sakamako 35

488 27 10
                                    

       
35

Agurguge

Washegari tinda safe hanan tashirya cikin shigarta ta barrister tawuce court don dama already anshirgar dasu kotu tagama duk abinda yakamata suyi,  daga nan akabasu date ranar dazusu zo don gabatarda Kara,

Hanan daga nan wucewa tayi station Inda aka rufe husna bayanai suka yi sosai duk tagyamata abinda zata ce a kotu Inda antambayeta.

2weeks later

Barrister hanan ce Sanye cikin suit baka da wig and gown, daga gafenta kuma prosecuting lawyer ne shima tsaye da irin shigarta, gardama suka yi sosai Inda hanan ta fadar ma kotu yanda tausayin ya gifta takashe shi batareda sanintaba,inda shikuma wancan Lawyern yake cewa ai hukunci mai kisa, kisane.

Bayan tambayoyi da kayima husna dakuma dubannan hujjoji da kuma quotes da hanan tabada yasa aka yanke mata shekara biyar a gidan yari da horo maitsanani.

Hanan tanemi alfarmar kotu danaso kotu tasa akama ta kuma yi gaggawar hukunta wannan matar wacce ke kai yaran mutane dakuma shi likitan dake karba, ahaka aka watse a kotu akan zaaje kamo Dr koko  dakuma hjy zainab.

Yan sanda ne suka tangaza ke yar husna zasu wuce da ita gidan yari, jiyowa tayi tana kallon hanan tana share kwalla, husna zuwa tayi ta rungumeta ita kwalla take tace karki damu kamar gobe ne everything will be gone kinji ko, daga mata Kai tayi tareda share kwalla, haka yan sanda suka wuce da ita gidan yari.

Shirya hilux din yan sanda akayi da wasu ma aikatan kotu zuwa garin abuja, yarinya suka samu sukayi plan yanda zasukama Dr koko don Idan sukayi wasa ze kubuce musu, bayan duk sungama karanta ma yarinyar yanda zatayi idantaje suka kaita kofar gidan hajiya zainab,

Zama tayi ta makure kamar gaske, hajiya zainab nafitowa yarinyar ta nufeta cikin sigar ban tausayi tace don Allah hajiya kitaima kamin iyayena sunrasu sunbarni Banda kowa, murmushi hajiya zainab tayi tace kwantar da hankalin ki baby kinkawo kuka gidan mutuwa, muje ciki suka shiga ciki tare da yarinyar, abinci tafara bata taci ta koshi tayi wanka tabata kaya masu kyau tasaka haka hjy zainab tadinga Kula da yusra har kwana ukku.

Hjy zainab tagama shirinta cikin kaya na alfarma, tace ma yusra tafito itama dam tagama shirinta tsab cikin kayanta masu kyau, sunshiga motar hajiya takoma ciki dauko key, dasuri yusra tayi dailing call da agogon dake masake a hannunta tace komai natafiya dede yanzu zamuje gidan likitan get prepared dasauri takashe ganin hajiya zainab na tahowa,

Basu tasaya ko Ina ba sai gidan Dr koko, as usual babu wani dogon bincike sucurity suka bar hajiya zainab tashiga don daman customer ce, gabatarda ita akayi gaban Dr koko, ya tarbeta hannu bibbiyu akabata daki hajiya zainab kuma tawuce.

Washegarin ranar da aka kawo ta aka dauki neighbour dinta  tana kallo akawuceta da ita aka hada ta gardi, yusra toshe kunnuwanta tayi jin ihun naigherbour din.

Bayan kamar two days aka dauki yusra, farko aka fara shiga da ita dakin da ake ajiye masu ciki da masu jarari matan dake kwance masu ciki sunkai su 30 sbda gurin babbane sosai kamar ward din asibiti, gakuma masu jarirai,  Kula da kuma abinci sosai akebasu babu abinda suka rasa.

Wani ketone Ana cemasa tiger  ya tangaza ke yar yusra zuwa dakin da suke disvirging mata, cewa tayi Dan allah ina jin fitsari, wani mugun kallo yamata yace inawasa dake, plss wallahi dagaske nake cewar yusra, ok muje,

har tailet ya kaita yamata tsaye aka, kamar zatakuka tace plss excuse me, ke zan ci uwarkifa, to agabanka zanyi fitsayin plss kafita, Dan matsawa yayi daga gurin,

Lekawa tayi tabbatarda tiger baya gurin,dasauri ta Danna agogon ta ma yan sanda text, saurin kira tayi tace u just have to hurry up, saurin katsewa tayi jin tiger nashirin tahowa, murtukewa yayi yace keda ubanwa kike magana, maraicewa tayi tace no one.

Yan sanda da sukayi ma gidan zobe sunkai su 50 da security  bakin gate suka fara bayan duk sun harharbe su suka shigo, Dr koko suka fara dam kewa don dama shine main target dinsu, hajya zainab daman tuni sukayi ram da ita ranar da takawo yusra.

Shiga sukayi su ka kakkama su tiger matan kuma akayi rescuing dinsu aka kaisu asibiti.

Washegari tinda wuri suka kama hanyar legas, direct kota aka wuce dasu, nan da nan alkali yayi musu hukunci Dede da laifinsu bajimawa aka wuce dasu gidan yari............

Murna sosai hanan tayi ganin tasamu nasara a sharaar.......

Kunyi hakuri plss bayawa, and I am appologysing da jina shiru two days.

Vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now