sakamako 25

261 18 0
                                    

  *25*

"Yan matane suka kawo mata abinci lafiyayye tareda cewa, welcom to Dr bilyaminu kokos kingdom, sannan sukafito.

"Dr kokone yashigo Don yimata tambayoyi.......
Ke yaya sunanki,tace Mimie
Shekaraki nawa tace 18
Haka yadinga yimata tambayayoyi tana bashi amsa.

"At last danna kiran hajiya Zainb yayi wacce takawo Mimie akan wai Mimie is still young sai tadan kara girma.

"Mimie de duk ta rude Don batasan me tazoyi a gidan ba kuma bata ga alamar mata a gidan ba gashi tinda matarnan takara gaba bata Kara ganinta ba.

"Da kadaici y ishe ta tamike taje dakin dake kusa da ita tayi knocking wata budurwa ce tabude mata, shiga tayi sukayi introducing kansu, Mimie ce ta tambaya tace wai mezamuyi agidannane, hmmm waccan tace au wai baki saniba, aa inafa nasani, to ai yanzu maza zaakawo su kwanta da ko wacce cikinmu, sai yayita rainon cikin in muka haihu sai ya sayarda jaririn, sayarwa kuma tafada a tsorace,

" kuma kisan me duk wani Abinda kike bukata zaa bakishi, tindaga kan abinci, Kula da lpia ke komai duk yimake zaayi,tabi jam gaba da gaban ta, ai zama gidan nan be ganniba dole nasan abinyi tafada a Ranta,Amma a zahiri sallama tayi tace baritaje dakinta, sallama sukayi tafito, tanafito taga Dr koko yana cinikin jariri da wata mata har ma sunsiya an bashi kudin.

"A tsorace ta koma daki tafara safa da marwa tana cewa wannan wace irin duniya ce, no wonder Naga gida kamar a lahira ashe kudin haramne, Amma wannan mutumi baida imani, gashi duk gidan nan zagaye yake da cctv camera da kuma security ba hanyar fita, yazama dole na nemo mafita.

"Ahaka tadinga zuwa gurin naibo dinta suna fira gashi harsunyi wata daya a gidan, kuma Kula sosai ake basu,

"To yau layi yazo kan naibo din Mimie tanaji tana gani aka dauketa aka fita da ita, kuka tadinga sharba kamar Ranta zefita, da sand'a tabisu abaya Don ganin Inda zaa Kaita, wani daki suka shiga da ita, taga wasu katti tube babu riga, sunyi ciki da ita wani daga cikinsu ya shiga babu Abinda Mimie tajiyo inbanda ihunta, salati Mimie ta saki, tazauna gun tana cewa shikenan sungama, tanajin motsin tafiya tayi sauri tayi bayan daki, saura kadan tasaki fitsari sbda tsoro Dan tasan Ana ganinta itace next kawai, yana wucewa da dugu tafada daki tana kuka ranar yini tayi tana kuka abunda tagani yana dawo mata.

"Yanzu batada abokin fira sai zaman daki itakadai,jin environment yayi shiru yasa tafito ta nufi wani daki, Inda taga mutane na yawanshiga, matane tagani kwance, da cikuna ajikin su wasu kuma sun haihu, gakuma wani daki daban jariraine kala kala aciki, mutane sai ciniki sukeyi kamar wani gwanjo.

"Dafe kirji tayi kamar idonta zefito ta lallaba takoma dakinta, tasan definitely itama watarana nan zaa kawota, to miye abinyi, shin wai hukuma batasan da zaman irin waddanan azzuluman ba? Nima ma De nace oho Mimie bansaniba. Ranar har firgita taringa cikin dare saboda tsananin tsoro gani take kamar itama zaazo a tafi da ita Inda akakai naibonta.

VOTE AND COMMENT

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now