🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Abin da wanda ya ji wani ciwon a Jikinsa Zai CeAnnabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ka sanya hannunka a wajen da yake maka ciwo a jikinka, ka ce;
بِسْمِ اللهِ (ثَلاثاً) Bismil-lah (3)
Da sunan Allah (nake neman waraka). (Sau uku).
Sannan ka ce;
أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ. (سبع)
A'oozu billahi waqudratih min sharri ma ajidu wa-ohazir. (7).29
Kwana tashi ba wuya asarar mai rai kyallu cikinta ya isa haihuwa babu abinda take ayyanawa sai son jiki,
Takanas inna ta nemo mata masu tayata zama saboda kar haihuwa tazo cikin dare ba kowa,
Babu wani babba a kusa da ita,
Kullum Danejo da inna sai sun mata magana ta daina son jiki amma ina idan banda barci bata da aikin yi '' uwa ba kwaba''
Kamar wasa ranan da yamma tana baccin ta fara jin kamar zatai fitsari,
Daga fitsari sai taji abin ya zarce tunaninta,
Ta fadawa su inna wuro itafa bata da lafiya,
Ko dai abinne to bari mugani zuwa anjima,
A'a nikam fadawa su inna danejo mu tafi asibiti ,
'Yan nan bazaki bari kidan bata lokaci a gida mu kinga idan mutanen da ne,
Wanki zaki debo ki hau yi,
Tab ai mu daku ba daya bane
Nikam idan bazaki fada mata ba bari naje da kaina,
A'a ki bari naje da kaina mu kinsan a Al'adar mu ta fulani ba dai dai bane mace ta nuna tana kan gwiwa ba,
To ai fulani kika ce,
Innawuro ta zagaya ta fada wa danejo ma'u fa nakan gwiwa ,
Subhanallahi tun yau she kenan?
Inaga yanzu ne,
To bari nazo kinga shiga daki zaki ga karamin akwati ki dauko kayan jarirai ne a ciki,
Suka rankaya sai wurin ma'u
Kyallu ba zama sai safa da marwa take,
Kamar wanda aka hankado Alhajijo sai gashi nan ya ganta a tsaye, ke miye hakan kamar wacce kika haɗiyi tabarya,
Waya sani ko tabaryar na hadiya dan rainin hankali
Su innawuro abin ya basu dariya dama sun saba ganin haka,
Yanzun zaka kaini Asibiti ne ko yaya?
Gaskiya kina da raki
Inaji abokaina suna cewa matansu basu zuwa asibiti sai sun kusan haihuwa amma ke daga fara abu kice akai ki asibitin ance miki asibitin cire miki zasuyi,
Danejo tace yanzu dai ba cece kuce zaku tsaya yiba,
Asan miye abinyi
Amma inaga ma'u ki hakura ki kara lokaci kafin a tafi,
Idan an tafi yanzu wahala zaki sha,
A'a gaaskiya nikam mu tafi kawai baku san abinda nake jiba,
A'a ina muka san abinda kike ji tunda bamu taba haihuwar ba,
Ah toh ai ku lokacinku ya wuce,
Inna wuro tana ta kwabarta amma inna,
Kamar kara zugata akeyi ,
Sun tafi asibiti akai sa,'a kuwa yan aikin yamma suna nan ana auna ta akace ta koma gida haihuwa da saura,
Domin yanzu tana mataki na biyu,
Tab lalle, akwai aiki inji Alhajijo
Suka koma gida inna wuro tace to kar ki zauna tashi za kiyi kina zirga zirga tab innawuro ki daina bata bakin ki ta shiga ta kwanta ,amma ina kwanciyar batai mata ba,
Alhajijo kuwa ya shura takalmi ya fita ita kuwa tune ta fara hawaye,
Inna wuro babu yadda batai ba akan kar tayi abin kunya ne,
Wallahi a fada nikam zanyi tunda ni nasan abinda nake ji,
Abu sai gaba yake yi, anata tunanin a koma asibiti saboda tsabar rakin da take yi ita dai danejo tafiya tayi ta barsu , har hudu na asuba abu daya akeyi, ala tilas Alhajijo ya kara jidansu sukai Asibiti, akace za'a gwada ta fir taki wai da zafi ungoxomar tace ruwanki ta kara gaba abinta,
Alhajijo kuwa sai diri yake mata,
Da fa taga abin babu sassauci batasan lokacin da tasamu ungozomar ba,
Aka duba tace da saura kina mataki na shida,
Wayyo na shiga uku,har yanzu da saura?
Eh inaga baki motsa jikin kine dama kuma hakan yake kasancewa idan ya zama ba'a motsa jiki,
Yanzu tashi ki fara zagaye wurin nan kinsan babu abinda yakai zagayen saukar da kan da service yafi budewa da wuri,
Innawuro tace to muje na tayaki,
Alhajijo yace to nikam zan koma gida saboda kin hana ni bacci zanje na kwanta,
Kwanciya ina wannan yanayin?
To cire miki zanyi idan na zauna?
Hmmmmmm
Wajen takwas na safe taji ruwa ya biyo sawonta,
Ai kuwa nan da nan aka wuce da ita zuwa labour room akace faya ce ta fashe,carab taga wata mata kayin ɗa yana fitowa tace sam ta fasa haihuwar zata koma gida,
Kin fasa?
Eh,
Ai ba'a fasa haihuwa yarinya ai kuwa fir taki kwanciya akai juyin duniya ta kwanta taki kwanciya,
Ta fara wani irin nishi, amma tsabar taurin kai taki da kyar aka sa ta kwanta,
Wayyo zanyi kashi,wayyo bayana zai fashe ta fara kiran sallar can ta sake ta kamo Fatiha,ta harde kafafunta ta matse gam,
Nurse din ta maka mata duka a cinya tace gyara kina son ki kashe danki ko?
Kuban abu zanyi kashi,
Tace kiyi anan zan kwashe
Tana nishi kai yana fituwa ta hade jinyarta nan kai ya koma, nurse din zabar takaice tafiya tai taci gaba da duba wata mai haihuwar da aka kawo,ta kira wanda suka kawo Asma'u Abdulhakeem inna wuro ta shigo nurse din tace mata,yarku tana da taurin kai kan yaro ya fito ta matse cinya ya koma,bansan yaya zamuyi da itab,
Don Allah don Annabi kiyi hakuri haihuwar fari ce,ba wani,
Nawa ne muke karban na farin basu mana haka ba,na hadaki da Allah kiyi hakuri tace to naji kyallu kuwa ido ya raina fata ta gama sadakarwa mutuwa zatayi,
Nurse din tazo taga babu alamar nakuda ta kwanta luf, nan dai ta kira likta tai mishi bayani,
Likitan yana dubawa yace abinda ke cikin babu rai shiyasa nakudar ta kwanta,
Na shiga uku ya mutu,
Eh kin kashe abinda yake cikinki
Wayyo na shiga uku ai baki shiga uku ba taurin kanki ya jawo miki sai ki gyara likita zai xo yasa miki ruwan nakuda, ruwan nakuda kuma? eh,
Dole asa miki ruwan nakuda zai taimaka miki wajen baki karfi ɗan ya fito domin kin riga da kin galabaita,kuma yaron ya mutu balle shima yayi kokarin fituwa,
Hankalinta yayi matukar tashi, bakinta ya riga da ya mutu,
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
SonstigesLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.