🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'ar Nema Wa 'Ya'ya Tsari.Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar:
أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.
O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah.30
YOLA
To inna bana son na miki gardama amma auren hadin nan akwai matsala wani sa'in,
Miye matsalar
Abdulhakeem?
Yanzu inna misalin irin na Asma'un nan ina ranar shi,
Kar ka damu,
Kayi tawakkali da Allah hafsatu halinsu ba iri daya bane da Asma'u,insha Allah zaka samu banbanci amma kafin ka je wurin ina baka shawaran kayi istihara da niyyar Allah ya zaba maka abinda yafi Alheri,
Insha Allahu zanyi,
Kuma inason ka kwantar da hankalinka,
Ka ga duk ka rame ka lalace maimakon ace mutum yayi aure yayi kumari yayi kyan gani amma kai sai uban kasusuwa ba kuma a rashin cefane ba,wallahi da ba don ina tura kannenka suna ganin abinda yake wakana ba da cewa zanyi ko kana daga cikin sahun mazan da basu son cefane a gida,
Haba innata ai ban taso naga haka a gidan nan ba,
To inna nagode bari na tashi,
A'a ka tsaya kace Abinci dare kawai
Lah kar ki damu zan turo Abdullahi ya dau kamin a'a nifa bana son gayyar tara kwanuka,
Ya fita yana dariya yasan za'ayi haka kuwa,
Ya isa majalisar su da suke zama, idan an tashi a wurin aiki,
Nan abokanshi sukai mishi ta'aziyya
Ya ce ya gode,
Can sai ya tsinkayo
Abokin shi yana mishi tsiya
Naso ace yaron nan yazo da rai sai bayan suna zan tambayeka nace yaya akayi har ka iya hada jikinka da biri har aka samo dan mutum?
Misbahu yace don Allah ka kyaleshi yaji da zafin mutuwar
Barshi misbahu ya fadi son ranshi martani yake maida min,
Cikin dare ya tashi yayi sallatul istikhara yayi addu'a bayan sati guda yaji a ranshi yana son ganin hafsatu ya shirya yaje gidansu kanshi tsaye ya shiga ya gaida kanwar baban tashi,
Ta tambaye shi mutanen gida tare da tambayar maijego,
Duk lafiyansu klau,Shiru ya ratsa wurin,
Can ta numfasa tace maman ka tazo gameda maganarku da hafsatu,
Gaskiya ina tunanin hafsatu da zama da kishiya ba wai don 'yata bace hafsatu bata iya rigima ba ina jiye mata rigimar masu kudi
Haba gwoggo
Insha Allahu ba komai. Zanyi matukar sa ido akan zaman su insha Allahu
Zancen kishi da yar masu kudi ma bai taso ba gwoggo tunda kowa halin shine zai fidda shi a wurin miji inaga wannan ba komai bane
Allah yasa bari na turo maka ita yanzu ta dawo daga makarantar islamiyar da take koyarwa,
Ta mike ciki ta shiga dakin yaran nata tayi magana da hafsatu, bakonta yana jiranta a faloBata tsaya wani bata lokaci ba ta zira dogon hijab dinta ta fito da sallama
Nesa dashi ta zauna a kasa ta gaishe shi cikin girmamawa hakan ya mishi dadi,
Hafsat ina so kibani hankalinki zamuyi magana,
Ta gyada kanta,
Nasan kin san komai ba sai na tsaya miki bayani ba, sannan gaskiya ni ba saurayi bane da zan yita zuwa zance gidanku ina ce miki i love you ba,
Saboda haka nake so don Allah tarbiyar da aka miki ki daure akan hakan kuma kar kice zaki ga abinda abokiyar zamanki take yi kice zakiyi sam bazai mana kyauba kisani rayuwar aure ba'a gina ta da karya bani son raini ko kadan haka zalika bani son karya gaskiya komai dacinta ki fito ki fada min bana son rufa rufa,
Ko kina da abin cewa,ta gyada kanta ,
Ke fito kiyi min magana da bakin ki sai gyada kai kike yi sai kace kadangaruwa,
Tayi murmushi ta sunkuyar da kanta
Kinyi shiru, tace, uhm
To nikam inaga zan tafi tunda ciwon baki kike yi, ya mike kice wa gwoggo zan tafi,
To ta shiga ya kare mata kallo don kyau tana da kyau ga nutsuwa kyakyawace ta karshe doguwa fara manyan idanu hanci ziyat kunsan dai kyawun fulani,fulaninma na yola wanda taken garin nasu kenan LAND OF BEAUTY, amma cikas dinshi daya ne bagidajiya ce ko duk ustazancin ne ko kunya ne oho,shidai koma minene baya son gidahumanci da gidadanci,amma bari yaga ko farkon zuwa ne,
Ah Abdulhakeem zaka tafi?
Eh gwoggo zan tafi,
To ka gaida innartaka Allah ya tabbatar da Alheri, ka cewa yayan ma ina zuwa insha Allahu a cikin satin nan,
To zan sanar mishi,
Nagode.
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
AléatoireLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.