part six

564 36 0
                                    

  06

Matsawa yayi a tunaninshi bazata taba soka masa wukar ba, cikin mugun fushi Don jitake komai zata iya masa a wanann lokacin, Kai tsaye tasoka masa wukar a wuya  baiyi auneba yaji saukar wuka salati ya shiga yi cikin wata irin muguwar azaba yafadi kasa

Wani uban ihuu tasaki tana nashiga ukkuna takallai wukar ta kalli murad kwance male male cikin jini rungumeshi tayi tana darzar kuka kamar Ranta zafita nashiga ukku murad kayi hakuri bada sanina nayiba, Dan Allah katashi kar kamutu, kakokarin magana yake yi to Amma yakasa.

Itakuwa bisola mikewa tayi arude tanufi part dinta tasako kaya ko jakar bata tsaya daukaba tanufo gate aguje ko raufu bata tsaya yima magana ba tayi waje, shikuwa rudewa yayi ganinta arudetake, gudu tadinga kwasa har bata ganin gaban ta kawai sotake tayi escaping dontasan yau ba abinda zehana husna kasheta.

Kowa tagani bangajeshi takeyi tayi gaba mutane sai kallonta sukayi kamar wata mahaukaciya, dede tazo zata tsallake titi wata trailer tayo kanta aguje ta taketa ko motsi bata Karaba ta mutu jini kawai kakegani yana gangara kamar ruwa mutanen sukazo kawo mata dauki Amma rai yayi halinsa, wayar ta aka dauka aka kira mamanta.

Hello yata ya kike sai yau kika tuna dani
Ehmm baita bace pls da wanake magana daga dayan bangaren
Ubanwaye Kai, wannan ba wayar yata bace
To yarki tayi hatsari tarasu. ......

Batakarasa jin Abinda zaceba luuuu ta suma, sai asibiti.

Husna kuka  take kasharban can taji kamar yadena numfashi dasauri ta sake shi takoma baya tana kwalo tulatulan idanuwanta tana kanga kunnenta saitin kirjinshi taji baya motsi, wata razananniyar Kara tasaki tana barkewa dawani sabonkuka, wayar ta ta lalubo tana latsakiran inspector  Sani,
Hello inspector nakashe mijina nashiga ukku
Ehh mekikefadane ganinan zuwa gidan

Tareda yansanda suka shigo gidan ,sukaga abokinsu rashe a cikin jini ko magana basu yimataba, suna realising ya mutu suka dau gawarsa suka saka  a mota, itakuwa ko kala basu cemata ba handcuff suka saka mata ba musu tamika musu hannun,yansanda sukayi gabada ita.

Tinda suka1 isa station ko uhm takicewa sunyi sunyi tayi magana Amma takiyi Don kowa mamakin anya ita ta kashe mijinta kuwa sukeyi, Don kowa yasan muguwar shakuwar dake take tsakaninsu, Amma taki basu dama Don su gudanarda bincike, abubuwan sun cakude masu sosai.

Duk an gama yayatata a kafafen yaďa labarai a tv ne, gidajen radio da sauransu.

Gawarsa aka Kai can kano gun iyayensa tinda suka isa, babarsa kuka take babu kakkautawa sai simbatu take tana ta cuceni takashemin da ni banwani yarda da itabanayi dama  shiya nace bazeauretaba daman ance tsintacciyar mage bata mage ,wallahi murad bashida hayaniya ko fada, gakirki, wallahi mutunne mai sanyin gaske nasan ba Karamin Abu yahadasuba,

Nan su yusuf suka tsaya har saida akayi sadakar ukku sukadawo.

Har lokacin tana kulle a cell,Amma still haryanzu bata magana sunma rasa yanda zasu fara case din Don ita kadai tasan Abinda yafaru , itakuma zatabada labari.

******************

Wata kyakyawar budurwace zaune a wani madedecin falo tana kurbar juice tana kallon television, wani shiri ne taga Ana gabatarwa da sauri ta aje cup din tana sauraron....

A yau ranar laraba ansamu rahoton wata baiwar Allah da ta kashe mijinta takuma dauki waya ta Sanar da yan sanda tafada musu Abinda ta aikata, ayanzu haka tana Nan police station din surulere dake lagas, takuma ki ba yansanda damar yin bincike, Don yau kawanata hudu bata magana. Amma tambayar Anan itace me ya Kai wannan baiwar Allah kashe mijin, Don bincike yanuna, suna zaman lpia da soyyayar gaske da mijin nata.

Mikewa tayi tasaka Vail tanufi police station din Inda husnatake,  sun gaisa da yan sanda tace am Barrister hanan abdulmalik tafada cikin natsuwa nazo ne I want to have chat wit the miss here,ok but saidai kiyi wasting time dinki, but bazatayi magaba, okey no probs let me check on here first, u are free since u insist, Tanks tafada.

Shiga tayi cikin cell tasameta zaune ta zabga tagumi tin tana kwalla har kwallan sun kafe, tasamu gu tazauna tafara magana.

Am barrister hanan Abdulmalik u have d right to be heard and u also have the right to be defended so don't fell any thing am also a woman I know how it fell, so fell free and talk to me, itade husna Banda ido babu Abinda take binta dashi , sai kwalla dake ta kwarara,duk wasu kalaman kwantar da hankali hanan tafada mata, tayi iyakar kokarinta Amma takiyi mata magana, ahaka de tamike akan zata dawo nan bada dadewa ba.

VOTE AND COMMENT

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now