16

417 28 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
   
رب نجنى من القوم الظالمين
Rabbi najjini minal kaumiz-zalimin
    
Nasreen baby Allah ya baki lafiya

16
     Binazir sau nawa zan fada miki ki fita harkan mutanen nan,
Mutanen da neman sharri suke mana.
Kuma kinsan dole yanzu haka zai kasance, tunda basu so haisam ya nemi Aisah ba musamman
Yadda yaanah ta kwallafah  rai akan haisam kuma na tabbata dama akwai wani nufi a ransu.

Ammi ke ce kike kyale su shiyasa suke miki cin kashin ai,
Binazir ke yarinya ce, abinda yake  kara damuna daya ne yadda zaman su Badar zai kasance a cikin gidan nan,
Badar bai da hakuri shima, su kuma ga munafurci ga makirci, Ah Ammi kina cewa bamu da hakuri GASKIYA DAYA CE ,fa banga fa dalilin da zai sa ana barin su suna rashin mutunci ba za'ana taka musu burki ba ai JIN KUNYAR MARAS KUNYA MA ASARA NE, ki dai Ammi tunda Allah yayi ke mai hakuri ce sai ki tayi
Ammi ta dan kwaleta, binazir hakuri neman shi ake a koya,
Mai hakuri bai taba faduwa kasa banza,
Nasani da ciwo kam sai an daure kafin ayi nasara,
   Shi kuma Allah ya kanyi talala wa wanda ya bijire mashi, zai barshi yayi ta yin abinda yaga dama lokacin da Allah zai kamashi kuma, babu sauran tsumi babu dabara,
Don Allah ki hankalata autan ammi ki fita batun su,
Kuma don Allah ina son idan Amaryar badar tazo ku samu ku hade kawunan ku kada kubar baraka ta shiga tsakaninku,
  Idan kin lura cikin gidan nan kowa nashi yake so,
   Nasan dai za'ai ta samun takun saka a tsakani musamman kyallu da 'ya'yanta zasu dauki aniyar wargaza zaman lafiyar da zasu shirya da matayensu, tunda basu samu yadda suke so ba
      Ammi cire kunya fa zakiye ki ja  surkar ki a jiki yadda baza su samu gangara ba. Balle kinsan su,
    Za su nuna nan dunia suna kaunarka Alhali cikin zuciyarsu ba haka bane,
  Eh MUSA A BAKI FIR'AUNA A ZUCI
    To Ammi ya akai suka kasa rabaki da ummi ina nifin mummy saudat?
Sun gagara ne kinsan idan aka ce miki akwai ilimi to komai zai zo da sauki lokacin da Abbanku ya auren na kasance bana jin hausa kuma banjin turanci tunda kamar yadda kika sani OMAN kasace mai cin gashin kanta, da yarenta take amfani ba irin nigeria bane da suke amfani da ENGLISH AS OFFICIAL LANGUAGE
NIGER kuma suke FRENCH,
Larabci kawai muke yi to lokacin da aka kawo ni ba mai jin yare na Aunty saudat ce take dan canka jefi jefi saboda ta karanta ISLAMIC STUDIES, amma in English to dole zakai borrowing course daga wasu department sai ta dauki ARABIC LANG,
To kinji saukin da na samu kenan ta iya gaisuwa da dai kananan abubuwa
Kuma dama tun farkon Auren su Allah bai hada jininta da hajja kime ba,
Saboda ita hajja tana da karancin sani, bata damu da kanta ba balle ta damu da dawainiyar miji, sai ya kasance Aunty sauda yar gayu ce mai aji tana bala'in kula da babanku umar, abinci kala kala gamshi ko ina tana nuna mai kulawa na musamman,
    To yadda na lura da mutanen SHIMALU NIGERIA arewacin nigeria suna da karancin wayewa akan kula da miji,
Idan aka samu mace na da wannan ra'ayin sai ace bata da kunya,idonta a bude yake, bayan kuma halal ne, abinda ba'a ganewa shine namiji kamar karamin yaro yake komawa musamman idan ya fara man yanta komai yafi son a mishi ke idan wayayye ne wanka ma ki mishi,
To mutanenku kuma daga zaran sun sa ido sunga haka sai ki zama abar kyama abin tsangwama a cikin yan uwa musamman idan akace kuna zama tare wato zama irin na gidan GANDU,
  Tofah saudat ta fara fuskantar kalubale, wai ta cika iyaye da fi'ili ta fiye son nuna komai ta iya gashi lokacin umaru ko fita baya yi kullum suna leke da juna ana haka ta samu ciki, ai kuma shikenan abinci, gyare gyaren gida ya dawo hannun baffanku umaru hayya ratata inji mai mata tara  ba sai abu ya kara kwabewa ba, wai iskanci ne ba wani lififin ciki,
    Hajja kime ta kara tada hankali wai tana ganin bukar ba namiji bane tunda har sauda ta samu ciki,
rashin zaman lafiya ya kara kankama a gidan cikin hajja kaka tana kwantar mata da hankali har ta sire mata ta rasa yadda zatai da ita, abu yazo akan gaba kyallu ta samu yadda take so,
Nan ta kara mata famfo aje Asibiti bukar yaki duk ana shi tunanin ma yaushe akai auren abu dai har wurin manya nan aka shawo kan bukar ya fara sintirin  asibiti gwaje gwaje kuwa babu wanda ba'ai ba ance lafiya sai dai kwayayen haihuwarta sun gaza shiyasa bata fiye yin RELEASING da wuri ba,kuma mahaifarta tayi sama kadan,
Amma sun rubuta mata magunguna sun kara musu karfin gwiwar su yauwaita yin MU'ASHARA ZAUJIYYA '' SEX'' a wannan lokaci ko Alla zai sa adace.
    Nan fa ta samu nutsuwa amma kuma mi zatayi sai ta kara kaimin wurin shaye shayen  maganin mata
  Bukar kam ya galabaita ba na wasa ba na gajarce muku har maganin karfin maza take nemowa tasa mishi a lemo bai sani ba,
Aiki ba kama hannun yaro ga tsananin kazanta ga rashin son gyaran wuri ita dai burinta su kwanta da kyar yayi na sati uku,ya kirkiro da tafiya oman don ya huta.
   Sauda kuwa tana ta fama ko kofar daki bata iya fitowa tsabar jiri da kasala rufin asiri yar garice aka nemo mata yar zama,
Hajja kime tana ta fi'ili a dole ta samu ciki itama don period dinta ya tsagaita,
Wai fa takanas sai ta shiga wurin sauda tana zubda yawu a leda wai ita ga mai ciki, kar ku manta tunda sauda ta fara ciwo fah bata shiga ta dubata
Sauda har ta fara daukar zafi ta watsar da ita, burinta su rabu lafiya da abinda yake jiginta
Ana haka karfe biyun dare ciwon mara ya addabi hajja kime sai ga jini ya ballo nan ta kira kyallu, kyallu ta tsorata ta kira hajja kaka ba kunya hajja kime take ihu a taimaketa kar ta rasa cikinta aka taso umaru ya kaita asibiti,
Likitoci sunyi iya kokarinsu sun gano matsalar ashe an samu rabon sai dai magungunan da take sha da sunan karin ni'ema sun zagwanyo da abinda ke cikin mahaifar.kunya kamar ta kashe umaru da hajja kaka,
Amma tai mirsisi wai ba wani sharrin mahassada ne,

