sakamako 14

351 26 0
                                        

  *14*

Wanda akecema bash yace kakoga Abinda nakegani, guy kodai gamo nayine 
Ganin irin kallon da suke mata yasa tamike dasauri tashige kitchen din jikinta na rawa, madam ta daka mata tsawa tace ke lpia yarkikuwa,

Ehm madam costomers ne suka shigo shiyasa nabasu guri suci abinci, ok to nazaci wani Abun kikayi, tawurgo mata kudi tace taje tasiyo mata maggi a tsallaken can.

Karba tayi tanajin dadin aiken dontasan lokacinda zata dawo suntafi, dasauri takama hanya saida taje,taga bayanan, sai ta matsa gaba wani shagon.

Ta Dade bata dawoba
Madam tace shegiya saida kikaga dama sannan kika dawo ko kin tafi gantalin da kikasaba, aa wallahi baya nanne shiyasa natafi wani shagon.

Baninan jeki kwaso  kwanukan da akaci abinci kizo kiwanke,to tace tashiga gurin cin abincin,

Zaune tagansu sungama Amma basu tashiba kowa yarike waya yana latse latse, matsawa tayi ta kwashe, nagefe gefen takai tadawo ta tsaya tana tunani yadda zata kwashe nagabansu, dakewa tayi tamatsa tasaka hannu, zata kwashe kwanukan, bash yayi saurin saka hannu zai dauka, tanasawa hannunsu ya hadu, wani mugun shock taji,tayi sauri tasake tana maka masa harara shikuwa Banda murmushi babu Abinda yakeyi dama da ganganyayi, kasa kasa yace guy

Am dyeing for dis gal
I swear this gal package, na her type I want,
Zata yi kyau dazuwa club,

Duk tunaninsa batajiba kwashe kwanukanta tayi tashige tana cewa uwarka zaka Kai club tsinanne kawai, ni dama Ina ganinshi, Naga yanamin kama da yan iska.

Murja tacemata ke wai lpia yarki klau kuwa kike magana ke kadai, lpia waka fanakeyi

Ooh nazata magana kikeyi,to kiyi kigama yamma tayi kije gidako, Nina wuce sai gobe, Allah y kaimu.

Itama tana gamawa tawuce gida,abunta.

Washegari ta tashi da mugun ciwon Kai, tamakasa zuwa aikin, tana nan kwance har kusan azahar bata Mike ba ganin kwanciyar bazatemataba yasa tamike da kyar tana tafiya.

Dede runfar Danladi ta tsaya, yana hango ta yace Mimie sai yau shigo mana, adaddafe tashigo,

Yace ke lpia ki kuwa, tace banlpia kaina ke ciwo,subuhanallahi sannu Allah y sawake, bari inkarbo maki Panadol can tsallake.

Baijima ba saigashi da Panadol yadawo bata yayi yadebo mata ruwa a kofi, takarba tayi ta shanye, bata sauran yayi yace ta tafidashi, takara korawa yar sauran indomin ya mika mata talashe, da yamma tatafi gida.

Daddare mugun zazzabi ya lullubeta tadinga kuka Dan batada abinyi, ahaka tayi hakuri har safiya tayi.

Murja tinda taje gun aikin ranar bataga Mimie ba, tin tana hakura har takasa, tayi tambaya, madam wai Mimie batazoba yau ba.

Shegiyar batazo ba kilan gantali tatafi, zatagamudani gobe Dan ubanta.

Itade murja duk tadamu Dan batada waya kuma batasan gidansuba, batasan ko bata lpia bane, ko kuma wani Abu yasameta, allahu a'alamu

Tana zaune saiga samarin jiya sunzo yauma, oder sukayi takawo musu, sai kalle sukeyi, bash yacema guy wai banga fine babe dinnanba fa, kodama banantakeba,

how did u want me to answer dat question,to bari na tambaye babe din can, pls noo Ina ruwanka da ita, wannan ai burning of reps ne.

Sukagama suka Mike,itakuwa murja duk batada kuzari kamar wata Mara lpia haka tagama aikinta tawuce gida batareda taga mimieba

Husna da kyar tamike, tadauko sauran maganinda danladi ya sayo mata tasha,taji bata iya zuwa gun aiki yauma, kamar jiya da kyar takai kanta gun Dan ladi,kozata samu dan wani abu taci, Amma saitaga bayanan, tajira  Shi har tagaji Amma bako alamari Shi, Ranta ba Dadi hakanan takoma badantasoba dan yamma tagabato dama shikadaine ke Dan temakamata gashi bayanan kuma ta daukeshi tamkar Dan uwa

Tafiya tadingayi kamar kwai yafashe mata aciki, Dan mugun zazzabi takeji ajikinta, yana cinta, horn taji Anayimata ba kakkautawa ashe kan titi take batamasaniba juyawar da zatayi taga jawad acikin mota.......

VOTE AND COMMENT

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEStories to obsess over. Discover now