15

388 22 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕🏼Gaskiya daya ce🖕🏼
( daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Umm imaN

ADDU'A NEMAN TSARI DAGA MUMMUNAN MAKOCI.

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

اللهم انى اعوذ بك من جار السوء فى دار المقامة فان جار البادية يتحوال
Allahumma inni A'uzu bika min jaris - su'ie fi daril makama fa innaj-jaril badiya yatahawwalu,

Naki ne wannan shafin yar uwa rabin jiki Kina sha'aninki 🧕🏼
Najida Aliyu Biecha
Allah ya barki da ya salees🥰

15
No wonder tasan cewa LEATHER OUD da yake hadawa da MUKHALAT SHAMS na kamfanin AJMAL a wurin shi ta taba jin kamshin domin maman su husna kasuwancin da take yi kenan, kuma tana order su kuma duk order da zatayi sai ta dauka musu, ita shafa ta dauki MUKHALAT SHAMS ita kuma husna ta dauki LEATHER OUD,
Zasu fita Shopping rannan sai shafa ta fesa nata sannan ta fesa na husna nan da nan sai taji qamshin gayen nan don bata san sunana shi ba, shiyasa ta fahimci lalle mix dinshi ne shi kadai da yake yi amfani dashi.

Shiyasa duk inda ya dosa kafin ya shiga wuri akan fahimci BADARALDEEN ne ya faso
Koba komai hankalinta yasamu nutsuwa saboda yana da irin qualities din da take so daga namiji, tana son namiji ya kasance
zabgegen kato,
don ita anata tsarin bata kaunar karamin namiji kasancewar duk wani kankanin namiji yana tare da fadin rai kunci da nuna shi wani, kai ita tana ganin abin burgewa ne a ganta yar das yar firit a gaban garjejen kato,
Kar kuce saboda wani dalili ne a'a ita dai a yadda ta lura idan ka ga gabjejiyar mace to zaka ga mijin dan firit kamar ta goya shi,
Idan kuma kaga mace yar firit to kasani zaka samu mijin jibge ge ne.
Ina yini kazo lafiya?
Lafiya klau,
Alhamdulillah yau dai ga muhammad a gabanki
Da fatan zakiyi hakurin rashin bayyana miki kaina da wuri ba, shi kinsan aure lokaci ne, hausawa suka ce kamar habo yake zuwa,
Tun haduwar mu ta farko nasa wa zuciyata bani da matar da ta wuce ke,
Sai gashi Allah ya nufa zamu zauna karkashin inuwa daya a matsayin mata da miji,
Ni gaskiya ban iya cewa ina sonki,
In ban aure kiba zan kashe kaina,
Ina!!!
Karya ne wannan
Ina da saurin hawa abin nufi bani da hakuri sai kin shirya don ban iya ganin anyi ba dai dai nayi shiru ba,
sai kin kiyaye bana son raini ko kadan,

Allah yasa mu dace,
Nan suka hau tattauna yadda abin zai kasance tace itama ba mai son tarkacen biki bane, amma tana ga zatai fulani eve sai kuma abinda sauran yan uwanta suka tattauna zasuyi.

Yaushe kike ganin zakuyi hutu.
Nan ba da dewa ba
Amma kasan next term zamu tai Acculturation gamburun ngala nan zamuyi karatun semester gaba daya
To kuma dole sai anje ne?
Eh,n
To amma da yake karatu ne ba yadda aka iya sai ki karisa da yake ma bamu da nisa. Da gamborun ngalan kin taba jin dajin sambisa ta zabura ta dago idanu!!
Kwantar da hankalinki ba sambisan muke ba muna dai kusa da nan ina ma ta tunanin ko zaki yadda ki amince da zaman kauyen kin saba zama a Abuja, dasu oman,
Tace haba nima ai tushena kauyen ne, tunda yayye nane suke birnin ba niba,
Miye a cikin kauyen?

Haka ne,

Amma ina da wani dan uwan mamata da yake birni cikin maiduguri sunan shima naci, shi ya biya min kudin makaranta ma nayi karatu,

Kinga yanzu bazan daura mishi nauyi nace dole sai ya bani gida a birni na zauna ba

Lokacin da muka hadu a oman din nan ma shi ya aike ni,
Da yake Ambassador Abokin shine suna wani harkan kasauwanci shiyasa yake aika na akai akai har nasan gari,
Kuma bai da yaya maza sai mata shi kuma ra'ayinshi na mutan da ne bai yadda da wayewar yaya mata ba.
Eh hakan yana da kyau ai.