  Tunda ga nan fa rashin zaman lafiya ya balle  gidan,
kyallu tana tayata tunda dama kawarta ce tana ganin ba'a son hajjar ce.
    Ba yadda hajja kaka batai ba kyallu ta daina shiga hidimar da ba tataba amma fir taki, to abinka da dan kishiya duk yadda kai gani za'ayi ana son rabata da yan uwanta ne,
Kishi sosai hajja take nunawa sauda, da fitinar ta ishi sauda ta lallaba umaru ta koma gida haihuwa,

     To ni kuma bayan an auro ni sai sauda ta samu halinmu yazo daya,
Kuma nima bani da wajen hira ranar da ba ranar girki naba sai wajenta shi kenan sukai iya juyin duniya su raba mu abin ya gagara kasancewar ni bama hausan nake jiba sai dai suyi ta damuwarsu ina kallonsu,ni abinda bana mantawa daashi sai irin yadda hajja kime take dankwalona ko ta tai ta murguda min baki, idan na fito.
Ita kuma kyallu idan taga hajja kime bazata kulani ba amma tana kaucewa zata so kulani musamman da yake an kawo ni da dukiya sosai kuma abin hanuna bai damen ba duk wata Abbu na yakan min aiken kudi babanku ya canza mun duk abinda zan sayo bana banbanci da hajja kaka da margayiya Shatu  maman su kyallu nake sayowa kuna komai zan saya nakan sayo da hajja da kyallu to na samu rangwami a wurin kyallu amma fah hajja kam kiri kiri zata ja hannuna muje madafi tasa a sink ta kona tace naar jahannama  naar jahannama '' wuta wuta,
  Ita dai kyallu kiyyayar ta ragu amma fa bata sona saboda ita mata ce mai isgili da nuna bata son wani ya fiita,

