🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya daya ce🖕🏼
( daga kinta sai bata)✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Umm imanIna muku jinjinar ban girma
Zubaida AbubakAr Alkali
Uwar dakina:
Aunty kalas
Shitu
Fuskar kamala
Maimuna musa
Sadiya baba
Monita
Matar mala
Hasana daifur Ahmed
Tauhida Balarabe
Binta musa
Hadixa Balarabe
Fatima Abdullahi
Maryam Idris
Rahila Bala Bashir
Allah ya miki rahama.
Rayyanatu Adamuبسم الله الرحمن الرحيم
09
A gigice Aisah ta juyo tana duban shafa lafiya kike?Nan shafa ta rikice tace ina kuwa lafiya, naji kin ambaci haj kyauta, duk wannan abin baanxiye yana jinsu bai kashe wayar ba, Aisah kina jina?
Ta manta ma waya take yi nan tace eh
Hayaniyar mi nake ji ne? Wallahi shafa ce ta tada hankali wai taji sunan yayarta,
Da yake itama tana da yaya mai wannan sunan kuma a oman take itama,
Ya ma kika ce sunan.
Shafa,
Shafa, nan ya nemi su juya harshe kanuri ai kuwa yace yaya siffanta yake?
Ta fara zayyano mishi fara, madaidaiciya a tsawo, siririya, anya ba ita bace kuwa kashe wayar bari nai saving numberta naga, sunanta zai hau kan whatsapp, amma yaya sunan babanta zan iya yin searching a facebook duk details dinta zai bayyana
Ba tare da bata lokaciba ya Adana number wayar a ma'adanan sunayi na cikin waya,
Ya shiga whatsapp ya duba contact din amma ba hotonta bane akai,
Idan ba ya bata gani bane hoton Aryaan ne dan gidan Ambsdr,
Ta rubata ''Miss u my Aryaan.
Baiyi kasa a gwiwa ba ya shiga facebook ya danna ya rubuta sunanta ya danna searching sai ga masu suna shaafa sun jero. Yai ta dubawa har yazo kan SHAFA'ATU LAWAL BUNGUDU. Ya shiga profile dinta yaga information dinta duka:
Tana zaune a Abuja
Daga zamfara
Ya shiga Albums dinta, shekenan yayi hamdala domin kuwa hoton da ya fara gani, hoton ta ne sun dauka. Ita da Aryaan a SHANGRI LA BARR, wani gidan tarihi ne dake cikin Birnin muscat can yayi ta scrolling yana duddubawa wani su da sisters dinta, wasu ita kadai. Ya sauka ya kira sis din nashi,
Wayar na hannun shafa ta mika mata,
Aisah itace fah, kai Alhamdulillah! Ai kuwa kayi dace, ita dai shafa duk ta tsargu duk da ba jin KANURI take yiba jikinta ya bata saboda yadda Aisah take ta kallonta,Baanziye na kashe wayar ya kira Ammi cikin xumudi take tambayar shi kunyi wayar?
Yace Alhamdulillah Ammi Ashe ma tare suke da ukhti course dinsu daya,
Alhamdulillah Allah mai iko,mai yin ? A'a kawai zan sa himma nazo, gaskiya zai fi kam.~~~~~~~~~~~~~~
AL QALAM
Ita dai shafa ta shiga rudu sosai, gashi Aisah taki mata bayanin komai, abinda ya dameta kuma taji an kira pull name dinta kuma ance ba komai, wayar ta karba ta kira haj kyauta taji shiru ta kira a kalla sau 4 kafin ta dauka, nan ta sauke numfashi a hankali shafa, na'am Aunty yy
gida yasu Aryaan? Duk lahiyar su kalau,
Alhamdulillah kina bidar wani abu nne?
A'a gaisuwa ce kawai ina my boy, yana can tare da Baban shi,
Yaya karatun dai?
Gashi yana ta bamu wahala, ai dole abinda ba yaren ka ba ai kam akwai wahala,
Ubangiji Allah ya baku sa'a, Amin a gaida su sultan Areef,
To zasu ji insha Allah.
Ana haka sai ga wata yar islamic studies taxo wucewa, tai musu sallama,
Tace. A'a baiwa ce da uwar gijiyar ta, eh nan shafa tace eh fulani ba, nan Aisah tace ko da wasa bare- bare sune iyayen gijin fulani,
Nan musu ya kaure tsakaninsu, shafa tace kinsan ko musulunci ya riga shigo mana akan ku, inji wa kin manta
Ai kowa idan kina neman musulunci ki zo borno birnin shehu ,
Hahhhaa bari kiji tarihin kafuwar maiduguri, garin Al'amin El kaneem,
Sun kasance sunyi hijira daga dutsen Arfa wanda ake ce mishi'' Jabalin noor'' wato dutsi mai haske, ta wannan dutsin ne aka samu sunan yaren
KA NUR wato KANURI KA din da hausa shine dutsi NOOR kuwa haske ne,
Basu yada zango ba sai da suka iso gamborun - ngala anan suka fara zama.Shi kuma Al,Amin El kanem shi yayi hijira daga gamborun- ngala zuwa maiduguri wato wani abin burgewaawa da kafuwar daular borno shine, AlAmin el kaneem tunda ya taso daga ngala yake karatun qur'ani bai tsaya ba sai lokacin da ya sauke Alqur'ani dama. Kuma Alkawari yayi duk inda ya sauki qur'ani to nan zai zauna shi da iyalan shi, KANEM BORNO EMPIRE kenan musulunci ya dade da shigo mana sai dai masana tarihi sunce babu takaimai ma lokacin da musulunci ya shigo, sun ambato cewa borno ta kasance daular musulunci tun qarni na tara miladiya. To naji amma fa mu fulani mun fiku Asali tunda mu daga sahabi mai girma mai daukaka muga samu Asali, UKBAH BIN NAFIU wanda ya shigo Afrika tun zamanin khalipa usman bin AFAAn zAN-NURAIN, aka turo shi nahiyar mu ta Afrika, anan ya auri yar sarkin rum ITALY kenan, mai suna BOJJO MANGA, da suka haifu ne yaran suka fara yaren fulatanci.
To kinji.Allah ya jikan SHAIKH USMAN BIN FODIO da ya jadda da mana musulunci.Nan mani driver yazo daukar Aisah. Shafa kuma ta shiga motarta kirar 207 sai rafukka quaters gidan Abokin yayanta, nan suka mata masauki don Alhaji bishir yace zai kama mata hayan gida tace bazata iya zama a hostel b a,
Shine ALHAJI USMAN TUNAU ya mata masauki a gidan shi, datijjon Arziki,Allah ya saka mishi da Alheri tare da iyalanshi gaba daya tunda take gidan, bata taba neman Abu ta rasa ba.
Aisah kuwa tana isa gida ta kwashi yadda sukai da Baanziye ta fadawa Aunty yabi, tace kai Alhamdulillah nayi murna!
Yanzu kin sanar wa shafan ne?
A'a ban fada mata ba,
Amma yace satin nan zai shigo in Allah ya yarda,
Allah ya kaimu, Amin.~~~ OMAAN ~~~
Baanziye kuwa yana gama waya ya tashi ya karisa gidan kawunshi yayan maman shi kawu Irfaan ya sanar dashi zai ji nigeria karshen sati,
Kawu Irfaan yace anya ka saurara inaga kamar zan ai ke ka Qatar munyi magana da chaiman na kamfanin mai na qatar oil and distrubution.
Baanxiye kamar zai yi ihu amma haka yace to kawu ba damuwa yaushe ne tafiyar ka zauna cikin shiri inaga zuwa Alhamis yace to.🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.