sakamako 15

335 26 0
                                    

  *15*

Kaucemasa tayi ,Dasauri tabi motar,tana kokarin yimasa magana, amma kafin ta isa har yaja mota a guje,yabar gurin.

Idontane ya cicciko da kwalla, Dan she have no hope yanzukan, tace kilama yagannine shine yaja mota karnamasa magana.

Shikuwa yana ja yafara fada Kaga shegiya tana son jamin sittin, irin sune ke jama mutun Balai tazo ta tsayamin ahanya na bigeta na Kaita asibiti, yayi kwafa yacigaba da tuki, Dan kwata kwata baimasan mimie bace.

Itako kama hanyar gidan tayi tanata tafiya tana tunani, tace kilan ma yamanta dani nice naketa haukana, ranar haka tawuni ba abinci bataciba yunwa nacinta sosai, a daren ranar wunitayi tana tunanin jawad harda mafarki,  daman Kullum cikin tunaninsa take Amma nayau kanyafi yawa.

Haka yauma bataje aikiba, haka kuma tawuni Dan taje still Dan ladi bayanan.

Itakuma murja kasa hakura tayi tacema madam tamata kwatancen wajen Wanda yakawo ta nan,

Hijab dinta tasaka takama hanyar gun cikin rashin saa, taje bayanan saidai takoma, haka washe gari duk bayanan,harde  tahakura.

Kwananta ukku kenan rabonta dagun aiki yaude taji Dan karfi karfi, kuma yunwa ta isheta dole taje gun, tashirya tsab tawuce.

Murja nacikin aiki taji sallamarta mikewa tayi tarungumeta tana sauke ajiyar zuciya, harnaji Dadi, inakika shigene Mimie kwana hudu kenan bake ba alamar ki.

Wallahi Banda lpia ne koyanzu ba warkewa nayiba, kawai karfin haline to shiga.

Tana shiga ta gaisheda madam,

too sai yau kikaga damar zuwa aiki ko, to ki kwantar da hankalin, basaikin fara fashiba sallamarki zanyi, saiki wuce,

wallahi madam bahakabane banida lpia ne,

To Ina ruwana da rashin lpia yarki ni.
Nan suka shiga rokonta itada murja da kyar tayarda ta maidata

Ahaka tadinga zuwa aiki Amma tindaga ranar bata Kara samun Danladi ba Kullum saita je Amma taga rufarsa a rufe rannan tanazuwa taga wani gun tayi tambayar danladi sai yace danladi ai yawuce gida wallahi waya akaimasa wai Dansa yarasu kuma gaskiya da kyar yadawo ganinan dama yace innaganki angyamiki dukjitayi badadi  ahaka de take zuwa aiki , duk jikinta a Sanyaye, Kullum kuma saitama madam banna.

Wasa wasa hartakai two month a gun madam, hakanan ba dadi take maleji Dan tasan intabar aikin wuya zataci.

Yauma kamar Kullum tatafi gun aiki, yanzu Ankara Mata matsayi tana kaiwa costomers abinci.

Suna zaune saiga bash da guy sunshigo, amma yau kam wankan nadaban ne, donkuwa bakaramin kyau sukayi ba, bash yasaka shirt da jeans ga wani uban boot da yasaka gakuma p cap yandora, afuska kuma an Dora wasu black shades,

Dama tindaga lokacinda sukaga husna suka Maida gun permanent place dinsu ko basu jin yunwa sai sunzo.

Murja taje siyo gishiri, Mimie takai musu menu suzaba, ordering white rice sukayi with coslow da peper soup din cow tail,damafa bawani yunwa sukejiba

Shinkafar tafara aje masu, tinda suka shigo ya zuba mata kyawawan idanunsa kamar maye,takoma takawo coslow da pepper soup din, daga karshe kuma tadauko miya, dede tazo aje miyan bash ya kashe mata ido daya tareda lashe baki, yacemata cikin murya mekama da rada u look sexy, jikin tane ya dau rawa bashiri taski bowl din miyar ta kife ajikinshi bowl din kuma ya fashe,

Cikin zafin rai yace whattt! are u insane,hannu yadaga zai kifa mata mari guy yayi saurin rike hanunsa yacewa u all cause dis then y the slap

Cikin takaici yace zaki zubamin miya ajiki kinsan Ina zanje kuwa, ohhh God tarusamin budget, mikewa yayi afusace batareda cin abincinba yayi waje, partyn da basu jeba kenan.

Madam nafitowa tatsin ka mata Mari, cikin zafin raitace kwano na nawa kikefasa min, nagaji da wanan iskancin naki inkin gaji basaiki fadamin ba, Ina suke,su costomomin?

can ciki tace sunwuce, ohh in addition kinkoremin costumers ko to wallahi yau kingama aiki Nan ko ubanwa ze rokeni, itade ba Abinda takeyi inba kuka ba...........

VOTE AND COMMENT

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now