Amma kauyen naku akwai kogi ko gulbi?
Miye kuma GULBI?
Bakasan gulbi ba?
Za ka sanshi wata ran a hankali,
Na dai samu na lallaba nayi gini acan kauye.
Allah yasa bazan takura miki ba
Nifa kar ka damu ai kauye na tashi

sai ki zauna acan
Ina labarin Aunty kyauta ne mata mai mutunci,
Tana can oman,
Garin da nake so kenan shafa ina son oman kina taya ni Addua Allah yasa inada rabu a kasar,

Allah ya ida nufi, yace
Amin
Hmmmm Talaka da
sa buri ko? koda yake fata nagari lamiri ne idan yaso in kinyi hutu sai kina tahowa kauyen,.
Amma sai kinyi hakuri muna da yawa
Tayi lakwas tana jin shi.
Sosai zaman karkara matan yayyu duk ana gauraye,
Haka ne Allah yasa mu dace
A zuciyar shi yana ta istigfarin karyan da yake sherawa,
Saboda shi koda wasa baya son ya auri macen da tasan yana da wani abu,
Matan zamani abin tsoro ne kudin kawai suke so,
Shiyasa yake ta shirya mata BASAJA.

Tace bari na baka waje ka sha ruwa, no kar ki damu ta mike ya xuba mata ido har ta bar falon gaskiya da kallon tsoro yake mata anya bazai ballata ba kuwa?
Anya bai fi karfinta ba,
Ta bashi wuri taheer ya fito ya zuzzuba mishi abinda zai taba
Yayi sallah ya dawo,
Ta shiga yana ta mata hira sai eh ko uhm yace kiyi hakuri
Ban taho maki da komai ba kinsan talaka zancen aure ya gabato zaka lallaba abinda yake hannunka ne don a fita kunya,

Kar ka damu Allah ya buda ya baka ikon fita kunyar mutane
Yace Amin.
To ni zan wuce inaga insha Allahu zanyi kokari muje gaisuwa can gida Zamfara na gansu su ganni,
Eh ya kamata ai kuwa,
Ba komai
Ammafa zaki ga neman auren kamar na 'ya'yan manya,shi wannan kawun nawa ne yake komai, na mishi magana akan ayi dai dai karfina yace bai son abin kashi, ni kuma gani nake da yayi komai dai dai karfina zai fi min, bana son aga kamar ni wani ne sai anyi aure na fara wuri wuri,
Uhhhhhhmmnnmm
Tace,
In ta nine kar ka damu Allah ya buda maka, ai shi arxiki nufi ne na Allah, kuma ba lokaci daya ake yinshi ba
Haka ne,
Nagode da kika fahimce ni.
Muje ki rakani na hau Acaba na je tasha in yaso na kwana a kano,

kinsan garin mu akwai nisa da nan,
Ayya Allah ya kaika lahiya na gode,

GORIBA ROAD

yana isa ya samu Aisah na jiran shi taji yadda ya kasance,
Yace ukhti yaushe kika koyi tsegumi,
Ya bata labari yadda sukai,
Tace wayyo baiwar Allah,
Kuma ta yadda ko.
Eh mana
Ta tsallake kenan...........
Kinsan da na lura mai son abin dunia ce zan rabu da ita.
Hmmmmm
Na fada maka bata da matsala,
Allah yasa

BORNO

BINAZIR ta fara shirye shirye ba kama hannun yaro wani abun ma da gayya take musamman idan taga yaana
Yau ma haka ya kasance tana ganin yaanah ta hau waya da yaya haisam, wai ya turo musu kudin ankon kawaye dana kanne domin yace shine zai yi, tace ka ga harda Aunty yaanah ma yanaah tace kan uba Kawancen uwarki zanyi bana Aisah ba,
Ai kuwa binazir tace ke uwata ba tsaranki bane...........

Sai ganin hajja kaltume tayi tazo taja hannun binazir, Binazir tana kyali ni ammi,
Yaanah tai kwafa zaki gane shayi ruwa ne, wallahi tai kwafa ta wuce ciki.........

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now