33
" Da Abinda ya kwana kenan Don haka yana tashi bayan sallar asuba Kobi takan cikin gidan beyiba ya wuce gun kawunsa
"A'a Murad Kaine a agaida namu,cewar matar kawun nasa
"Eh wallahi anty Ina kwana
"Lpia Lau yaushe a garin
"Jiya wallahi, ehmm anty uncle na nan yafada yana shafa Kai
"Eh yana nan bari amasa mgna" tafada tana shigewa cikin gidan
Badadewa saiga kawu yafito har kasa yaduka ya gaisar da uncle din nasa amsa yayi cikin fara'a, cewa yayi akawo musu breakfast bayan.
Umma jin shiru murad baishigo ba tasan lalle fushi yayi, itama bataji dadin hakan ba Don tana mugun son danta, Amma yazatayi son da take mai baze hanata fada mai gaskiya ba kuma itafa bazata amince da yarinyar ba.
Kawo ne zaune ya tattare natsuwarsa yace inajinka murad
"Kawu daman ba wani abu bane, daman aure nake son yi kuma shine nafada umma tace wai bazata amince ba,
Ahh murad fadamin gaskiya mahaifiyarka bazata taba haka Aureba tafikowa son ganin hakan
Shafa keyya yayi yana kawu labirine ai tsawo nan yashiga basa labarin kamar yanda ya ba umman sa
Kawu ya kada kansa cikin gamsuwa yace ka tabbata gaskiya ne Abinda kake fada
Eh Kawu iya gaskiyar kenan, kuma Sai naga kamar jahadi zanyi
Kwarai kuwa murad zamuyi mgna da ita ni zan jaronci aure karka damu Ina ita yarinyar tAke
Tana can legas din ganin bai cancanta muzauna gida daya ba yasa na kaita gidan abokiyar akin mu
To yayi Allah yayi ma albarka ya baka ladan taimako bada jiyawa ba zaa daura auren zuwa nanda wata daya
Nagode Kawu Allah y saka da alkhairi.
Yana zaune saiga Salem first born din Kawu daki suka wuce suka sha firar su har Sai dare sannan yawuce gida
Bayan yadawo yashiga gun umma, dauke Kai tayi kamar bata ganshiba, matsowa yayi yace umma na kiyi hakuri insha Allah bazanyi Abinda bakiso ba inde kan wannan na hakura kinji umma, kallon shi tayi tace daga ina kake, wani important abu najeyi dama shi ya kawo ni,
Abinci yaci yakoshi ya sanarda ita flight din 10am zebi insha Allah, tho Allah kaimu amin
Tinda wuri yatashi yahada karamar jakar shi da yazo da ita break fast yayi a gaggauce yama umma sallama direct airport ya tsaya badade jigirnsu yadira a garin lagos
Kamarjira yake baije gida ba saida ya wuce gun husna nan yaci abinci yamata bayanin komai, kalar farincikin da tashiga baya misaltuwa, nan da nan kuma farincikin ya gushe tunawa da tayi kowa, kowace uwa burinta takai yarta gidan miji Amman ita Banda ita, kwalla yashiga sauko mata lallashinta yayi harsaida ta Dena kukan sannan ya wuce.
Bayan tafiyar murad kawo yazo har gida gun umma da maganar nan, Amma tace itafa murad baze auri Mara asali ba, da kyar kawo ya shawo kanta da nasiha da lalama Amma badon tayarda ba Don kawai anfi karfin ta, in Kawu yace abu bata isa ta musa donmin kuma shine babban wansu baki daya.
Tana shiga daki tadauki waya cikin fada tace murad shine kaje ka hada nida kawo ko ka kyau ta, aure ko ban hana ba Allah y taimaka, cikin lallausan lafazi yace umma kiyi hakuri bahaka abin yakeba, don allah kisama aurenan albarka, inkuma bakiso har yanzu se na hakura nafison farincikinki akan nata,ki kiyafemin inna bata miki rai, Allah y yafe mana baki daya, Allah kuma yasa albarka Amin umma haka nake son ji takashe wayata
Ana saura sati biyu daurin aure Kawu yace ya taho da husna kano nan gidansu su shirya kafin lokaci yayi, toh Kawu zamu taho insha Allah
Zuwa yayi gidan su Amra yayi sallama da mami yamata bayanin komai ba Abinda ya boye mata bakomai murad alalh y saka maka da alkhairi kuma allah y taimakeka karike yarinyarnan amana kaga marainiyace allah y sa alkhairi in kundawo munzo, toh hajiya nima nagode Allah y bar Zumunci.
Washe gari morning flight zasubi tattara kayanta tayi tass sukayi sallama da mamy nasiha sosai tamata me shiga jiki irin Wanda uwa kema yaranta, kuka sosai takeyi sbda a Dan zaman nan sunshaku haka su Amira sunata kuka, har Amra da ba shiri suke ba saida taji ba Dadi haka sukayi sallama cike da kewa ta wuce direct airport suka nufa ba jimawa suka sauka kano ta dabo........
Vote and comment
YOU ARE READING
SAKAMAKO.......THE OUTCOME
No FicciónLabarin husna, labari mai cike da darussa masu dinbin yawa, labarine na kaddarar wata yarinya Wanda mahaifinta shine yakashe mahaifiyarta a sanadiyar haka tagudu tabar gidan Dan itama yana barazana da Tata rayuwar, da tafiyarta tagamu da iftilai kal...
