26

381 24 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
          [ JIRE TILO]

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'ar wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci.

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon.
بسم الله الرحمن الرحيم
26
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa tsakanin Alhajijo da  kyallu bai fasa ayyana mata rashin mutunci ba ita ma tana nan daram akan bakanta,
Xama yaki dadi
Ko girki batayi
Zumunci ya fara lalacewa saboda ita danejo tana ganin danta a cikin garari ko abinci sai dai ya saya ko.yaje gida yaci,
Inna kuwa bata ganin laifin kyallu saboda ubanta wani ne,
Kunsan a zamanin nan akace kai wani ne to ga gaskiya baro baro  vaza'a iya fadanta Ba  saboda dan abinda za'ace gashi ko hungo

     BORNO
   Yaa kime idan hankalinta dubu  ne to ya tashi saboda  tunda akace sauda nada ciki sai hankalinta ya tashi,
Tana matar yaya ace bata samu ciki ba wanda anata haukan tunda so take jikanta ya zama shine jikan farko a gidan,
Nan ta fara daga mishi hankali wai su tafi asibiti a duba su.
Haka kuwa akai akace lafiyarta kalau shima haka lokaci ne bai yiba, nan aka basu magani suna sha amma da sharadin saduwa dole,har su kammala shan maganin,
   Shine fah ta dawo ta fara shaye shayen magunan mata dana gargajiya dana turawa .

