10

525 28 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕🏼Gaskiya daya ce🖕🏼
(Daga kinta sai bata)

My Aminiyass 👑
Aisha usman tunau
Maman Al'amin da sadeeq Allah ya rayamana twin
sauwama da siyamA
Ban manta da Amal ba🥰🥰🥰🥰

Annabin rahama ( S.A.W) yace '' kalmomi biyu masu nauyi a mizani masu  sauki a kan harce,mafi soyuwa a wajen Allah :
SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI
SUBHANALLAHIL AZEEM.
بسم الله الرحمن الرحيم

10

    Bukar ina son ka kira mini umaru ina nemanku gaba daya ku zuwa bayan isha akwai maganar da zamu tattauna, insha Allahu hajja zan sanar dashi.
     Umar shine mahaifin Haisam Allah bai bashi haihuwa da yawa ba kamar dan uwanshi bukar, nashi yaran biyu ne Haisam da suraj, saudat Allah ya bata tsananin son 'ya'ya mata sai Allah bai bata ba, shiyasa ta rungumi binazir kamar ita ta haife ta tana mugun sonta komai taga na 'ya'ya mata sai ta saya mata, shiyasa shakuwarsu tai tsanani ita da haisam, suraj ne ma basu fiye shiri ba don shi yana da zuciya ita kuma binazir shakwaba da tsolaya,
       Haisam kuwa biye ta yake yi, shiyasa gaba daya Ahalin gidan Alh malah suke ganin soyayya ce tsakanin binazir da haisam.

   Abinda zai burge ka da zuria suna da matukar son nasu, shiyasa lokacin da suka tashi gini sukai har da sashen yan uwansu mata da suke ciki daya.akai sa'a kuwa mazajen yan uwan basu da matsala  suka tattara suka dawo, mijin Aunty Aisha ne ma yaso ki saboda yana ganin su manya ne,da gyar Alh malah ya shawo kanshi yana tunanin kar wata rana a mishi gori duk da yasan wacece Aisha,
    Sam bata da matsala.
   Kusan ung guda suka samu suka zuba gidaje dana masu musu hidima da ma ai' katansu dai de da masu aikin gidajen man su suna tare dasu, gidajen bukar dana umar a jere suke  iri daya ne, sai banbancin yawan dakuna domin shi bikar mata 2 gare shi umar kuwa sauda ce ita daya, don yana ganin bazai iya mata kishiya ba saboda yadda take kyautata mishi, biyayya kyautatawa uwa uba yadda ta rungumi yan uwanshi, musammam mahaifiyar shi,  shiyasa yan tsurku irinsu kyallu suke ganin kamar ta mallake shi ne, ( kunsan hausawanmu idan suka  ga baka kaiwa karar  miji, yana mutuntaka, bai ci maka mutunci ba kuma ba'a hayaniya shikenan   ka malleke shi kuma ba'a kaunar ya maka abin arziki sai a fara nuna maka tsana)
  Suna idar da sallar isha' suka nufi bangaren mahaifiyarsu,
Tana ganinsu ta sallami masu mata hidima suka kuma bangarensu, nan tace wa bukar ya kira mata Aisha babbar yarsu,
Ya  kirata ta waya, ba bata lokaci kuwa tazo suka risina suka gaidata, suna matukar girmamata kasancewar ta rike girmanta babu ruwanta da hidimar gidajensu da matansu duk wacce tazo fa ni'ima idan bata zo ba shikenan,
      Umar bude mana fili da Addu'a
  Yana gama addu'ar Adda  Aisha tace ni kuwa  sai naga da. Anyiwa kyallu magana sai taga kamar ana ware tane saboda ba ciki daya muka fito ba,.

