🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'a ga Wanda Ya ce maka Yana Son ka.أَحَبَّكَ الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.
Ahabbakal lazi ahbabtani lahu45
Kariso ciki,
Wai ban gane ba na ganku cirko cirko,
Wai fah na shigo wurin kaltum da niyyar ce mata mun dawo daga Asibiti sai naji kyallu na tuhumarta miyasa ta bari na biki asibiti wai zan cutar da Binazir shine kaltum take ce mata ita ko a da bata dauke ni a macuciya ba balle yanzu,
Kuma yadda take fada mata nayi imani da Allah haka take fadamin nima tana ce min kun ware kanku baku kaunata saboda ni yar talaka ce,
Ku yayan masu shi.Sauda tace ramin karya kurarre ne,
Kuma _KARYA FURE TAKE BATA YAYA_
Kyallu tace kunen ki bai ji dai dai,Ni ba dake nake yi ba,
Sai dai idan zaku nuna min yan ubanci tunda ba ciki daya muka fito da mazajenku ba,Owh shiyasa ki ke hadassa fitina tsakanin,
ai saratu da kuka fito ciki daya da mijinta baki mata ,Wato dama kinso wargaza ma hajja kan 'ya'yanta,
To bari na fadamiki da kam na dauki zugarki da ban gane nufinki ba amma yanzu kam sai dai wata kuma ba dai ni ba,
Kuma wallahi Allah ya isa tsakanina da ke kin hanani zaman lafiya da mijina,
Kin hanani kyautatawa surkata,
Kullum kina nuna min ke mai kaunata ce ashe munafurta ta kike yiKaltum tace ya isa haka ai ita *GASKIYA* *DAYA CE* daga kinta sai bata
Sauda tace kwarai kuwa
Haba kyallu kema fah kina da 'ya'yan nan idan aka musu bazaki ji dadi ba
Ba abinda yafi illa irin kai kawo magana a tsakanin mutane,
Sai kana zaune zuciya daya da mutum
A fara kawo maka sukar shi,
Shikenan sai zargi ya fara shiga tsakani
Idan baka kai zuciya nesa ba sai kallon banza sai sa'insa shikenan sai gaba,
Don Allah kyallu ke ba yarinya bace ki rabu da wannan damuwarLalle yau kun nuna min hadin kai to wallahi bazan yarda sai na fadawa mazajenku,
Bismillah.
Nace bismillah kar ki fasa,Ai dama borin kunya da hauka ake nade ta
Aisah kam yanzu ta aminci da canjin da take ji a jikinta domin ko yaushe a cikin bacci take ga kwadayi
Alhamdulillah baanziye da haisam suna ta samun nasara da cigaba a rayuwarsu saboda sun rike gaskiya a cikin Al'amuransu domin kullum nasihar iyayensu kenan ku rike GASKIYA,
duk abinda zakayi ka rike gaskiya to za ka ga cigaba a rayuwarka saboda ita GASKIYA DAYA CE mai yinta baya tabewa kullum Al'amarinshi gaba zaina yi .Haba sulaiman daga haihuwa sai ka debi jiki ka tafi baza ka bari sai ana gobe suna ba mu dunguma mu tafi ba,
Haba hajiya ai inaga iyayenta baza su ji dadi ba ace ta haihun ina nigeria kuma banjeba wani nawa ma bai jeba ai abin baiyi ma'ana ba
To zumudi sarki TABARGAZA kawai daga haihuwa sai a kama hanya mu tafi,
To mama ko ke bazaki je ba ai kannena sun shirya mu tafi,
Bafa wahala zasuyi ba a jirgi ne,
Ko a iska ne sai suna
Ana haka sai ga mahaifinshi yace tattaunawar mi ake yi?
.wai Alhaji cewa yayi zai tafi Maiduguri dubo yaronshi da matar
Ah eh mana yayi dai dai
To da yaushe kike kaunar yaje
Ana gobe suna,
Sam ba dattako bane ya shirya dashi dasu samira da sumayya su tafi
Yau dinnnan idan yaso su dawo sai su koma kafin suna,
In kuma sun so sai su zauna
Haba hajiya yanzu ace hajara ta haihu mijinta ko wani danginta suki zuwa zaki ji dadi,
Ah toh miye a ciki?
A'ah hajiya
Su shirya a yau dinnan su tafi ya rubuta check ya mika mishi
Ka sai mata kaji kayan tea rago wanda za'ayi kauri dashi,
Insha Allahu zan bawa mahaifiyarka kudi ta sai zannuwa da kayan jariri
Yauwa Abba wani suna kaga ya dace a sa ma yaron,
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.