sakamako 28

298 21 0
                                    


   28

Kallonta yakeyi ciki rashin fahimtar me take fada, kwantar da murya yayi yace kinga saurara kiji asibiti kike bakida ne, ni ba ma cuci bane taimakon ki zanyi

Jin an ambaci taimako yasa ta Dena ihun datakeyi tana kallon shi, komawa tayi karshen gado a Dan tsorace tanacewa to Kai waye

Murmushi yayi yace duk zan amsa miki waddan Tambayoyin naki amma sakin warke kinga baki gama warkewa ba Amma Abinda nikeso kisaka ranki shine niba macucibane kuma bazan cutar dake don  haka ki kwantarda hankalin kinji bari naje na siyomiki wani abu kici Sanan in siya Miki magungunanki

mikewa yayi yanufi kofa harze fita yaji muryarta tana cewa to a Ina kaganni mekuma ya kawo ni asibiti?

dariya ma tabashi Don hakan yanuna haryanzu a tsorace take be juyoba yace zan amsamiki wanan tambayar Amma sai kin ci abinci kinsha magani baijira  cewartaba yayi gaba.

Bayansa tabi da kallo tana tunanin waye shi kuma a Ina yaganta, komawa tayi ta kwanta wata muguwar yunwa na cin cikinta,

Daga asibitin direct eatery yawuce abinci yamata take away sannan yasiya ruwa da kuma hollandia milk, bayan yafito ya tsaya yasimata fruit sbda tana bukatarsu, daga Nan yawuce super market yasiyo mata kayan sawa da kayan amfani irinsu hijab abinsallah, brush, Macline, da takaimi, sabulunwanka da sauransu saida yatabbar da yasiyo komai sannan yabiya yayi sallar magrib Sanan yakoma.

Yadda yabarta haka ya dawo ya isketa shiga cikin dakin yayi ya mika mata komai karba tayi tana kallon shi cewa yayi kitashiyi wanka, kiyi brush, kiyi sallah kafin nadawo, zanje masallaci nima nayi sallah kinji ko gyda masa kai tayi

Harze fita yakoma yahada mata ruwan wanka yakira nurse tacire mata drip din sannan kuma ta taimaka mata.

Nurse din takaita bathroom tayi wanka tayi brush sannan tafito, cikin kayan taduba tamika mata gawn Mara nauyi tasaka tahau sallaya Don gabatarda sallah tana idarwa tace ma nurse din zata iya tafiya

ta Dade tana adduoi, tana zaune kan sallayar saigashi yadawo kujera yaja ya zauna kusa da gadon bata cire hijab dinba bayan takoma kan gado, abinci yazuba mata da kanshi ya mika mata, yakuma tsiyayo hollandia ya bata, tadan ci sosai daga karshe ta mika masa sauran ajiyewa yayi kasa, jiyayi  tace cikin murya mai laushi kaito bakaciba, murmushi yayi yadago yana kallonta gani yayi tana wasa da yasunta yace ai ni nakoshi..

Magugunan ya ballo ya mika mata, karba tayi yakuma mika mata ruwa, Shan maganin tayi ta mika masa sauran ya ajeyi...

Dagowa yayi yana kallonta na yan mintuna Sanan yace yaya sunanki?

kaitsaye tace masa Asmau,

Jinjina Kai yayi yace husna kenan, yace kwanaki hudu dasuka wuce nadawo aiki cikin dare ana ruwa na bankeki bansaniba, yaukwananki hudu a asibiti sai yaukika farfado, Don haka yanzu kimin kwatancen gidanku Dan nasan iyayen na can suna nemanki

Shiru tayi tana tausayin kanta Dan Danan kwalla suka cika mata ido

Jin shirun yayi yawa yasa yadago yana kallonta, kwalla yagani a idonta yace subuhannallah no bance kimin kukaba tambayar kawai nakeyi to kiyi hakuri Idan nabata miki rai

Ganin bata son zancen yasa yashare shima yadanjima yana mata fira, sai dayaga tayi bacci sannan ya lullube ta yarage sanyin AC dankin yawuce gida

Tinda yakoma gida yake tunaninta to meyasata kuka sbda ya tambayeta iyayenta, kalamta na ranar yafado masa Inda takecewa ni marainiya ce... jinjana Kai yayi yace maybe shiyasa take kuka, cike yake da tambayayoyi akanta Amma wazai amsa masa, cikin ransa yace ko kuma bari tawanke I need to hear her story Don nasan yadda zantaimaka mata,

juyawa yayi yaja blanket yarufe kansa lumshe ido yayi zuciyarsa cike da tuninta har bacci yadaukeshi.......

Niko nace ayi bacci lpia

Vote and comment 

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now