36
Not edited
6 years later.
Shekaru sunja, kuma abubuwa dayawa sunfaru, ciki kuwa harda zaman husna gidan yari, rasuwar Dr koko dakuma rasuwar baban bash.
Gyara murya hanan tayi tareda ajiye glass cup dinda ke hannun ta, tana kallon husna da kyau, wanda batafi watanni da dawowa daga gidan yari ba,
"Yanzu Ina so ki shirya komai naki jibizamu bi flight muje Abuja da Abba na ya matsa min da na dawo Aurena yakusa sannan kafin lokacin inason muje kaduna gun Dangin ki."
Dan sauke ajiyar zuciya tayi tace, zaki iya gane gidan hajiyar da kika zauna kuwa Anan legos? Dan gyada tayi tareda cewa zan gane, yawwa to ina so ki shirya ko zuwa gobe sai muje kafin mubar garin ko!, to shikenan barrister nagode sosai.
Dan murmushi tayi tareda cewa bakomai husna ai kin can canci a tausaya miki.
Washegari tinda wuri kowace taga ma shirinta cikin kaya masu kyau, suka kama hanyar gidan hajiya.
Tayi mamakin ganin su sosai kuma tayi farin ciki, tareda tambayar ta Ina murad ai bai kyauta ya watsar da ita,
Kwalla ne suka cika ma husna ido jin an tado mata da tsohon mikin dake a ranta, nan barrister tashiga bata labarin duk abinda yafaru, itama saida tayi kwalla sbda tausayi dakuma rashin jin dadin alamarin,
Nasiha sosai hajiya tama husna tareda da nuna mata ita kalar tata kaddarar kenan kuma ta rungumeta hannu bibbiyu, sannan kuma ta manta komai abinda ya faru.
Sun Dan Jima a gidan hajiya kafin daga karshe suka mata sallama akan samu wuce Amman bazasu sake dawowa Lagos ba, sosai su Amra musamman Amira sukayi kuka, hajiya ta cika su da kudi masu yawa da kayan anfani, haka suka bar gidan tana jin kewar gidan sosai.
Titi Hanan takama tana tsula gudu, ganin ta canza hanya yasa husna ta kalleta alamar Ina zamu Amman Hanan bata tanka mata ba, Adede gate din gidan husna ta Parker, shesshekar kukan husna ne ya karu, tazuba ma gate din ido tana kallonshi babu kiftawa babu abinda take tunawa sai zamantewarsu da murad mai cike da soyyaya, kin shiga tayi da kyar Hanan ta lallabata sukashiga duk abubuwan anfaninta kashewa tayi suka saka su a mota suka kulle gidan suka wuce...
Bayan sunkoma gida da daddare Hanan ta hada duk kayayyakinta masu anfani a jaka wanda zatayi tafiya dasu,
Itakuwa husna da kyar ta iya hada komai nata, a daren ranar batayi bacci ba, jitake komai ya zame mata sabo gal, tasan wannan rabon bazaitaba gogewa a cikin zuciyarta ba, Kara fashewa tayi da kuka ta tuna maganganun murad a cikin kunnuwanta, toshe kunnuwantayi kamar wata zararriya tana birgima a kan gado, tabbas tasan har ta mutu bazata sake samun miji irin murad ba, mutum Mai kirki da hakuri,sanyi hali uwa, uba kuma ga iya madarar soyyaya, acikin daren tayi kuka Wanda bata tabayin irinshiba kamar ranta zaifita daga karshe taba zuciyarta hakuri, tana cewa husna kalar taki kaddarar kenan wannan kuma shine *SAKAMAKON* duk yabar gida da kyar tayi shiru amman bacci saidai barawo.
Tinda asuba ta tashi tashiga bathroom tayi alwala tayi sallah, da kyar ta Idar da sallar don jin kanta take kamar ba nata ba saboda mugun kukan da tasha ga idanuwanta sunyi luhu luhu duk sun kumbure, kwanciya tayi akan abin sallan, nan da nan bacci yayi gaba da ita.