Bukar yace kyaleta kawai kinsan bakinsu daya da kime, kuma wannan tattaunawa tsakaninmu.
Hajja kaka tace eh a kyaleta.
      Kamar yadda kuka sani na tara ku anan ne saboda ina so ku sanarwa wa ya'yayenku lokaci yayi da zaasu kawo matar aure kowa. Kowannensu ya fidda wacce yake so idan ma a dangi ne ko kuma a wani waje ne, to muna maraba , bama nuna banbancin  jinsi ko kabila, abu daya ne kawai banda kafura indai musulma ce to muna lale da ita, saboda Allah da kanshi yayi magana akan babu kabila da tafi wata fifiko a wurinshi, sài wanda yafi tsoron Allah, haka ne ko ba haka bane?
Eh gaskiiya haka ne,
   Domin dazu maidakinka tazo nan ita da kyallu akan maganar baanziye wai sai dai ya auri daya daga cikin 'ya'yanta kai kuma baka basu goyan baya ba,
   Haka ne.
Ne dai na musu bayanin cewa idan yace yana so da kanshi bazan ki ba ai kannan shine, idan muka bashi da niyya to hakura da hakan shine mafi a'a la saboda bazan takura ayi abinda ba dai dai ba,
Amma ya kika gani hajja ya fada tare da sunkuyar da kanshi kasa.
Alamar girmamawa . eh hakan dai dai ne ko lokacinku ba'a muku auren zabi ba,
Saboda haka su zaba da kansu, saboda kwanciyar hankalinsu yanzu zamani ya canza.
Eh hajja gaskiya yanxu da da ba daya bane, saboda mutanen da zaka iya umartar su da yin abu kuma suyi biyayya ko baza so. Amma mutanen yanzu kiri kiri zasu nuna maka kana musu shishige a cikin lamuransu,
Allah yasa mu dace. Suka ce Amin
   Nan Bukar ya numfasa yace inaga shi dai wannan kamar ya samu.wa kenan?
   Ina nufin baanziye, To dan nema a can dangin mahaifiyar shin ya samu?
A'a yar zamfara ce,
  Abokiyar karatun Aisah ce,
  A'a masha Allah cewar Adda Aishatu .

Ai kuwa tunda suke tare da chuwu na lalle ta kir ki ce,
  Umaru yace ko Allah yaasa,
  Amin
    Amma inaga haisam kamar son juna suke da binazir? Inji Adda  Aisha. Eh to Allahu 'a'a lamu kwanikin baya dai kamar uaa kime tace min wai kamar yana neman kanwarta yaana indai ba na bata jiba. Nan Adda  Aisha tace anya wannan kamar fa shishiginsu ne, saboda kowa yasan haisam ai yasan shi da binazir.amma dai koma minene ina bukatar su hallara anan, dashi da ya samun, da kuma haisam duk su taho insha Allahu juma'ar kar shen watan nan za'a ai zama dasu. To hajja mungode,Allah ya kara miki lafiya, tare da nisan kwana, tace Amin
Ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya.
  Amin dan nan suka karanta kulhuwa kafa goma sha daya da niyyar Allah ya kai haske kabarin  matattun su.
Aka shafa Add'ua aka cigaba da tattauna lamurran rayuwa.

~~~~~~~~~~~~~~
  Yaana Abinda nake son ki dashi shine ki kara kaimi wajen neman yarda zaki shiga a wurin haisam sannan ki fara shiga wurin mahaifiyar shi kina kyautata mata, ai kinsan yadda wannan makirar ( kaltum) ta saye zuciyar saudat kenan da cusa mata 'ya'yanta, musamman maras kunyar ñan binazir idan akwai wanda na tsana a duniyar nan to bayan ta ne ,inji yaana kenan don ina ganin kamar soyayya suke da haisam kowani lokaci indai yana nigeria to suna tare,
Kyalesu kawai ki kira min talatu mai aiki akwai inda zan aiketa can dambua wurin boka nakan dutsin sai ya farraqa tsakanin binazir da haisam.
  
Shiyasa nake sonki yayata
Allah ya mallaka miki Alh Bukar, yo dama ai nawane,
   
   Ai ko ban haihu dashiba. Nawa ne ni kadai wancan  ( kawai tana zaune ne saboda ta haifa mishi yara tana kula dasu,
Haka ne, idan wani ne kam yadda bakya haihuwar nan ai da ya dade da sallamanki,
   
  Oh an ce miki na tsaya ne, idan baki sani ba har india naje, can suka tsafe shi,
Nida shi mutu ka raba( Allah ya rabamu da shirka, wanda yayi nisa baya jin kira)

