sakamako 32

277 18 0
                                    

      30

"A Aminu kano  international airport yasuka kamar misalin karfe 12:pm kasancewar babu kowa A gidan nasu yasa babu wanda yazo daukarsa adaiadaita ya samu yashiga yace masa nasarawa Gra zasuje, tafiya sudanyi me nisa sannan aka saukeshia a dede bakin gate din wani gida, gidan ginin zamani mai kyau sosai, sauka yayi yamika masa kudi da yar karama Jakarsa yashige batare da ya tsaya karbar chanjiba

Sallama yayi daga bakin kofa, wata yar dattojuwar matace zaune cikin ado tayi kyau sosai Sanye take cikin gown Brown ta dry lace sai wal wali take, fara ce Amma ba sosai ba kana iya kiranta da black buety

Karasowa yayi kusa da ita yamata side hug tana welcome home murad, tanks umma ya kike ya gida, alhmdullah how was the journey, Alhamdullh umma ta, aikifa komai alhmdullah umma bari naje nayi wanka in chanza kaya sai indawo to bakomai Ina nan inajiran ka dawo kafadamin albishir din da ke tafe  da kai daga ni akwai magana a bakinka, murmushi yayi yace umma kenan lets just come back zakiji kuwa, mika masa key din hannunta tayi ya karba yawuce

Dakinsa yawuce yabude Wanda rabonda da yabudesa anjima don ya Jima rabonsa da kanon, wani sassanyan kamshine yabugi hancinsa, lumsha ido yayi yana shaka yana Kara jin kaunar ummansa na tsrgashi Don yasan kadan ne daga cikin aikinta.

Banyan kamar Awa daya yafito Sanye cikin kanan kaya sun masa kyau sosai, ya tarda ita zaune tana latsa waya, kayi sallah ko, eh umma daga masallaci ma nake, good oya muje kaci abinci

Daning yawuce direct don dama yunwa yakeji sosai, bubbude warmers din yayi wanda aka danka su akan dining din wani kamashi na tashi me Dadi, Karasowa itama tayi tamusu serving saida yace yakoshi sannan, kallonta yayi yace umma na I missed ur cooking kinsan abincin ki is a special one, murmushi tayi tace Bana son santifa, wai  umma Ina yaran gidan ne, basanan sun je islamiya, a yau Saturday din,  eh tahfiz mana ok namanta, mikewa yayi yace umma bari naje mugaisa da frnds zuwa anjima zanzo muyi fira, to adawo lpia.

Tinda ta tashi takeson kiranshi Amma takasa kuma batasan meyasaba, duk jinta taken somehow batasan dalili ba she is just unhappy har mamay tagane hakan ta tambayeta Amma tace bakomai, tana kwance cikin tunani taji ringing din waya sauri dauka tayi Don tasan shine bayan shi ba me kiranta, daga dayan bangaren Akace

Kanwata ya kike shine ko kinemi yayanki ko

turo baki tayi kamar tana gabanshi tace ba kai bane katafi kabarni,

Oh ni bana ce miki it's urgent ba kuma innadawo zan miki bayani

Kamar zatayi kuka tace to yaushe zaka dawo

Jibi fa nace

Toh Allah y kaimu ka gaida umma tafada tana goge kwalla

Lallashinta yashiga yi, yace toh shikenan nafasa siyen tsarabar

Kayi hakuri nadena

Sauke wayar tayi tana share kwalla Amra dake gefe tawani tabe baki Taja uban tsaki, juyawa husna tayi ta zabga mata harara tamike tashige toilet.

Bayan isha suna zaune shida umma tace to inajinka

Umma Daman maganar aure ce tadawo Dani, fadada murmushinta tayi tace Alhamdullh ashe daman zanga wannan lokacin, wacece ya sunan ta kuma a can din kuka hadu Amma de yar arewa ce koh Don kasan bana son kwashe kwashe,

Sauke kansa yayi yace umma sunan ta husna, to masha Allah, kuma a can muka hadu, Amma umma banson adauki lokaci da tsawo,dama me zaa jira abinda ake jira tuntuni, kuma wallahi umma marainiya ce tausayinta nakeji, Wayyo Allah sarki Amma to aiki take a can legas din kokuwa gun yanuwanta take, shiru yAyi yafara tunanin yanda ze gyama umma wacece husna, umma wannan labarine me tsawo wallahi kuma sai kin tausaya mata nan yashiga ba umma labari tinfarkon rayuwarta har Lokacinda yataimaketa har izuwa yanzu kamar yanda tagyamsa

Akufule umma tadago Kai tana kallon shi, Amma ban taba sanin Kai shasha bane sai yau, kazomin da labarin kanzon kurege labarin banza kacemin inyarda dashi,

Umma wallahi iya gaskiya kenan babu karya acikin wannan batun

To inkai mahaukacine muba mahaukata bane, tazauna ta tsara maka labarin banza kaikuma a Taka karamar kwakwalwar har kayarda,toh baa taba auren marar asali a zuriyar muba kuma bazaafara a kanka ba, wa ma yasani ko karuwace ko kuma wani mugun abin kunyar tayi tagudu daga gidan su,

Murad ji yayi kamar ansoke shi jin umma ta ambaci karuwa, umma ki fahimceni dakyau......

Baigamaba tadaga mai hannu tace dakata malam, Karka sake wannan zancen, taimakon dakayi mata allah y biya,kaje ka nemo wata bahanaka aure nayi ba Amma wannan bada yawunaba wallahi waishin Ina yan matan naka masu sonka, kokuwa duk fadin kano yan mata sunkarene

Umma.....

Rufemin baki sakaran banza saidai sonta yakasheka Amma wallahi inhar Ina raye bazaka auri yar barikiba, ,Mara tunani kawai tashi kaban gurin takarashe maganar cikin karaji, in wani abu tama Ina maka a dduar Allah y yayema inkuma mafarki kake kayi gaggawar farkawa

Mikewa yayi jikinshi ba kwari yanufi dakin sa kwamciya kawai yayi yama rasa ya zai bullo ma alamarin kansa ya daure dole yashawo kan umma amma tayayam idea ce tafado masa murmushi yasaki ganin yasamu mafita a dduar sa Allah yasa hakan yayi aiki dahaka bacci yayi gaba dashi.

Vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now