🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya Dayace🖕🏼
(Daga kinta sai bata)✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
kulsum Bappah
Umm imanWannan shafin sadaukarwa ne ga
Ga dukkan Angwaye da Amaren da aka daura aure:
29/dec/2018
Allah ya basu zaman lafiya,hakuri, juriya da kuma karin muhibba 💞💞💞💞💞💞💞
Fauziyya kuma Allah ya mata Rahama!Addu'ar Haduwa da Abokan gaba👇🏼👇🏼👇🏼
ALLAHUMMA INNA NAJ'AULKA FI NUHURIHIM, WA NA UZU BIKA MIN SHURURIHIM,ALLAHUMMA ANTA ADUDI WA ANTA NASIRI BIKA AHULU WA BIKA USULU WA BIKA UKATIL.
13
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun
Shi shafa'atu taake ta maimaitawa a zuciyarta, ita ko gwoggo mero Albarka take ta mata, tana ganin tsabar kunya ce ta hanata magana,
Baata san cike take da tu'ajjabi ba,
Gani take kamar mafarki, aure ba tare da saninta ba, kuma wai har an sa biki bata san angon ba,
Wayar Aisah ta shigo kamar jira take tayi caraf ta dauka,
Kai wayar ce a hanunki haka,
Bari kawai dama kiranki nake son yi,
Kinsan Abinda yake faruwa kuwa Aisah?
A'a sai kin fada,
Wai aure za'ai man kuma bani da masaniya, ban san waye shiba, ke har ansa rana.
Aisah tai murmushi
To nima maganar da zan miki kenan ansa min biki da yayana haisam,
Wani haisam daya?
Haisam da kinga ce min taku bata zo dayaba,
Shi fa, shaf,
Kinsan bai taba nuna min koda alama ba,
Wallahi ba don ummi ba maihaifiyar shi da sai na bashi kunya kullum a gwasale nake a wurinshi.
Aisah kukan dadi kike yi , nifa ban san waye shiba,
Baki ne? fari n?, masaki ne? duk ban sani ba kuma na rasa wanda zan dosa tunda shi yaya bishir gani yake kamar mun riga da
mun fahimci juna, mun Amince shiyasa zancen yaje wurinshi,
Husna ma fishi take dani wai na boye mata,
Khairan insha Allah yanzu yaushe ne naki, Aisah tace sallah da sati biyu, kina nufin rana daya zamuyi aure Aisah, wai yaya abubuwan mu suke zuwa daya ne kam Aisah?
Idan baki manta ba randa muka fara haduwa Abayar mu iri dayace,
Course dinmu daya,
Duk wasu ra'ayoyinmu daya,
Wayyo Aisah,
Baza mu halarci bikin juna ba
Shafa,
na'am baku taba waya da mutum bane?
Ya kira ban san number ba sai na ki dauka
Wai tsabagen rainin hankali da rainin wayo ya min text, wai dauki waya mijinki ne,
Kinji dalilin dana san maganar ma ,shine na tuntubi husna don na tabbatar ina kira itama ta hau zazzaga min wai na munafurceta, hakan ya tabbatar min da zancen na dau waya gaskiya ne,
Aisah ban san yadda zan tunkari yaya bishir ba,
Aisah ko sai dariya take yi, tsabar mugunta ma dariya kike min?
Wani mugunta banbancina da ke kadan ne ai tunda na san dai ko waye,
Hmmmmmmm
Mtwsssssssss baki da matsala.
Shafa kwantar da hankalinki insha Allah mutumin kirki ne,
Saboda yadda kike fadin dattakon su yaya bishir baza su hada ki da mutumin banza ba.Allah yasa,
Wayyo Aisah yanzu duk zabin da nake son ya faskara
Hahhhhhhhhhh Aisah ta cigaba da dariya.
