sakamako 13

333 28 0
                                    

*13*

Haka taciga da zuwa gurin Maishayi Kullum, in yamma tayi takoma kangon tayi kwanciyar ta,

Gashi har tacika one month dazuwa Abuja, rannan ta tashi takama hanyar zuwa gun Maishayi, yabata abinci kamar yadda yasaba, saida taci takoshi Sannan yace

Nifa ko sunan ki bansaniba
Bata kalleshiba tace Mimie
To ke yar garinnance tace eh
To Ina iyayenki tace sun rasu
To wallahi nide nayi iyakar Abinda Zan iya, Dan nikaina bawani jarin kirki gareniba.
Danhaka gaskiya kinemi wanigun.
Idontane yaciko da hawaye takalleshi a raunane tace inka koreni Banda Inda zanrinka cin abinci.
To gaskiya taimako daya zanmiki zankaiki gun wata mata inyaso ko aiki kyarinka mata.
To tace, yace gobe kizo muje sai inkaiki.

Washegari tazo suka kama hanya sunyi tafiya me tsawo sannan suka isa gun, sallama sukayi wata dirkekiyar mata tafito, kana ganinta kasan ba bahausabace,

Tace aa Danladi inakasamu yarinya me chayu aka?

Wallahi madam gunki nakawota, Dan Allah kidauketa aiki ko wanke wanke tariga maki

Ni Danladi nace maka Ina neman Dan aiki ne, nawa sunsheni,  so katafida ita

Haba madam kataimaka mata marainiyace fa

To inna dauketa mutane ai Dena siyen abincina zasuyi,jifa yadda tayi datti

Taimakamata zakiyi madam,

Husna tace ni Dan Allah ko bazaki biyaniba zanyi inde zaki rinka bani abinci

Haka Danladi ya dinga rokonta da kyar yasamu tayarda, yatafi tadinga godia,

Sunyi akan gobe zata fara aiki.

Tindawuri takama hanyar gun madam, madam saiwani kyankyaminta take kamar taga kashi, ta nuna mata tulin wanke wanke tace ga aikin can kiyi,

Saikusa karfe 10 tagama wanke wanken Don yawa ne dashi tanagamawa ta hadata da shara, tass tashare ko Ina, takuma hadata da hura murhu, saida tagama sannan akabata abinci Wanda mutane sukarage taci harta ture tanata ganin yan aikin sunata aikinsu,

Can wata daga cikinsu tazo tamata magana,
Amma yau kikafara zuwa ko
Eh yaunafara
Nisunan murja kefa tace
Sunana Mimie,
Mimie me ya aikeki aiki kasan matannan wallahi batada kirki kokadan nima wallahi nagaji neman hanyar gudu nakeyi
Bakomai zanyi hakanan, sai nadinga kiyayewa,
Kuma hakane, Allah y tsimake mu sukace Amin tajatasuka wuce ciki tare

Sai karfe shidan yamma sannan tabarta tatafi da kyar take tafiyarma Don tagaji ga uban aiki datasha,  Amma tace hakanan zanzauna tinda inaci  inkoshi.

Hakama washegari tafito da wuri tafara akinta, tana cikin wanke wanken tsautsayi yasa tafasa plate, ranar dukantane kawai madam batayiba, kamar zatacinyeta, har abinci taki bata ranar  wai punishment dinta kenan,

Murja ce tadauko nata abincin sukaci tare, cikin kwanki biyu sun shaku da murja sosai, takawo mata kaya Dan ta canza najikinta duk sunkode.

Hartafara sabawa da jarabar matar, intanayi bata damuwa.

Tin  lokacinda husna tafara aiki gun, customers suka fara mata yawa kowa ribiben shagon akeyi.

Ta Kanje gun Danladi suyi fira inta taso aiki watarana.

Yanzu harkosawa takeyi gari yawaye tatafi gurin aikinta Don,yanzu da tasamu murja, sukanyi fira ta debe mata kewa,

Duk idon murja takawo mata firar ina danginta sai tayi saurin kawar da zancan.

Duk Inda taje bata taba reviling identity dintaba, babu wanda yasan labarinta, Don bata son tabada chance dinda zaayi bincike akanta so kowa ya tambaya cewa take sunanta Mimie.

Ranar suna zaune suna fira cikin gun cin abinci saiga wasu samari sunshigo kana ganinsu kasan kudi sunzauna musu, daya daga cikin su babu Inda idonshi yasauka sai a kanta, yawani kwallo ido kamar yaga Abinda tsoro
Dan uwan yacemasa Kai lpia yarka kuwa, ido nane yayi gamo,what an epitome of beauty.........

VOTE AND COMMENT

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now