👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑*PAGE* 4⃣4⃣
*BAYAN SATI 'DAYA*
Zarah fitowa tayi daga part d'inta tanufi part d'in yarima dan tagyara mai kasancewar tun da girki yakoma hannun sumayya bata k'ara sashi a idoba dan ko da girki yadawo kanta batabi ta kansaba daurewa kawai take tana kwana part d'inta ammah duk wani tunani da ruhinta yana wajen yarima, ahaka tacinye kwanakinta, har sumayya tayi nata, duka baifi sau ukku sukayi waya da shi ba shima ko da ya kira toh jikinta zai tambaya sai yakashe wayar.
Lokacin da ta isa part d'insa wani irin nishad'i taji, ahankali tatura bedroom d'insa tashiga, saida gabanta yafad'i ganinsa tayi d'aure da towel da alamu daga wanka yafito, shima yarima ido yazuba mata har ta iso inda yake fuskarta d'auke da murmushi da mamakinsa sai ji yayi ta fad'a jikinsa ta rungumesa, shi kansa saida yalumshe ido tare da yin ajiyar zuciya, ahankali yakai hannu shima yarungumeta.
K'ara shigewa jikinsa tayi ahankali tace baby na yi missing d'inka sosai, shuru yarima yayi sannan chan yace banga alamar hakanba,
'Dago kai tayi takalli cikin idonsa sannan tace saboda me kace haka?Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, shima tsura mata ido yayi sai chan yakai hannunsa yazame mata veil d'in da tayafa, d'an janye jikinta tayi daga nasa, k'irjinta yazuba ma ido sai daga baya yakai hannu yashafi k'ashin wuyanta sannan yamaida kallonsa ga fuskarta yace ammah bakya cin abinci ko?
Zarah murmushi tayi sannan tace me kagani?
Idanunsa yamaida ga k'ashin wuyan sannan yace wannan k'ashin fa?
Kallonsa take koda ta san maganarsa gaskiya ce ba wani iya cin abincin kirki takeba yanzu daurewa kawai take tana d'ancin kad'an shima ba kowane abinci ba, turo baki Zarah tayi cikin shagwa6a tace ina ci man.Bakinta yazuba ma ido yana kallon yadda take maganar, fari Zarah tayi masa da ido sannan tace ya dai?
Yarima janyeta yayi daga jikinsa a kasalance yanufi wajen mirror yad'auki lotion yafara shafawa, bai ankaraba sai jin zarah yayi bayansa ta rungumesa, maida idanuwansa yayi yalumshe, zarah ma kwantar da kanta tayi a bayansa fuskarta d'auke da murmushi sai chan tajanye jikinta takai hannu tad'ebo mai d'in tana shafa mai a baya cikin wani irin salo, rikitasa takusan yi ganin haka yasa yajanye jikinsa yace kibarshi zan shafa.Murmushi zarah tayi sannan tace toh, wajen wardrobe d'insa tanufa tabud'e tad'auko masa manyan kaya, galila maroon colour kasancewar tana son colour d'in, zuwa tayi tafeshe kayan da perform sannan takalli yarima da yake tsaye yana kallonta,
Murmushi tayi sannan tataka ta isa inda yake tamik'a mai tace ga kayan,
Shima d'an guntun murmushi yayi sannan yakar6a ahankali yace nagode.Zarah juya baya tayi dan yasa kayan, ganin haka yasa yarima yayi murmushi sannan yashiga sawa saida tatabbatar da ya gama sannan tajuyo takallesa, zuba mai ido tayi lokacin da yake sanya hula a kansa ya yi mata gwanin kyau, sonsa ne yake fizgarta ji take kamar tarungumesa.
Yarima ma kallonta yayi sannan yace ya dai, Kallon fa?
Ajiyar zuwa ta aje sannan tace ka yi kyau.
Murmushi yayi tare da d'aura hannunsa saman kumatunta sannan yace na gode, sai nadawo.Shafa hannun nasa tayi da yake saman kumatunta sannan ahankali tace adawo lafiya.
Zare hannunsa yayi yawuce yabud'e k'ofa zai fita, tsaye tayi tana kallonsa cike da sonsa har yafita, ta dad'e tsaye tana kallon k'ofar chan tayi murmushi tashiga gyara mai room d'insa.
Bayan ta gama part d'inta takoma duk abinda zatayi tunanin yarima kawai yake fad'o mata a rai, ita kanta abin har mamaki yake bata ta rasa wane irin so takeyi masa.
