Da sauki sannunku da dawowa tana tunanin sauka akan gadon dakin da take kusa da na hajja tace kwanta don Allah ta sauko ta gaidata tace da sauki tunda nasha ruwa ai,
Allah ya raba lafiya
Ta kau da kanta tai shiru,
Ta koma falo ta samu fanna na cin abinci tace baki karisa dakin naku baNe,
Shatu taji shiru ba fanna tace kince min tare kuke?
Eh dazu da zanje dauko plate nagansu sun shiga dakin hajja ne,
Eyyeh
Ta zaburah
Tasan akwai wani abu a kasa
Anyi wani abun ne?Ba komai mama
Tace fada min gaskiya akwai wani abun da ma dai su baba fanna din sun gagara hakuri ne,
Nan ta shirya mata magana kamar ba da ita akai wa rashin mutunci ba, ba komai ai,
Ya wuce mama,
Dalla dalla zaki min,
Ta shirya karya ta fadawa shatu wai yaa kura ce dasu fanna suka ce saukar da aka musu bai musu ba suka samu muka tafi wani gida ,
Ina zuwa
Ta shiga dakin hajja,
Tunda aka sallamo sauda bata shiga ta mata sannu ba amma yanzu ta shiga zatai rashin da'a
Babu abinda ya kona mata rai sai ganin abinci da tai a gaban fanna to ashe kema hassada kike min
To idan baku shirya mata daki ba sai mi,
Don ma cikin dangi kuka kaita balle raina ya bace
Yaa kurah ta fito daga bandaki,
Kwarai cikin gata muka kaita ,amma banga alamar gatan ba tunda ai gata bai wuce dangin ubanta ba amma aka walakanta mu tsiyar kananan mutane kenan fanna tai caraf tace rashi bai yiba. wallahi hajja ta shigo daga fannin Alhaji kenan tace yaa kura miye hakan?Nan ta tsaida su,
Aisha tace tsakanin ku,
sauda tace hmmmmmn
Allah ya kyautaComment
Vote
Share
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.