sakamako 26

305 22 0
                                        

   26

  "duk yinin ranar bata fitoba tunani mafita kawai takeyi Amma takasa samun solution kokadan.

Kusan satinta daya kenan bata ko lekawa waje sbda tsoro da takeji tana zaune a daki ta idar da sallah kenan taji hayani lekawa tayi a ta window taga mota ce tashigo Don dibar kaya angama cika motar sosai Wanda yazo kwasar kayan kuma suka koma gefe da Dr koko suna tautaunawa dubarace tafado mata ganin sunshiga cikin office yasa tafito dagudu tashige cikin kaya ta labe yanda bazaka taba gane akwai mutum aciki sungama tautauwa yafito zasu wuce karkarwa jikinta yakeyi sbda tsoron kar aganta, jin anshiga motar har an Tatar yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya,

Tace finally yau Allah y firdata, Amma ko inazuje oho,kwakkaran motsi ma batayi Don kar ajita

Tafiya suka kwasa ba yar kadan ba taringa tunanin ko de wata kasar zasune

Kwanan su biyu ahanya, itakuma ba abinci da drivern yadan tsaya Ina tanasan fitsari ko wani Abun sai tasauka a boye.

Daddare suka shigo garin Lagos bayan duk tagama jigata, drivern ya fita itama tasamu tallaba tafito dagudu..

Dan tsagaitawa tayi tace Barr wannan shine musabbabin zuwa na Lagos batare da bata lokaci tacigaba.......

Bama tasan wani gari sukeba itade burinta kawai karsukamata gudu tafara tikawa ganin garin bakikkirin Ana neman kufcewa da ruwa, ba kuwa taje ko inaba ruwa ya barke, kuma ko mota bata ganiba balle tayi tunanin taimako zaizomata

Tadanyi nisa kuma ruwan Kara karfi yakeyi Don ko gaban ta bata gani gashi ta jike sharkaf sai tsiyaya takeyi...

Haske taga yana gabatota bayan ta tabbatar mota ce kezuwa saurin shiga mota gaban motar tayi tana daga hannu, motarkuwa tsayawa tayi, tayi  sauri tabude tashiga tana rawar sanyi, hayaki taga yana tashi cikin motar tana juyawa taga sigarinshi kawai yakezuka, sai a sanna taji tsoro yakamata, kauda kanta tayi tana karanto addua a aranta...

Sundanyi tafiya me tsawo sannan taga ya faka gefe yasaka ma motar lock yakuma zuge glass din motar tsorone yafara shigarta sosai, rokonsa tasoma yi tana Dan Allah ka taimakamin...

Zan taimaka miki Amma sai kin bani hadin Kai, rokonsa tacigaba gayi amma Sam yaki saurarenta saima karfi da yanemi yasamata ganin yana neman cin galaba akanta yasa ta tafasha cikin motar ko zata ji wani abun,kwalbar turare taji tayi sauren daukota tabuga masa a akai kwalbar fashe wa tayi saiga jini yana gudana kamar ruwa ganin ko motsi baiyiba yasa tagane yamutu tsorone yakamata yafito motar dasauri...

Gudu tacigaba dayi ga dare yayi gakuma ruwan baa daukeba tayi tafiya me tsawo sannan taga ruwan yafara tsagaitawa bata tsayaba tacigaba da tafiya dede wani titi tazo zata tsallake wata mota tabugeta Don Sam shi beganta ba..

Dasauri yafito yana salati baitsaya wani tunani ba ya dauketa yasaka a mota ko motsi batayi addua yakeyi Allah yasa bata mutuba

Direct wata private hospital yawuce da ita Dan Danan aka karbeta aka wuce da ita a&e taimakokon gaggawa aka bata sukayi dressing cewukan da taji sannan suka jona mata oxygen Dan ya taimaka mata.

Dr alious yafito ya tarar da Wanda ya kawota a zauna ya mika masa hannu suka gaisa yace was the name again yace murad

Mr murad amm  everything is well but she's still unconscious Amma nanda 24hrs zata farka, yabiya komai Sanan yace akula da ita sosai zuwa gobe insha Allah zandawo da safe before yaje office

Motarsa ya shiga yakoma gida cike da tunanin baiwar Allah nan hakanan yaji yana mugun tausayinta ranar baccinsa rabi da rabi yayi

Tinda safe ya shirya donzuwa office breakfast yabiya ya sama mata sannan yawuce asibitin direct office din Dr alious yanufa sugaisa suka shiga dakin tare Dan duba ko tafarka amma saisuka samu bata farfadoba wucewa office yayi Don dama yayi latti yace zedawo inyatashi yasan by then tatashi

Fita yayi office cike da damuwa sosai afuskarsa Don ko aikin kiriki beyiba ranar.......

Vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEStories to obsess over. Discover now