Sauda kuwa tsabar laulayi sashen hajja ta dawo da zama kuma ba laifi hajja tana iya  kokarinta
Ta saba idan umar zai fita sai ta mishi rakiya saboda ba laifi jikin da sauki ba kamar da ba,
Ashe suna hankalce da hakan shatu ta sa masu aikinta su nemo mata karkashi su kirba su dauraye ruwan zata yi amfani da shi,
Ba bata lokaci washe gari suka kawo mata,
Ta nunawa yaa kime tace mu fara gwada wannan idan bai yiwu ba sai mu canza dabara,
  Ita dai bata san mi za'ayi dashi ba tace, Ajiye min zan nuna miki abinda zakiyi dashi gobe da safe,
   Umar ya fito kenan daga dakin hajja sauda na binshi a baya yana cewa ai yanzu kam kinji sauke kya dawo dakinki,
  Ta murmusa tace ka fadawa hajja to,
Tace bani da ta ido ko?
Ah to nima bazan iyaba,
     Shikenan duk lokacin da ta sallameki sai ki dawo ina maraba,
Ga yaya Bukar a mota yana jira na
Ki koma kibi a hankali kinga ko jiya da kika ga likita yace banda hanzari da son samu ne da ya baki bed rest tunda cikin yana wahal dake,
Ba komai zan kiyaye,
Allah ya tsare ya bada sa'a,
Ta juya kenan ta bude kofar da zata shiga tsakar gidan sai taji ta a kasa sharab kuma ta buga cikinta a sama kan kace miye taji mararta ta kulle shatu ta fito ta same ta a kwance,
Ah lafiya sauda a kasa  ,hakan yayi dai dai da fituwar hajja kaka kafin ta karaso maza maza shatu ta daga saudat  ta sakale mata kafada Ata kaita daki tana mita,.ai dama iyayi  ne keda ba lafiya ba na miye sai kin rako miji,
Ko dama yan bokon nan ba kunya ke gare ku ba , idan banda haka an baki hutu kar kina takura kanki amma kullum saboda iyaye ke ga mai miji sai kin mishi fi'ili,
Can sauda tace yaa salam sai ga jini yana bin kafarta,
Shatu kuwa sauri sauri take yi taje ta gyara wurin kar aga ruwan yauki,
Hajja kaka ganin jinin ya sata kidimewa ta dau waya ta kira su umar a wurin aiki nan da nan suka garzayo suka dawo gida ya shiga yana canza mata kayan sawa kai sai yaji yauki a jikin zaninta,
Suka fito Bukar ya kira yaa kime yace ta shirya su tafi tare suka kama hanya
Sun zo dai dai inda sauda ta fadi yaa kime ma ta zame ta sa kara nan da nan su hajja da shatu suka fito lafiya kan kace kwabo hannu ya suntume abinka da mi raki, sai kama hannun take yi tana ciwa ta shiga uku ta karye nan dai shatu ta dauko mayafi suka tafi,
An shigar da sauda dakin masu haihuwa ita kuma yaa kime aka wuce da ita ganin likita hannu kam sai kara tashi yake yi ashe karaya aka samu shatu tace baza ayi daurin asibiti ba zasu tafi ayi na gida
Haka dai suka fita ko bin takan sauda busu yiba,
Likitan matan yayi ta fada wa umar yana cewa jiya jiya nace muku ta kiyaye abinda  zatayi ta jijjiga jikinta saboda dama cikin bai zauna yadda ake soba gashi nan ya zube,
Umar dai ba ta cikin yake ba ta sauda yake yi amma itan ina da lafiyarta?
Eh za'a mata wankin ciki ne,
    Ana bukatar wani kayan da zata canza sai ruwan zafi da abinci domin tana farkawa zata farka ne da yunwa,
Yace bari naje
   Ya samu hajja tana tambayar masu aiki yaya taga kamar an zubda ruwan karkashi hanya?
Suka ce basu da masaniya,
   Sunga dai daso mai aikin shatu da karkashi jiya amma basu san mi tayi dashi ba
Ta sallame su,
Suna tashi sai ga umar yake cewa bari tayi za'ayi wankin ciki ta tambaye shi yaa kime fah tace eh karaya ta samu a hannun,
Yake cewa abin mamaki hajja a wuri daya fa suka fadi,
Kuma naga kamar danshi a jikin zanin sauda dana taba sai  naji yauki,
Hajja nan ta tabbatar da zargin ta,
Tace ba komai tsautsayi ne bata son ya fuskanci akwai wani abu,
To
Yaa kime kuwa sai sowa da ihu take yi,
Madaurin yace wa  bukar yaje ya sayo bandeji don sun daina dauri da tsumma
Daf da zai shigo ne yaji yaa kime na cewa  shatu ni dai kin cuce ni kinga abinda kika jawo min na cuceki kuma kifa kikace kina neman hanyar da zaki zubda cikin nan cikin sauki shiyasa ni kuma na biyo ta wannan hanyar tunda dama a asibiti sunce cikin bai zauna da kyau ba ko wani irin jijjiga jiki tai zai zube shiyasa na nemo karkashi na zuba a hanyar,
Amma dai ko ba komai ai burin ki ya cika,
Amma kuma a an barni da ciwo ko?
    Shatu zatai magana Bukar yayi sallama ya shiga, da kamar bazai jira suba,
Amma sai ya danne ya gaisu gida shi kuma ya wuce Asibiti,
Dai dai wannan lokacin aka fiddo da sauda aka kaita dakin yan bari idan ta huta sai su tafi gida,
  Bukar sanda ya biya yasai kaje dasu maltina na karin jini,
   Ya bayar ana dafawa. Wa majin yata,
   Sauda ta warware kamar babu abinda ya faru,
    Bukar kuwa sai ya yini bai shiga ya duba yaa kime ba itama tana dakin shatu,
   Da daddare ne yake fadawa hajja abinda yaji daga bakin shatu da yaa kime,
Biri yayi kama da mutum nan hajja tace na fahimci hakan amma da yake bani da hujja shiyasa bance komai ba kuma don Allah kar ka sanar wa umar kasan shi da zuciya ,
Insha Allahu amma gaskiya zan dau mataki akan  yaa kime,
Hmmmmm
Bukar hakuri zakayi Allah ya shirye su,
Kullum kina hanani akan kuduri na kice nayi hakuri abinci wannan bata iya ba ga kazantar masifa,
Kar ka damu irinsu abokan zama ake musu xaka ga sun dai daita,
Yanzu hajja kina nufin idan nayi aure xata nutsu?
eh haka nake tsammani idan taga wata tana yi itama zata iya dawowa kan  hanya,
Hmmmmmmm
   Kinsan hajja na boye muku ne akwai wacce nake so amma dai yarinya ce bata isa auren ba,
Wacece kenan
Ummu kulsum ce yar gidan Alh umair,
Kai Bukar zasu bari ka aureta kuwa ka rabota da mahaifarta ka kawo ta nisan dunia ya nigeria ,
Eh zasu yarda saboda mutane ne masu sanin Addini kuma sun san aure babu inda baya kaiwa mutum,
  To amma sun sani kuwa
Eh gaskiya basu sani ba sai dai mama zubaida kullum tana ce min wai ko yar gida za'ayi ne da kai da kanwar taka, nakan mata murmushi kawai shiyasa da zancen auren nan ya taso na gagara sanar da ita,
To ummukulsum din takai shekara nawa yanzu ?
Inaga zata kai sha takwas to ai takai aure anan,
Tab ina! su fa suna dadewa basuyi aure ba sai dai kakansu baya son wannan jinkirin shi,
  Allah ya sanya Alheri, zan cigaba da maka Addu'ar dacewa da mace tagari,
Nagode hajja,
     
YOLA
  
   kyallu dai ana nan anata fafatawa sai ciwo ta rasa miye kullum zazZabi akai gwaji aka ce massasarar cizon sauro ne,
  Ranar tijarar ta ta tashi,samun shi tayi a falo yana tare da kanin shi zai aike shi, wai ya bata takardarta domin wa'adin da ta dibar wa kanta ya kare,
Ki bari sai kin bani ajiyata tukun,
Wacce ajiya kabani ?
Abinda yake kasar marar ki,
Ta duba bata ga komai ba ya sallame kanin nashi,
Yace ma'u na gama dake ko yanzu,
Na mai dake   uwa saboda haka ki bini a sannu saki dai yana hanuna ki bari idan kika haifa min abinda ke cikin ki kika shayar dashi sai ki tafi,
Ai baka isaba,
Cikin banza wallahi zub dashi zanyi
Bismillah. Shege ka fasa akan cikin nan zanyi tattaki naje na samu uban naki na fada mishi duk abinda kike yi tun farkon kawo ki,
Har izuwa yau dinnan,
  Bata son yace zai hadata da Alh saboda tana tsoron halin shi,
Nidai na fada maka,
Nima na fada miki,
Kuma daga yau ko ina zaki je ki tabbatar ni zan kai ki,.
Taja tsuka ta koma daki tana ta shafa mararta,ita kuma duk iskancinta da rashin hankalinta tana son yara,
   BORNO