~~~~~~~~~~~~~~
       Katsina
  Aisah take tambayar  shafa wai shin za'a barki  kiyi  aure yanzu?
Tace wace irin tambaya ce wannan? Me ya kawo zancen Aure kuma, ke tambayar ki kawai nayi, ba dama na tambaye ki, to naji kinsan shi aure mukaddari ne, kuma lokaci ne idan lokacin yayi ba makawa sai anyi,

Haka ne, to ke fah? Ni ai Aure ba yanzu ba sai na gama mana hajiya shafa.
     Ko?
Allah ya nuna mana.
  Amin. 
   Tab Ace yanxu kana cikin karatun kayadda mukai nesan ñan sai ka samu miji iyayenka su Amince dashi, yace bazaka cigaba da karatu ba,
Ke shafa bakin ya tsaya haka,
Ai fata nagari lamiri.
     Yanzu nan da watanni fa, zamu fara shirye shiryen tafiya gamboron ngala ko? Eh kamar yaune na ka gu naje ngala nan naji ance suna da lecturers masu zafi, tabbas hakane,
Haka ake fadi.

~~~~~~~~~~~~~~
  Alh Bukar ne ya kira badaar ya shaida mishi akwai meeting kar shen watan nan,
Yace dama yana hanya insha Allah yanxu ma kawu Irfaan ne ya aike ni.
To Allah ya kawo ka lafiya,
  Nan ya kira haisam ma ya shaida mishi,
Yace insha Allah ina tafe Bappa.
  Haka dai sukai ta kiran yaran suna fada musu, Aisah hankalinta a kwance tasan zancen auren Badar ne,
  
Abin mamaki kuwa zuwa ran Alhamis duk sun hallara,
   Alh umar ne da mai dakinshi saudat suka yima dansu bayanin dalilin kiran.
    Nan mahaifin nashi yake tambayar shi ko akwai wanda ya tsayar yace eh,
  Akwai ta gida ne,to da gaske ne ashe hasashen da mutane suke yi?
      Nan aka kira Alhaji a waya abinda ya katse su kenan
   Washe gari bayan anyi sallar juma'a falon Alhaji malah ya cika da yaya da jikokin gidan, aka bude fili da addu'a akai ciye ciye da lashe lashe,
    Kowa na cikin farin ciki nan Alh Bukar yake cewa ya sama wa binazir bAZe university dake Abuja. Nan akai ta mata Allah ya sanya Alheri.
     Hajja kaka tace to ina haisam ina badaru? Suka amsa gamu nan, kun san dalilin taraku anan ko? Suka ce eh, yauwa badaru a ina kasama min Kishiyar? Kyallu idonta kyam akanshi,
Ya gyara zama yace zamfara.
    Kyallu ta miki zubur,yanzu ka kwammace ka auri bare akan jininka?  Haba haba,
      Hajja kaka tace to, nayi tsammanin ma balarabiya ka samo mana,
  Ina! Wannan bafulatana ce, hhhaahh kace baiwar mu ma zaka aura,
Eh naji kishi dai kike yi. Kyallu kuwa da yaranta kamar zasu fashe.
     Ana zUwa kan haisam yaa kime tai tsagal tace ai she kam na gida ne,
Yace eh tabbas na gida ne
   Nan yaana ta bankawa binazir harara ta sakar mata dariya irin itace din nan,
Bata ankara ba taji Adda Aisha na cewa yaanar ce ko binazir,
      Sai dai yaana inji yaa kime,
Ita dai kaltum ta musu shiru.
Can suka tsinkayo muryar haisam na cewa, binazir ai kanwata ce,
     Haba wa nan yaa kime suka hada ido da yaana, tana murmushin nasara boka yayi aiki,
      AISAH na zaba............... ...

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now