Allah dai yasa ba gajeri bane,
Amin Aisah nikam na hakura da wasu qualities din da nake so,
Aisah kuwa tsaabar zolaya sai ce mata take, to yanzu yaya batun fidda anko?
Sai anjima ki kike batun anko.
Kat ta kashe wayar
Aisah takira ya baanziye tace ya kamata. Ka kira shafa don tana cikin rudani na rashin sanin waye mijin da aka hadata dashi,
Ammafa kar ka nuna mata kai dan uwa nane,
Kar ki damu don wannan
~~~~~~~~~~~~~
BORNO
Shirye shirye ya fara kankama yadda za'a tafi gaisuwa to dama masu neman kuka ne balle an jefe su da kashin awaki
Abu namu maganin a kwabe mu,
An sanar ranar laraba za'a kai kayan tambaya da toshi kasancewar a Abuja ne duk abin yazo da saukiMmn husn fadawa matan ibraheem da kuma sister dinta da take gwarinpha, da makociyarta da kawayenta don tarban yan kawo kayan,
Nan ta kira Aunty fanta matar IG na police don taji Mi ake tanada idan za'a kawo kayan toshi sannan wasu girki yan garin suka fi so nan ta fara ayyano mata,
Mmn husna tace bari kawai zan shigo da yamma yafi karfin waya.
ABUJA
Laraba tabawa ranar sa:a MALAH AIR LINE ne yake kokari samun ma tsaya a filin tashi da saukar jiragen sama na gida dana waje a Dr nmamdi Azikwe dai dai tuwar shi kenan yayi dai dai fituwar iyalan gidan malah haj saudat ce, sai kyallu da ta biyu ganin kwakwaf sai kuma sistern haj saudat din ,
Manyan manyan motocin da suka faka masu dauke da number malah suka shiga sai MAITAMA DISTRICT AREA
Kyallu sai yada zance take, haj sauda kuwa bata san tana yi ba kunu wa wani gida don ba sa'ar yinta bace,
Isarsu keda wuya securities suka hau wangale musu gate
Sun kutsa gate na hudu kenan suka hango farfajiyar da aka tanada wajen adana motoci, motoci ashirin zasu iya samun ma tsuguni,
Kyallu dai tana rarraba ido a zatonta arzikinsu bai kai haka ba
Nan ta fara tabe baki
Security mata sukai musu iso inda aka tanada can sashen mamansu husna da take saukar da manyan bakinta wanda suka chanchanci sauka a wurin,
Haduwa iya haduwa ba karya ya qayatu wurin kayan kyale kyale dai kam sun taimakawa falon ya haskaka saboda maman su husna ba'a barta a baya ba wajen gyare gyare duk bayan wata shida take canza fenti kayan falon ta mai dashi zuwa na zamani na yayi da ake yi,
Yasha 3D wall paper 3D marbles, to don su dinma zaani ne ta tarda muje amma duk da haka abin ya kayatar dasu
Anka musu iso sun ka zazzauna,
Chan sai ga CHEFS sun fara shirya musu dishes iri iri kama daga na kanuri na igbo yoruba kai harda tsallaken kasan india dana larabawa,,
Wuri ya cika da kayan ciye ciye da lashe lashe,
Nan uwayen Amarya suka fito cikin suturu na ban girma da Alfarma, to dama yaya kowa yasan yan bungudu yasan su da iya wanka sa sutura mai tsada,
Kyallu dai abin ya bata mamaki ashe suma wasu ne ne,Nan aka fara musu maraba lale da zuwa matar IG haj fanta ta fara marabtansu da yaren da suka fi sani kanuri
Aka gaisah suka ce bari su basu wuri su dan sha ruwa.
Nan CHEFS suka fitu suka fara aikinsu cikin hikima da kwarewa, gaban kowa suka iso zasu nuna musu takarda mai dauke da samfurin Abincin da yake tanade a wurin , haj saudat ta zabi tuwon shinkafa miyar ogbono, yayinda sister tace. Asa mata sinasir da miyar kubewa danya sai farfesun kan rago
Kyallu kuwa,
TANDOORI CHICKEN
da RICE $ MILK STEW ta zaba .
