*24*Hajiya tashiga ciki tayi sallama taji shiru, daki tanufa Nanma bakowa karar ruwan dataji ya tabbatanmata da mijinta wanka yakeyi, guri tasamu tazauna, tanajiran Shi yafito,
Yanafitowa tace aa honey wankake kenan Inata sallama ai, wallahi kuwa, mikewa tayi tafita, tace ma baby jeki kiramin Mimie, inata kiranta Amma bata amsaba kila baccitake,
Je dubamin dakin to, ok tace tamike, tashiga dakin ammataga wayam, gakuma kayanta da komai, saitayi tunanin ko tana toilet, guri tasamu tazauna, Amma har 5mins bataji alamun mutumba bude toilet din tayi taga wayam,
Dasauri takoma tacema momy batagantaba, where could she be, tambayar mijinta tayi tace baiji motsin Mimie ba Amma sai yace Shi duk yau ko motsinta bejiba.
Kamar wasa gashi har bayan asr Amma ba Mimie ba alamarta, nan da nan hankali yatashi, momy zuwa tayi gurin megadi, tace ko Mimie tafita, sai yace mata eh tace kece kika aiketa, Amma bata dawoba, eh gaskiya nide bangantaba.
Komawa tayi cikin gida ta dauko hijab suka nufi gun police Don bada cigiyarta, anyi magana dasu sunce insha Allah zaa nemota.
Tinda suka koma gida baby ke sharbar kuka wai Mimie ta bata, momy ce tadinga lallashinta.
Itakuwa gudu tadinga yi harseda taga tayi ma unguwar mugun nisa tukun ta tsaya tana haki, lokaci guda kuma ta fasheda kuka, tanacewa wai meke faruwadanine, ahaka zankare rayuwa a titi,duk Inda naje da abubuwa sundedeta sai wani Abun yafadomin, kuka tadiginyi, hajiya nasan ban kyauta mikiba, Amma kiyi hakuri, hakan shine kadai, mafita nima ban so rabuwa dakuba, baby bansan halinda zaki shiga ba inkika wayi gari kika ga bannan ba ahaka tadinga rusar kuka har seda tagaji Dan kanta ta hakura.
Mikewa tayi taciga da tafiya tana matsar kwalla gwaninban tausayi, harseda tazo wata yar kasuwa sannan tsaya, wasu tasamu suka Dan tsammata abinci taci tasamu wata runfa tayi kwanciyar ta.
Washe gari tamike tashiga cikin kasuwar wata hajiya tagani tasayi kaya masu uban yawa, taimaka mata tayi takaimata kayan mota, dari biyar tabata, ta karba tanata murna, don tasamu na abinci.
Haka tadingayi har tsawon satin daya in anyi siyayya takwashi kayan takai abata dari biyu,dari biyar .
Tanan nan zaune saiga, matar rannan ta dawo, Kara kwashe mata kaya tayi takai mata mota, matarce tajuwo tace, yarinya wai ke inane gidanku, Mimie tace banida gida,to Ina iyayenki, sun rasu duka biyun, ta Gyada mata Kai, Allah sarki Allah y jikansu, ai baki gyamin dawuriba da na taimakeki ai rayuwar titi be kamace ya maceba.
To shigo muje tabude mata mota tashigo, Taja suka Kara gaba, saida su kaje gidan hajiya tayi wanka tabata kaya masu kyau tasaka, taci abinci sannan, tace tatashi suje Inda zata Kaita.
Adede wani gida suka Kara yin parking mai kyaun gaske Wanda yaci uban nasu baby,cematayi tashigo nan takara ganin abin mamak, gidan gari gudan, Dan akwai asibiti babba a gida, gakuma titina lpia lau duk acikin gidan.
Shiga sukayi falon mai masifar kyau da tsada, wani mutumi tagani zaune kan kujerun alfarma, masu shegen kyau, bazawuce 45 yrs ba, welcoming dinsu yayi Don dama yasaba da hajiyar,
Kawai cema hajiyar yayi bravo, cewa akayi tamike, tamike saida yagama mata kallon tsab sannan yakira wata budurwa tanuna mata dakinta, shiga akayi da ita dakin, Wanda duk abin bukata akwai Shi aciki, Nan Akace tazauna,dakin tashiga bi da kallo kamar wacce bata tabaganin gidaba.
Shikuwa wani yare sukayi da mutumin sannan tamasa sallama tawuce abunta................
VOTE AND COMMENT
![](https://img.wattpad.com/cover/186057373-288-k635870.jpg)
YOU ARE READING
SAKAMAKO.......THE OUTCOME
Não FicçãoLabarin husna, labari mai cike da darussa masu dinbin yawa, labarine na kaddarar wata yarinya Wanda mahaifinta shine yakashe mahaifiyarta a sanadiyar haka tagudu tabar gidan Dan itama yana barazana da Tata rayuwar, da tafiyarta tagamu da iftilai kal...