*16*Fizgota madam tayi tawurgata waje kamar wani tsumma tafiddo dubu biyar ta wurgamata tace karna sake ganin ko inuwarki tsinanniya me kashin tsiya kawai.
Murja ce tafito tadagata tana kuka, itama tanata bata hakuri, kije yanzu Amma zuwa two week nasan ta huce saiki dawo,zata maidaki, nasan yanzu harda fushi,
Murja tafiya zanyi kuma yanda nabar uwata haka zanbar gurin madam, to yanzu inazaki, duk inda Allah y nufa, ai daman bansan zanzo nanba tana gama fadin haka ta kwashe kudin tawuce tana kuka, dakuma tunanin inzata nufa.
Tafiya kawai take tana tunanin ita haka rayuwarta zata kare a tambade, kwalla ne suka gangaro mata lalle ummana tayi gaskiya Ina ganin inna bargida zansamu sauki ashe abubuwan ma Kara tabarbaremata zasuyi, Inda nazauna da ko farida, da ya Abdul nasan zasurinka taimakamin, dandanan wata muguwar nadama tadawo mata cikin muryar kuka tace *nayi nadama*
Daga karshe yanke shawara tayi kawai bari takoma kangonta tazauna yafi tadinga gantali, a titi.
Tindaga lokacinda madam takoreta bata Kara zuwa ko inaba, Nan take kwance cikin kangonnan, saidai In tajiyunwa da Dan kudin da madam tabata taje tasiyo abinci taci.
Ranarda tacika two weeks tace Kai kwanciyar bazatayimin ba Idan kudin dake hannuna suka kare fa gashi saura 2k, tana nan tana tunani taji alamar tsayuwar mota dasauri tafito taga maza sunfito su ukku Sanye cikin bakaken suit, Sun nufi ginin, dasauri tanemi gu taboye tana lekensu.
Daya daga cikinsu yace to wannan shine ginin kuma daga gobe insha Allah xa a cigaba da ginin, Don munaso mukammala, kafin next month, wani daga cikinsu yace yes sir, but muna bukatar kayan aiki, to kamar nawa ze isheku, 10mil. inaganin zekarasa mana ginin ok zanturo 12m in case in wani Abun yataso ok tank u sir see u.
Suka kama hanya suka wuce, fitowa tayi tace nashiga ukku dole intashi gobe zasu cigaba da aikinsu, karsuzo su iske ni sukoreni.
Yar ledan kayanta ta dauka Wanda duk murja tabata tamike tafara tafiya, saida tayi tafiya me mugun nisa sannan tajuyo taga babu alamar mota ko wani abu tsorone ya fara kamata, gashi dare yayi kuma babu wani kangon dazata fake, gashi tagaji ga kuma yunwa nadamunta she have no option haka tasamu wata gutter ta kwanta aciki.
Dare na tsalawa tafara jin kukan karnuka da dabbobi kala kala tsoro tafaraji tanajin kar suzo suna neman abinci su cinyeta, Allah Allah tadingayi safiya tayi tamike takama gaban ta Dan Nan bagurin kwana bane.
Tana jin anfara kiraye kirayen sallah ta sauri tamike ta tattara ledarta tayi gaba, tafiya tadinga yi batareda Sanin Inda tanufa ba,
Gurin karfe goma haka tazo wani waje kamar tasha, taga mutane sai hada hada suke, wata me kosai tahango dasauri takarasa gurin Dan Dama yunwa takusa yimata lahani,
Cikin kudin tamika dari tace abata kokon hamsin da kasan hamsin, aka zuba mata, takarba tacinye,
Jin bata koshiba yasa takara mika wata Darin aka kara miko mata, saida taji takoshi sannan tamike tadinga gararanba nan, tin tana ganin mutane har yakoma kowa yatashi, saboda dare dayayi kowa ya wuce gida, itakuma runfar wani shago tasamu ta kwana.
Tana fara jin hayaniyar mutane tasan gari yafara haske tayi saurin mikewa kafin mai shagon yazo yamata wulakanci,
Yau ma kamar jiya gun mai kosan takara komawa tabada kudi aka zuba mata kosai, sannan ta tashi tashiga sabgoginta, haka Indare yayi zata koma runfar ta kwanta..
VOTE AND COMMENT
YOU ARE READING
SAKAMAKO.......THE OUTCOME
Non-FictionLabarin husna, labari mai cike da darussa masu dinbin yawa, labarine na kaddarar wata yarinya Wanda mahaifinta shine yakashe mahaifiyarta a sanadiyar haka tagudu tabar gidan Dan itama yana barazana da Tata rayuwar, da tafiyarta tagamu da iftilai kal...