sakamako 29

291 22 0
                                    

    29

Tunda wuri yatashi yayi wanka yagama shirinsa yafita, eatry ya nufa yaci breakfast sannan itama yamata take away direct room dinta yanufa Don ancanzamata daki, da sallama yashiga room din kwance ya isketa yana shigowata Mike zaune

Sukuyar da Kai tayi tace Ina kwana, dagowa yayi da murmushi yace lpia klau husna kintashi lpia? Yayajikin naki
Allhamdullah naji sauki saidai wasu pains de kawai to Allah y sawake tace Amin.

Kinyi brush ko daga masa Kai tayi, abincin yazuba mata ya matso yana kokarin kaimata abaki rike spoon din tayi, tace ngode ta karba tacigaba da ci, bayan tagama ya ballo magani yabata tasha, sudanyi fira, sannan yatashi yayi tafiyarsa office.

Kullum yakanzo sosai gashi tafara Sabawa dashi sosai intaga bezoba tadinga damuwa kenan, yanzu sake fira sukeyi sosai da ita yar yana tunanin dama haka take ashe

Satinsu biyu a asibitin ganin tasamu sauki Sosai likita ya sallamesu, bayan yadawo aiki dayamma ya biyo ya dauke duka suttara komai yasata amota suka wuce,

tafiya sukeyi Amma babu wanda yayi ma wani mgna, itade zuciyarta Fal take da tunanin yanzu ita inazataje daga nan kuma zuciyarta fal da fargaba, gani tayi ya tsaya dede wata supermarket cewa yayi tajirasa a mota, yafita kaya yajido mata sosai kayan sawa, hijab,mayafai,cosmetics,underwares Dade sauransu

Bai wani Dade ba saigashi yafito an rakosa da kaya niki niki, boot yabude aka zuba kayan yaja suka wuce, still baice mata komaiba haka itama batace komai ba saima yunwa dake damunta, gani tayi yafaka wani eatery yace fito, zama sukayi kowa yayi ordering Abinda yakeso saida sukaci suka Koshi sannan suka fito

Direct lekki suka wuce gani tayi sunzo wani ubangida mai shegen kyau, dasauri gate man yabude ya shiga da motar, gate man yabude boot yakwashe kaya yashiga dasu, mai gadi mamakine fal a zuciyarsa ganin ogansa yazo da mace Abinda be taba ganiba.

Cimatay yayi mushiga yayi gaba tabishi a sanyaye zuciyarta na mata sake sake, shiga yayi yazauna akan sitters din falon,itama tashigo tazauna duk a takure, jin muryarsa tayi yana cewa kisaki jikin ki ba abinda zanmiki,

Dan murmushi tasake tana yan waigege waigege, kakira matar gidan mana mugaisa,

dagawo yayi  yana murmushi yace aini banida mata

Damm!! Taji gaban ta yafadi, dagowa tayi bakinta fal da tanbayoyi kafin tace wani abu yace amma soon insha Allah, jitayi wani abu yasoketa Dan Danan mood dinta ya canza daure wa tayi tace to Ina iyayenka da yan wanka?

Duk basa nan suna kano, ai ni Dan kanone Amma nan Nike aiki nakanje kano akai akai

Maya fito dake by dat tym of d night ranar Dana bugeki?
Daga Ina kike?
Ina kuma zakije?
Ina iyayenki?
Inane kuke zama?

Tambayoyinsa suka saukarmata kamar aradu a ka, tinda take bawanda yasa labarin, tunani yashigayi sosai

Muryarsa takara ji yana cewa don't tell me what am suspecting is right

Aa wallahi bahaka bane Abinda kake tunani ba shibane

Then how

Kuka tafara tana tausayin kanta

Wai meyasa duk sanda ya tambayeta gameda wacece ita saitafara suka definitely dere is something tausayinta yaji ya dawo kusada ita yakama hannunta yace it's okay, Idan bakisan gyamin kibarsa Amma inkika gyamin kinga sai nasan yanda zan taimakeki ko, dan Allah kidena kukan nan yashiga lallashinta yana gyamata kalamai masu sanyaya zuciya, nanda nan taji zuciyarta tayi sanyi at least yau ansamu me lallshinta she just have to tell him sbda yanzu a mtsayin Dan uwa take kallon shi, share hawayen tayi tace

Sunana Asmau Muhammad kabir.............. nan takwashe duk labarinta tabashi bata boye mishi komai ba, tana gamawa ta kwace dawani kuka mai cike da tausayi da nadama,

kallonsa tayi da jajayen idanunta tancewa wallahi *nayi nadama* wanan shine *sakamakon* dukwani wanda ze bargida don ganin zesamu mafita dana sani danayi zamana ko gurin inna nakoma nasan bazata bari a cutardaniba, yayi matukar tausaya mata yace karki damu insha Allah zan taimaka miki Amma yanzu bari naje sallah indawo,

Daki yanuna mata yace kije kiyi wanka, ki shirya kigama komai kiyi sallah ina dawowa yanzu,

Mikewa tayi tashige dakin shikuma ya wuce masallaci, tsayawa tayi tanata kallon dakin ko ina fes kuma komai sabo dakin ya burgeta matuka, toilet tashiga shima kallo tatsayi komai fari gashi fes kamar kaci abinci a ciki komai nazamani taciro towel dinda ke rataye tadaura ruwan dumi tacika Jacuzzi dashi dama tana ganinshi a film, Maya mayai tagani da sabulao dakuma turarukan wanka kalala, tazuba turaruka kala masau shegen kamshi sannan tashiga, tana gamawa tadauko Maya mayen wanke gashi masu kamshin gaske, tagama komai sannan tafito,

Kayan tashiga budewa nan tayi shafa ba abinda babu tashafa turaruka kalala, takuma bude wata jakar tajawo wata gown Mara nauyi tasaka, tabbude komai Don ganin Abinda ke ciki harda su pant da bra da pad  dauka tayi a kuyace tasaka..............

Vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now