7

507 34 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕🏼Gaskiya Daya ce🖕🏼
{ daga kinta sai bata)

✍🏽✍🏽✍🏽
Kulsum Bappah
   Maman toxee
Da toxeeya 😜😜😜

بسم الله الرحمن الرحيم

07

      Muscat 
Fituwar shi kenan   ya cire helmet hula  irinta injiniyoyi, duk da sanyin A.C da yake Tashi a office din  zafi yake ji, domin maganar mahaifiyar shi ce da hajja kaka suke mishi yawo, to yanxu shi wazai fara dosa yace bashi da budurwa a yarda? Ya kulla wannan ya since shi kadai, dai ana haka sai ga kawunshi kanin mahaifiyar shi  Abdul shakur ya girme mishi da kadan, nan yake tambayar shi mi yasa shi shiru,ya shafo sumar shi,yace wallahi mutanen gida sun takura min akan maganar aure, Aure? Da kananun shekarunka, kai haba kawu kasan mu can a nigeria da wuri ake aure. To ina wannan course mate dinka da ta nuna tana son ka? Wai kana nufin najwa ? Kai ina! Ai baza'a bari na auri bare ba abin nufi wanda ba kabilar mu daya ba, ka ga ko mahaifiyata ai a ta biyu tazo ,suna da riko da kabilanci, misamman abinda ya shafi maiduguri har ya dangana da arewacin bauchi musamman wani gari Azare,  to sai ka nema a dangi, eh akwai tabbas amma ina ganin kamar yanayin tarbiyar sai a hankali, autar su babanmu wanda zuwanmun nan ka ganta, oh eh sunanta ne wahala , 😄 kyallun ne wani iri akwai yaranta su bintu  fanta yaakurah iya gana to matsalar uwar ta sakalta su sun taso babu tarbiya, gaskiya badar kar kayi sake ka auri irin wadannan matan a farko domin kuwa tarbiyar gidanka zai ruguje, insha Allah kawu. Nan ya tuno yarinyar da yaganta  a gidan Ambassador sageer,  ma farko dai bai san sunanta ba yasan dai tabbas daga nigeria take tunda haj kyauta yaranta duk maza ne, kawai sai ya yanke shawarar yaje gidan ko zai samu wani information akanta, ba tare da bata lokaci ba ya dauki motar shi ya dau hanya, 
    
  ********************** 

  Ba gardama  mai gadi ya barshi ya shiga kasancewar ya saba zuwa , ya sameta a palo suka gaisa take tambayarshi  Aisah da yake wani zuwanta hutu wurin kakannin ya kawota,
  Yace Aisah tana karatu a katsina ai kai, haba tana Alqalam kenan? Eh nan take tace ikon Allah shafa ma can take kuwa, kaunata da   suka zo hutu har ka kaisu shopping ohh! Eyyah nagane  nan mai aiki ta kawo mishi Abinci da abin sha, nan ta bashi wuri, can sai ga Aryaan ya shigo, uncle kazo?  My boy eh tun dazu, uncle  yaushe zaka tai nigeria, nayi kusa , zaka bini ne? Eh  zaka kaini wurin Aunty shafa kasanta ? Wannan wacce take goyona idan tazo? Oh ai ban santa ba, to bari na dauko wayar mama na nuna maka hotonta,yana fita a falon kenan yayi tuntube ya fadi, nan haj kyauta ta fito ta rarrashe shiya dawo hoton da bai kawo ba kinan, badar har ga Allah bai ji dadi ba, sukai sallama ya tafi,amma dai ya dan samu karin haske, yana tunanin idan ya kira Aisah zai tambayeta ko tasan shafan.

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

    MAIDUGURI. 

      Kyallu ne da ya kime a parlour suke kus kus na dai sa kunne amma ban fahimci mi suke cewa ba,  Koma minene idan tai tsami zamuji, suka yi shewa suka tafa tace taso muje mu same shi kafin ya fita, kamar mutanen kirki suka shiga  yaa kime ta kime akan kujeran da Alh Bukar yake zaune,  ita kuma kyallu tana zaune a kujeran mutum daya.
  Suka  gaisa cikin girmamawa mi ke tafe daku naga bakinku akwai magana?

  Nan kyallu suka hada ido da yaa kime tai mata signal,
  Nan ya kime ta fara farfari da ido ranka ya dade dama batun baanziye ne,naji hajja kaka ta damu ya fito da matar aure shine mukace to mi zai hana     tunda gasu bintu ko fanta mi zai hana ya zabi daya a cikinsu? Eh lalle kun kawo shawara, nan suka kalli juna sukai murmushi hakan su zata cimma ruwa,  shi banxiye yasan da maganar? Ko kuma  kunyi shawara ne da kaltum? ko kuma kun ari bakinta kun ci mata Albasa ne?  Nan kyallu ta fara marairaita tana cewa haba yaya kasan kaltum bata da matsala, kuma ma in banda abinka ma ai da   Kai da kaya duk mallakar wuya ne, eh haka ne yaa kime ta karba, ai Alhaji inaga ba sai anyi shawara dashi ba idan ka zartas ai shikenan. Eh banyi auren dole ba haka zalika Alkawari na daukar wa kaina Alkawari bazan ma wa 'ya'ya na auren dole ba ke kyallu shaida ce, dukkanmu daga mazan har matan babu wanda aka tilasta kowa zabinshi ya kawo ni kai na... Sai yayi shiru bazan hana ba matukar shi yazo min da maganar, sai suka ga ya dau waya ya fara larabci yasan da kaltum yake waya. Nan kyallu taji kamar ta bar fallon, amma da yake makira ce tana kokarin ta jefa komarta  ⚓ sai ta dake, bayan yan mintuna sai ga kaltum ta fito ta kofar da yake sadata da sashin maigidan cikin shiga ta Alfarma.
    Assalamu Alaikum yaa kime bata samu damar amsawa ba ta juyar da kanta tana kallon dinning Area.mai gidan ya ganta yayi murmushi, kan kace kwabo kamshin oud da take amfani da shi ya ratsa hancinsu,  ya gauraye da turaren wutan touch me da take turara kayanta dashi, duk daga kafar da zata yi qamshi ne yake kara watsuwa,   ta samu kasa dai dai kafar maigidan ta zauna, bayanta yana shafar kafar shi,  kyallu da yake bata da ta ido ta fara gaidata cikin ladabi,kaltum kanta ya daure don tasan rabon da kyallu ta gaidata ma har ta manta amma tsabar kissa da rashin kunya har da mata wani ladabi, kaltum a zuciyarta tace zanyi maganunku, yanzu ba da bane da kam kunci kashi a kaina lokacin da ban san ku su waye ba, Ah mmn bintu ya su bintu da yan uwanta, lafiyarsu kalau, yanxu ma zancen su bintun ne ya kawo mu, eyyah nan ya kime ta dinga harararta har wata zuciyar ta fara zargin anya kuwa kyallu ba fuska biyu ne da itaba taga kamar babu wata kiyayya a tsakaninsu da kaltum, domin yaa kime mace ce mai zazzafan kishi da ko kare ne matukar ya gifta ta side din kaltum to shikenan ta daina kallon shi, kai tsabar zafin kishin ta da rashin rabo yasa ta daina zuwa umrah da aikin hajji tunda aka aure kaltum tace ai larabawa jinin kaltum ne, ita dasu haihata haihata( kunji fa damsil basirati,da tsananin rashin rabo) nan taji maigidan yana magana da kaltum cikin yaren da ta tsani jinshi, sudai sunyi zuru basu san mai ake tattaunawa ba, can Alh bukar ya numfasa yace....................

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now