Takan min yake dan dole da abinda nake bata ammafa aka ce maka bukar yaje oman ya dawo an min aika kamar zasu kashe ni
Har na fara tsintar abinda suke fadi.kuma kar kusha mamaki kyallu har daki zata bini ta dauki abinda taga dama bana hanata kai har dogayen riguna na take diba. Hajja kaka ta lura da hakan tasan mugunta ne, tai mata fada sai tasa kuka tace yan ubanci ne,don bata da wanda suke ciki daya ne shiyasa ake son rbata da yan uwanta,
  Bukar yace a kyale ta, to Ammi nikam dawo daga farko mana.
Yaya akai har alaka ta shiga tsakanin ku dasu Abbu,
Cinikaiyya da gaskiya da rikon amanar kakanku shine sanadi kinsan a dunia komai yana da sila!
yadda Abbana ya aure ki,
Rabonku ne,
Amma idan kina son tarihi je ki tambayi Adda Aishatu, 

nikam  Ammi baki fadamin yaya kuke da ita Adda Aishan ba,
         Baiwar Allah ko lokacin da aka aure ni ta so ni sosai, sai dai tsakani na da ita sai sallama ta musulunci nima na amsa mata,
Idan ta ganni zata zo ta rungumi ne da fara'arta,
Nima sai naji ta kwanta min arai

Matsalar daya. Babu dama muyi magana.

amma duk randa zata zo wurin mu sai ta gaso min kaza ta kawo min.
Allah sarki inji Binazir,

ai kuwa yanzu zan tafi ba bata lokaci.

~~~~~~~~~~~~~~

   Ta same ta zaune ta idar da sallar la'asar ta haye kan gadon tana jira ta gama Addu'a tan shafawa ta jiyo ta shafe kan binazir sukai murmushi, ta gaida Adda shatu, kinsan mi ya kawo ni?
Sai kin fada 'yata,
     Tarihi ne nake son ji yau daga bakinki da baya karya,
To yar nema ni ba likitanci kike kokarin karantawa ba?
Eh,
to da kin sauya zuwa aikin jarida,
Ko miyasa kowa yake fadamin haka?
Yaya haisam kullum haka yake fada min. Gaskiya yake fada miki,
    Kinga ki bari sai dare yayi tukunna amma ki sani kwana zakiyi anan,
Ba damuwa bari na fadawa Ammi
   Ina jinki,
Miya faru, Ammi zan kwana nan don tace tana da abin yi sai dare ta fara min, hmmmmmm, ki gaidata Allah ya kaimu,

~~~~~~~~~~~~~~

WAIWAYE ADON TAFIYA

Kamar yadda kika sani Alh MALAH SHARIF Shine sunan mahaifinmu,
Mahaifarshi DIKWA,
  DIKWA, hukuma ce da take karkashin jihar borno mutanen garin sun shahara da kasuwanci,da kuma karatum muhammadiya, Abokin Alh sharif,Alh BUKAR MAINA  yana zaune a cikin garin maiduguri sai Alh sharif ya yanke shawarar tura malah can domin ya samu karatun zamani, kasancewar yana da sha'awar hakan, ba musu tsakaninsu da Alh Bukar ya wuce haka, nan ya sashi a boko tare da 'ya'yanshi  2 maza Al'AMIN DA USMANU suna mai inkiya da MAI BORNO,
  har suka kammala jamia, Alamin ya zama kwararen likita yayinda usman kuma ya zama building ENGR, shi kuma Malah ya karanta  BUSINESS ADMINISTRATION, kar ku manta tun yara karatun bai watsar da nema ba yakanyi. Sare saren shi ya aika dikwa a sayar mishi,
  Har ya fara karfi a harkar kasuwanci,
Alhaji Bukar ya umurce su dasu da kowanne ya kawo matar da zai aura ya gaji da ciyar dasu😨😨😨😨

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now