    Dukkansu sun warke sun koma shashinsu,
Ba'a dade ba sauda ta fara jin alamu irin na wancan karon,
    Bata fadawa kowa ba tayi ta daurewa, har yakai wata hudu ñan ya fara dago riga,
Yaa kime da tai arba ta ganshi sai zancen  baya ya taso na zirga zirgan Asibiti,
Likita yace bazai mata gwaje gwaje ba tunda yayi wancan har ya bata magani,
Tace eh tana shan maganin tsautsayi ya fada mata ta karye
Ya kara dorata akan maganin ya kara maimaita musu sharadin saduwa dole,
   Tace ya sauketa a ung,
Taje ta jido maganin mata sosai wannan karan harda na Asia ta sayo,
Ta fara sha ,
Haba kullum sai ciwon mara,
Shi kuwa tsabar jarabarta,
Tafiya ya kirkira yace ana neman shi. A oman
  Yaa kime dai tayi sa'a an samu  abinda ake bukata, ammafa kullum cikin ciwon mara take ranar da daddare sai abu ya karu sai jini ya balle abin ya wuce tunanin mai hankali, Ta sanar da mai tayata kwana ta kira su hajja suka kaita Asibiti akace shigar ciki ne amma yana son ya lalace saboda may be tana shan wani abu da bai dace ba, amma idan suka duba suka ga ya riga da ya lalace zasu  cire su mata wankin ciki
   Don Allah kar ku cire,
Wallahi ina son abina,
Likita yace duk yadda kike so idan muka ga ya baci dole za'a cire yanzu aje ayi hoto, mugani,
    Yanzu mi kike sha haka da har yayi  miki irin wannan  illar lokaci guda,
Tace babu,
Yace akwai 
Sukai ta kai ruwa rana da likta kafin ta yarda ta fada mishi abinda take sha,
Yace kinyi kuskure a ba kowani maganin asibiti bane ake son a hadashi da wani,
Kinga kin jawo wa kanki ,aka shiga da ita tana ji tana gani aka burge cikin ga uwar azaba ga kunyar da aka barta dashi domin likita ya ma umar bayanin komai,
Ya sanar dashi cewa maganin ya taba mata mahaifa zai yi wuya ta haihu nan gaba,
   Hankalinshi ya tashi amma bai sanar da ita ba yayi waya ya fadawa Bukar yace ba damuwa ,ita ce sila kar ka damu,
   
    OMAN

Kulsum  tana ganin shi ta canza fuska,da kyar ya shawu kanta,
Ashe  wai kishi take yi. Tunda yayi aure,
Yace ina sonki har yanzu idan kuma zaki yarda to zan aure ki,
Mizai hana tace mishi zaki iya zama a nigeria kuwa tace ehh ai kai nake so ba garinku ba ,
Kuma kasani yanzu zan sanar da baba zancenka,
Kai kulsum anya zasu yarda balle sun san ban dadi da yin aure ba,
Kar ka damu,
Umair ya gama jin komai yace to kai bukar mi zai saka karin  aure yanzu?
Yaushe ma kai auren
  Saalim yace a'a baba babu ruwan mu  da  aurren shi abinda inaga zaifi shine muji ta bakin kulsum ta amince zata iya aurenshi?
   Don suna son juna kam,
Inji saalim,
To zanyi magana da kulsum din,
Mama zubaida tace, sai dai kasan bata gama college
ba,
Eh abu mai sauki dama ga yadda aka tanada mishi ya zauna da matar shi,
Inaga sai su zauna anan din zuwa ta kamalla in zai barta anan  to idan kuma can gida zai tafi da ita duk daya,
     An Kira kulsum an tamvayeta  tace ita ta amince dashi,
Magana ta kankama ya kira umar ya sanar dashi akan ya fadawa Alh ya samu mata yana son ya kara aure,
  Da Alh har yaki amma da hajja ta wayar mishi da kai  ta sanar dashi bayanin likita na lalacewar mahaifar yaa kime akan bazata iya haihuwa ba,shine yake son yayi aure ko yana da rabon samun  nashi shima,
   Nan ta mishi bayanin abinda bukar ya fada mata yaji abinda suka shirya akan cikin saudatu,
Ta roke shi ko wa yan uwanshi kar ya fadiwa zancen karin auren Bukar din yace insha Allahu sai dai suji daga baya
   Hidimar mata na damunshi,
Amma ba komai Allah ya tabbatar musu da Alheri,
    Shiri na ta kankama  har Alh malah yaje neman aure da kanshi, komai ya daidaita sai lokaci kawai ake jira,
    Yaa kime bata san abinda yake faruwa ba da yake yana yawan turo mata kudi kuma umar ma yana kokarin   dubata, shiyasa hankalinta a kwance.

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now