sakamako 08

444 32 0
                                    

   
  08

Saida yamma lis suka koma gida Wanda hakan ba Karamin Balai ya haddasamata ba, Dan duka ranar tashashi, harta gode Allah Itako husna Banda kuka babu Abinda takeyi.

Washegari saida husna te mata gashi sbda duk ya kumburamata Jiki, tanayi tana mamakin hali irinna wannan mutum, lokaci guda wani mugun tsanar shi takamata

Umma kinga bazamu zauna yunwa takashemuba kinga fa Shi yana cin abincin Shi, ni a ganina kisamomin Inda zanrinka yin aiki, aringa biyana sai muringa anfani da abincin.

To makaratarfa kidena kome, babuwani aikin dazakiyi ban yardaba zandeje insamu ko wankau ne inrinka yi.

To umma Amma wallahi sai Allah yasaka mana.

Mikewa tayi tanufi gidan su farida Dan tadan mance Abinda ke damunta

Tanafita uwarta ta rushe da kuka saida tayi me isarta,sannan tayi shiru tana tunanin rayuwar tana kuma tausayama yarta duk ranar daakace bata Nan.

Mikewa tayi Jiki ba kwari tafere sauran yar doyar dake gidan tace Sunci ko Maida yajine, kafin wannan jarabbaben ya dawo.

Ranar yagama yawansa yadawo a make yana tangadi,

Dakinsa ya shiga yana ta dube dube duk ya birkita dakin, yafito yancewa

Ke Ina kudina Dana ajiye,

Tace kudi kuma, nifa banga kudinka ba nida ko dakin bana shiga, kilan de ka kashe kamanta.

Ke Don uwarki dandanan yafara jibgarta dama sanadi yake nema,

dagudu husna takama janyeshi tana karka ka shemin uwa mugu kawai, kadena tafada tana kuka, juyowa yayi ya hankadeta yana karyaki zanyi shegiya nine mugu, ya koma kanta naushe yakaimata a hanci, Dan Danan jini yabarke, indo naganinhaka ta Mike adaddafe ta jijjiga yarta tana shikenan ya ka shemin ýa banyafema ba, kuma allah sai yayi mana hisabi.

Dagudu ta rarimi hijab ta shiga gidan su farida, daukar husna akai akasa a mota yayansu ya ja suka wuce asibitin.

Emergency aka Kaita Dan Danan sukamata treatment jinin yatsaya, yayan farida ya Abdul shine ya biya duk bills din.

Yacema maman husna, nizan wuce Allah y bata lpia, Amin nagode Abdullahi Allah y yi albarka,

Kwanasu hudu asibitin kuma tawarke saidai sauran ciwon dayajimata sune basu Ida warkewa ba,kullum tare suke yini da farida, mamanta ma tazo saudaya, shima lado tinda yazo sau daya baikara zuwa ba.

Ranarda aka sallamesu, ya Abdul yazo yamaidasu gida, siyayya sosai yayi masu,su fruit da drinks da sauransu, itakuwa ummy (maman farida) lafiyyayen abinci tayimusu da farfesun naman rago.

Tinranda ya yimata wannan taasar baikara kawana gida ba you harkusan sati, indo kuwa ko damuwa batayiba Don hakan yafimata kwanciyar hankali.

Umma wai auren soyyaya kukayi da baba kuwa,
Dum taji tambayar yar Tata,Don bata taba zaton zatayi mata wannan tambayarba.

Meyasa kikemin irin wannan tanbayan husna

To ai umma Naga yanzu ya tsanaki, nima kuma baya sona

Bahaka bane husna yanasonki, shinefa babanki,kuma yanasona.

Wallahi baya sonki inde yana sonki baze dinga dukanki ba

Toya isa haka, kuma dama Inason miki magana, babu ruwanki da Abinda babanki yakemin kinji, kinga dakika sa baki, gashi haryakusa hallakaminke, kidena kinga ke kadai kika ragemin inkika mutu bansan yadda zanyi ba,

ai bazan mutuba umma Ina nan tare dake.

To yanzu tashi kici abinci zubowa tayi a plate tayi feeding dinta taci takoshi Sannan itama taci.

Kwana biyu da dawowa saiga lado ya dawo, ranar ma kamar yadda yasaba sai da ya jibgeta, husna taji warning dinda mamanta tamata nasaka baki, saida yagama yayi ficewarsa,

fittarsa kenan saiga kawu Abu kanin indo yashigo dasauri ta goge hawayen,  tareda kirkiro murmushi

Sun gaisa yake tambayarta ko lpia tace masa lpia klau bawata matsala, husna ta bude baki zatayi magana, Indo ta watsamata harara bashiri tayi shuru,

Yamika yabasu Dan Abinda yakawo Musu suka karba sunata godia, indo tace ya iya takaraji

Yace tawarke tinda baki kara zuwa kika gaishe ta ba, zanzo insha Allahu, kozuwa jibi kagaisheta Dan Allah .

Ok zataji Nina wuce, agasheda lado Dan Allah, ya Mike yayi waje....

Don't forget to vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now