page 1⃣1⃣
Yarima suhail bayan gimbiya sumayya ta fita dafe kansa yayi cike da jin haushin sumayya da take nema taraina masa wayau, watau ta ma san ya yi missing d'inta? to kenan ita batayi missing d'insaba tana nufin taimakonsa ma zatayi. tabbas yasan ya yi *BABBAN KUSKURE* da ya amince ya aureta domin ko kad'an batasan minene aureba
tsaki yaja yace Allah yashirya sannan yakoma yakwanta yana mamakin halin sumayya.Sumayya a fusace takoma d'akinta cike da bak'in cikin wulak'ancin da Yarima yayi mata, ace kamarta daga ta je tataimaka masa shine yakoreta
tana shiga bedroom tamurza key nan tafad'a saman gado tafara kuka.tun daga ranar aka koma 'yar gidan jiya ba mai kula d'an uwansa kowa harkar gabansa yakeyi
_______________
A 6angaren su zarah har yanzu babu abinda yasauya daga halaiyar 'yan gidansu, malam bello yanzu islamiyya kawai suke samu suna had'uwa
yauma bayan ta taso daga islamiyya tafiya take a nutse kanta sadde a k'asa daga bayanta taji ana mata sallama kamar ba zata amsaba sai kuma chan ta amsa batare da ta tsayaba mutumin cigaba yayi da binta yace dan Allah 'yan mata kitsaya kisaurareni mana,
Zarah ahankali tad'ago kai takalli mutumin da bazai gaza shekaru ashirin da biyarba, k'ara d'aure fuskarta tayi tace lafiya malam kaketa bina?
Murmushi mutumin yayi yace ni dai sunana hamza ina zama chan waccan rumfar mai kayan miyar kullum ina ganin giftawarki idan kin dawo islamiyya kuma gaskiya ina sonki saisa natunkareki nafad'a miki domin insamu matsugunni a zuciyanki wlh ina sonki, ina k'aunarki ina begenki, wlh indai baki amshi tayin soyayya taba zan iya mutuwa.
zarah baki tasaki tana kallonsa maganganunsa har sukaso subata dariya tadake tace ka gama?
hamza yace eh nagama ina dai son inji daga gareki domin kema nasan nayi miki
Zarah d'an murmushi tayi tace nagode sosai da tayinka ammah saidai kayi hak'uri domin ina da wanda nake......
katseta hamza yayi yace dakata malama ai daman abinda naji ma tsoro kenan saisa tun tuni nak'i tunkararki da maganar ammah wlh bakiyimin adalciba danma kin samu ance ana sonki wanene anguwarnan bai san halin gidankuba waye baisan ku 'yan iska bane, dan ma kin samu antaimaka ance ana sonki.
zarah murmushin takaici tayi sannan tace toh nagode kuma so ne bazan ta6a sonkaba, tana gama fad'in haka tawuce tabarsa tana jinsa yana ta yada mata bak'ak'en maganganu ammah tasharesa cikin ranta ko wani irin abune yatokare mata mak'oshi tabbas tasan abinda bawan Allahn nan yafad'a gaskiyane a game da gidansu, ahaka ta isa gida da tunani iri-iri cikin ranta.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Rauda yau kasancewar ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazza6i kwance tawuni bata iya komai, da kaganta kasan tana jin jiki tuni ta fita hayyacinta saboda Amai da take yawan yi
su mama sun tusata a gaba kowa tausayinta yakeji ganin irin wahalar da take sha kallonsu kawai zakayi kasan suna cikin matsanancin tashin hankali.
zarah ko kuka kawai takeyi tana rik'e da hannun yayartata ko kad'an bata yarda tamatsa daga kusa da itaba domin ita tana da k'wallafar 'yan uwanta.
mama ce tahad'o mata ruwan bunu tare da indomie matsa mata sukayi sai taci, ba dan tasoba tadaure tamik'e dakyar tayi loma ukku shima dan taga hankalin dangin nata a tashe, kafin kace mi dagudu tamik'e tanufi toilet tadinga kwarara amai dasauri zarah tabita tarik'eta tana mata sannu har saida tagama, Aysha ce tad'ebo musu ruwa a buta nan zarah tataimaka mata tawanke jikinta sannan suka fito takoma takwanta.