Sun gama dai daita cikinsu
Aka fara gabatar da kayan Al'ada na toshi
Akwati set 4 kala daban daban shida shida, shabiyu na uwa ne sha biyu kuma na yarinyar kenan,
Alawa goro chewing gum dozen doxen, sai buhun dabino2
Akai ta sanya Albarka da murna
Amma duk da haka sanda kyallu taso kwafsawa,
Aka basu tukwice mai tsoka tare da kayan tsaraba a manyan bokatai,
Danmbu kaji, soyayyen kaji na larabawa da aka nadeta cikin flour, kilishi, Tandoori chicken, masa yar BAUCHI buhunan shinkafa jarakan mangyada, flour, da yake Aunty fanta ta fada musu yadda suke gudanar da Al'adarsu ta maiduguri aka rabu cikin fara'a da mutunta juna.
~~~~~~~~~~~~~~
Irin wanan kayan exactly aka kaiwa Hajja Aishatu na Aisah don tace ba dauke kafa karkashin jagorancin matar ALH AMINU BUKAR, kuma suma an musu karban girma kasancewar duk abu daya ne.
INA LABARIN YAANA DA HAJJA KIME ???
yaana tai kuka har ba'a kama hannun yaro duk kananun idon nan sunyi luhu luhu, hajja kime kuwa duk yadda tai da daurewarta sanda ta gaza ta gagara zaune ta gagara tsaye,ana cikin haka ta yanke shawaran tura yaana gidan Aminiyarta a 303 kusa da unimaid, ko zata samu nutsuwa fituwarta da trolly kenan sukai arba da binazir zata fannin hajja Aisha sukai kallon kallo binazir kuwa ta kura mata ido don tana son ta tantance,
Yaana taja dogon tsoki ta shige motarta, tana kudirta irin daukar fansar da zatai musu tare da cin Alwashin lalata duk wata kauna da haisam zai nunawa Aisah,
Hajja Aisha ta kira yaa kime ta sanar mata za'a kawo kayan tambaya da toshi na Aisah ta shirya ta zo shiyarta,
tace kanta na ciwo,
Tace Allah kara sauki amma ai bazai hanaki zuwa ba tunda ba a kwance kike ba,
Bari naga!
Ke umurni nake baki ba neman shawaraba don tasan kawai pretend ne bata son zuwa ne,
Kafin tace wani Abu ta kashe wayar,
Yaa kime taja tsuka.
~~~~~~~~~~~~~~
KATSINAN DIKKO
shafa na zaune tana nazarin test din da zasuyi amma rabi tunani take yi duk da cewa ita a ganinta ba abinda zai daga mata hankali,
Amma wannan yana neman chaza mata tunani
Taji wayarta cikin muryar nancy Akram cikin wakar EL DONIA HELWA, tana tsiwa idan bata manta ba wancan number ce
Har tai kusan katsewa ta dauka tai sallam tai shiru
Ya amsa
Ta daure fuska moye? Waye kenan da fulatanci,
Bai saurareta ba ya fara mata magana shafa'atu yaya kike
Tace mishi '' moi jo on mi andama'' da wa nake magana ban sanka ba?
Yasan fulatanci take yi amma bai san mi yake fada ba itama da gangan tai hakan don tasan ko daga danginta ne,
Sai taji yace
Ko ba da shafa'atu nake magna ba........
Ta kashe wayar
Ba abinda ya tsana irin wulakanci nan da nan ranshi zai baci
Ya kara bugawa taki dagawa.
Ya tura test kamar haka: duk daya,
Muhammad yake magana mijinki.insha Allah,
Ayi bacci lafiya.
Taga text din tace dan rainin hankali kai kasani, bazaka hanani karatuna ba.🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.