✔
*PAGE* 4⃣2⃣
Bayan kwana d'aya zarah ce wajen wardrobe d'inta tana jera kayanta, bud'e k'ofar da akayine yasa tajuya takallesa wani irin sanyi taji a ranta dan rabonta da tasakashi idonta kwana biyu kenan, ahankali tajanye idonta daga kallonsa tacigaba da gyara kayanta.
Yarima jinginewa yayi jikin k'ofar tare da zuba mata ido yana kallonta zarah har tatsargu da kallon da yakemata, ahankali tasaci kallonsa karaf suka had'a ido, wata irin kunyace taji ta kamata,
Ina wuni? tace chan cikin mak'oshinta,
Yarima har a lokacin kallonta yake ahankali yace lafiya, ya k'arfin jikin?
Alhmdllh, na warke, cewar zarah.
Eh naga alama tunda har kina iya takawa, Allah yak'ara sauk'i.
Ameen nagode sosai.Shuru sukayi ba wanda yak'ara magana sai chan yarima yace akwai abinda kike buk'ata?
Girgiza kai zarah tayi sannan tamaida wardrobe d'inta tarufe tawuce taje tazauna saman gadonta, har a lokacin yarima binta yake da kallo sai kuma chan yace ohk, Allah yak'ara sauk'i, yana fad'in haka yawuce yafita daga d'akin.Zarah rakasa tayi da ido har yafita sannan taja dogon numfashi tare da jawo wayarta takira su mama dan sugaisa.
Koda ranar girkinta yazo part d'inta tayi kwanciyarta bata lek'asaba wai ita fushi take tunda yayi kwana biyu baizo yadubata ba, yarima tun yanasa ran zatazo ammah bata zo ba daga k'arshe saidai yahak'ura yayi baccinsa.
Da safe taso tahad'a mai breakfast ammah tayi late bata farkaba har yafita saida taji ba dad'i dan haka taje tagyara masa part d'insa tass sannan tadawo tashiga kitchen dan tad'aura lunch.
Wajen k'arfe ukku tagama shirinta tafito tanufi part d'insa dan tasan lokacin ya dawo, tana shiga tsaye tayi bakin k'ofa da mamaki tabi sumayya da kallo ta tisa yarima gaba tana mai labari cike da farin cikin kud'in da tarok'esa yabata shidai gabad'aya hankalinsa ba wajenta yakeba yana wajen wayarsa da yake dannawa yana wani research, ganin zarah yasa takwantar da kanta a kafad'ansa tana murmushi,
Wani irin kishi ne yakama zarah cikin zuciyanta tace ashe yau za'ayita, wucewa tayi tafara takawa nan tasaki wata irin k'ara, ba yarimaba hatta ita kanta sumayya saida tatsorata, yarima baisan lokacin da yature sumayya daga jikinsa yamik'eba yanufi wajen zarah.
Rik'ota yayi a rud'e yace meyasameki ba dai k'afarba,
Zarah saman k'irjinsa tafad'a tare da sakin kukan shagwa6a, nan yarima ya ida rikicewa yace ya akayi ne?
K'ara shigewa tayi jikinsa sannan tace k'afarce naji ta d'an min zafi,
Wani irin ajiyan zuciya yarima yasafke sannan yace sannu muje induba miki
'Dago kai zarah tayi takallesa tace kar kadamu yanzu ta daina muje kayi lunch nasan ka kwaso yunwa.
Sumayya sakin baki tayi tana kallonsu ita ba abinda zarah tayibane yabata mamaki, ganin yadda yarima yarikice mata abinda ita bai ta6ayiba akanta.Shi kansa yarima sai daga baya yafara jin wani iri, janye zarah yayi daga jikinsa yawuce yashige bedroom d'insa.
Sumayya kamar daman jira take yana shigewa tamik'e cike da 6acin rai tace ma zarah ke k'aramar karuwa wlh kinyi kad'an baki isa kizo kice zakiyi ma mijina kissa ba agabana, munafukar banza 'yar talakkawa.
Murmushi zarah tayi cikin rashin damuwa tace Aunty sumayya kenan ai nad'auka koma minayi akan mijina daidaine tunda yau ranar girkina ce dan haka ni kinga ma wucewata kihuta lafiya 'yar masu kud'i,
Nan sumayya ta ida k'ulewa tace ke har kin isa kice mijinki bayan tare dashi kikazo kika tarar da ni?
Zarah cikin sauri tanufi bedroom d'in yarima tana Murmushi saida tabud'e k'ofar sannan tace am idan kin fita kija mana k'ofar, tana fad'in haka tamaida k'ofar tarufe.Sumayya k'arshen k'ulewa ta k'ule ji take kamar tad'aura hannu saman ka tafasa ihu saboda takaici yacikin sauri tafita tabar d'akin cike da tsanar zarah dan ji take ko wuk'a aka bata zata iya da6a mata.
Yarima tunda yashiga bedroom d'in zama yayi saman bed d'insa tare da dafe kansa cike da mamakin kansa,
Zarah tsaye tayi tana kallonsa sannan chan tataka ahankali tanufi inda yake daga gefensa tazauna ganin alamun tunani yake yasa takai hannu tadafa kafad'arsa.
