🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Falalar Tasbihi, Da Godiya Ga Allah, Da Yin La ilaha Illal Lah, da yin KabbaraAbu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito cewa; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ.
Subhanal-lahil azeem wabihamdih.
(sau dari)
جمعة مباركة اليكن
33
Eh Alhajijon ne yace tabari sai ya dawo kafin su tafi,
To amma shi mi zai sa yace haka bayan wancan matar tashi tana nan,
Umm ban san dalilin shi na fadan hakan ba,
To Allah ya dawo dasu lafiya,
AminFadi tashi asarar mai rai kulsum har sunyi Arbain,
Badar kuwa da kyar take goyan shi saboda girman da yayi kana ganinshi kasan jinin ubanshi yafi karfi saboda yaro dai ya koma baki bakin ma irin na KANURAI,
hancin shi da gashin kanshi ne kawai ya debo na larabawa,
Na tabbata da za'a fita dashi za'a ce ba danta bane,
Sun fara shirye shiryen dawowa nigeria
Iyayenta dai dai da cokali sanda aka sa ke mata su an riga da har an turo su nigeria
Bukar ya yiwa umar magana ya karbi key a wurin hajja a kwashe kayan kulsum din kafin su dawo a zuba sabin kayan
Wancan kuma a zuba a store kafin su dawo.anyi an gama dan uwa,Lokacin mahajjata sauran sati daya su dawo,
Amma Bukar ya dan jinkirta tafiyar yana jira ya gama wasu hidimomin shi,
Ana jibi mahajjata zasu dawo kyallu ta fara ciwon karya wai duk don su yaudari Alhaji,
Ta narke ta shagwabe
A ranar da zasu dawo shatu ta tuntubi Alhaji akan akaita Asibiti jikin yaki, suka ki zuwa teaching hospital sai wani asibitin kudi suka tafi,
Tace wa likita bata samun bacci ne kuma babu damar ta huta a gida shiyasa take son ta dan samu hutu ko na kwana biyu ne,
Ba komai ya dirka mata Alluran bacci batai kwakwaran minti goma ba bacci ya tafi da ita,
Shatu ta koma gida ta turo da so mai aikinta
Bata fi minti goma da shiga gidanba mahajjata suka shigo
Alhajijo dakin baki yayi masauki yayi wanka ya kintsa ya fito ya shiga sashin hajja ya gaisheta cikin mutunci da mutuntawa tasa aka kawo mishi Abinci
Ya gagara ci saboda kunya,tace bari to na bayar akai maka
Dakin shatu ya shiga,
Ya tadda yaa kime tana ta zuba a shatu,
Ya yi sallama yaakime dai ta amsa amma shatu bata amsaba ,
Shatu ta umurci yaakime da ta karisa kofarta tasa daaso ta share tayi goge gogen kura,
Ina yini inna shatu,
Ban wuni ba marar tai ido ( kunya ) tsabar walakanci kishiya kayiwa kyallu,saboda ka samu goyon bayan uwarka,
To bari na fada maka kyallu tafi karfin zama da kishiya,
Kai kanka kasan baka isa ka aure taba,
Da kai sa'an akai auren kullum sai rashin arxiki,
Duk hakan bai maka dai dai ba sanda ka yo mata kishiya,
Kishiyarma yar matsiyata,
Wallahi da ina nan kuka zo tafiya saudiyan nan da baza ka je ba shasha sha marar hankali wanda bakasan inda yake maka ciwo ba,
Kamar yadda kika ji nai aure a sama nima a saman naji mahaifina ne ya wuce gaba sanda ya nema min matar
Tunda yasan irin zaman da muke yi da kyallu.
Ai yayi dai dai da ya aura maka matan, amma kasani auren ku da kyallu ya kare takardarta nake so kabani yanzu,
Ya mike tsaye a wani dalili kenan,
Ko kina da hujjar da zakice sai na saketa tunda duk rashin da'a da rashin tarbiyar da take min ni ban nemi na sauwwake mata ba sai ke,
A matsayinki na uwa bai dace ki furta wadan nan kala manba,
Koda yake ba laifin ki bane,
Laifi inna ce da tace mu rufawa juna asiri,
Kinga da naki na bada hadin kai ai da an aura mata dai dai ita maigadin da Alhaji yace,
To tsagiri,ni dinma tsagerancin zaka min,
No no ba haka bane
To ko kaki ko ka so zaman ka da kyallu ya kare,
Hmmmmm yasa dariya uwata ta kaina inna shatu,
Nikam yanzu na fara zama da Asma'u
Kuma ki daina bata bakinki saki a hanuna yake,banga mai tursasani na sake taba ,
Da ma ace baki nema bane, to da sauki,
Ki cigaba da riketa,
Ni kuwa na samu damar da zanyi soyayyata da Amaryata mai halayen yan Aljanna,
Yasa kai zai fita,
Tace idan na hadaka da ubanka ai zaka sauta,
Ba ubana ne yake aurentaba ,
Ni Abdulhakeem nike da wannan damar da ikon saki,
Inna shatu yanzu naji son zama da ma'u ko don ribar da zata samu a gidana ,
Ribar mi ribar rashin kunya ko ta talauci,
Naji wadanan shashashan su umar sun baka aiki,
Eh tabass inna ina gama hutawa da Yar Aljanna zan fara zuwa,
Ribar da nake son yar taki ta samu ,shine,
Duk rintsi idan taga abinda yar Aljanna take yimin a matsayina na mijinta,
Itama ina mata tsammanin zata yi watsi da tar biyar da ta taso akai ta kama na yar Aljanna hafsa,
Na barki lafiya inna
Bai saurare taba ya fice yaje yayiwa hajja sallama ya dauko tsarabar da yayiwa Alhaji da nasu Bukar turarrur ruka masu tsada da sallayar sallah mai tsada sai kuma hajja da shatu dogayen riguna da taimakon sauda yayi wannan sayayyar,
Tace kaje da kanka kayiwa Alhaji godia sai ka wuce,
Yana zaune a falo,
Ya zauna can gefe dashi ya gaishe shi yace zai wuce,
Eh gashi matarka na Asibiti kaje ka dubata kuwa?
Zan shiga anyi min kwatancen wurin,
Owk bari na kira driver yakai ka
Yauwa ga sako don Allah ka tabbata ka kaiwa Prof usman da kanka drivern da zai kai ka yasan gidan,
Nagode Allah ya kara girma idan yaso zuwa wani satin sai ka fara zuwa gidan man,
Insha Allahu,
Allah ya jikan mahaifa,
Yace Amin
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.