Can cikin barci taji kamar Ana mata magana da kyar ta dago idanunta dasuka rine har bata gani sosai, ta kalle Hanan, ganin tayi Sanye cikin abaya baka tayi kyau sosai hakan yayi mata nunida harta shirya, da sauri ta Mike tana goge idanu tareda kallon agogo ganin 9:30 yasa ta mike da sauri tana nashiga ukku kiyi hakuri inazuwa Dan Allah.
Agaggauce tayi wanka tasaka gown dark blue babu abinda tashafa a fuskarta haka kuma babu abinda taci don tasan kotaci amai zatayi ma, tana fitowa taga Hanan tasa duk ankai kayan mota, itama motar tashiga gidan baya, Hanan kuma na zaune a gidan gaba seat din mai zaman banza sai drivern da zai su Airport daman taxi suka dauka.
Suna sauka Airport ba dadewa bayan an gama musu komai suka shiga jirgi ya tashi zuwa garin Abuja, husna sai kallon window take tana ma Lagos kallon karshe don tasan kila har abada ita da Lagos kuma daman kaddara takawota daga nan kuma tashiga wani tunanin yanzu wata rayuwa zatayi Idan takoma Abuja haka ta dinga tunane tunane har suka sauka Abuja.
Anan ma wata taxi din suka shiga, kalle kalle kawai husna take tana tunanin rayuwar datayi shekara kusan goma da suka shude, gani tayi sun shigo wata unguwa mai kyaun gaske tana ta kallon titi wanda aka ma ado da wasu itatuwa masu kama da na kwakwa.
Adaidai wani katon gate suka faka husna ta sallame me taxi tanufi gate din gidan, mai gadine ya shiga Washe baki yana wata sabon gani Allah y taimaka barrister, murmushi tayi tareda amsawa, nan ya gaisheda husna itama tareda shigo musu da kayan ciki.
Direct mai entrance din gidan Hanan tahufa husna na biye da ita a baya, tayi knocking ba dadewa wa wata yar budurwa wacce bazata wuce 18yrs ba ta rungumeta tana Aunty kece, wallahi munyi kewar sosai, cikeda tsantsaar farin cikin ganin juna suka shiga gaisawa, Anty ki zauna bari na kira momy tafada tazata nufi sama, sai alokacin ta ga husna tace laaa Aunty saiki cemin a tareda bakuwa kike saida ta gaisheda sannan tawuce kiran mumy.
Suna zaune badedewa wata yar babbar mata tafito fuskarta dauke da fara'a, da gudu Hanan ta mike wata karamar yarinya tarungume mumy tana momy I missed u so much, nima nayi missing dinki daughter nan suka shiga gaisawa bayan sungama suka gaisa da husna, Hanan nacewa mumy itace nake baki labarinta ai, Ayya Allah sarki baiwar Allah, Allah y baki ikon cinye jarabawar ki muje kuci abinci.
Zama sukayi dining saida kowace ta cika cikinta sosai sannan suka Mike don shiga daki su huta, har daki momy taraka su cikeda, daga karshe mumy cewa tayi kuhuta nasan akwai gajiya a tattare daku...
Mikewa husna tayi tashiga bathroom don watsa ruwa, kallon tabisu dashi na ban shaawa dan murmusawa tayi tace daman nice nake samun wannan gatan nan, Amman tsarin gidan yamin don suna kaunar Junansu.
Bin dakin taciga ba Dayi tana tunanin kalar zaman dazatayi a gidan.....
It's been a while koh, hmm yanzu zakurinka samun update frequently, saboda muna quarantine, coronavirus tasaka mu zaman banza lol
Please stay home and stay safe I love u all.
MRS ABDOOL.....
Vote and comment
YOU ARE READING
SAKAMAKO.......THE OUTCOME
No FicciónLabarin husna, labari mai cike da darussa masu dinbin yawa, labarine na kaddarar wata yarinya Wanda mahaifinta shine yakashe mahaifiyarta a sanadiyar haka tagudu tabar gidan Dan itama yana barazana da Tata rayuwar, da tafiyarta tagamu da iftilai kal...