*PAGE* 3⃣5⃣
Zarah a ranar d'akinta tawuni ko nan da wajen part d'inta bata fitaba breakfast ma kasawa tayi duk sai tadinga jin badad'i ganin yadda suka rabu da yarima, waya kawai take da 'yan gidansu tana samun sauk'in kad'aici, cheque d'in da yabata cikin wardrobe d'inta tasaka shi.
kad'an kad'an taduba waya taga ko yarima zai kirata ammah shuru itakuma tana tsoron kiransa gudun kar yak'i d'aukar wayarta.gimbiya sumayya koda Yarima yafita wayarta tacigaba da yi nan take shaida ma zinat Yarima yayi tafiya,
murmushi zinat tayi tace lallai baby kice zaki huta dayawa,
hmm wane hutu wannan 'yar matsiyatan tazo ta hanani inwala,
dariya zinat tayi tace haba baby waike meyasa kike damuwa da wannan gajar ai nad'auka kin wuce ajinta kibarta ai dole tafita tabarmiki gida,murmushin jin dad'i sumayya tayi tace baby saisa nake k'ara sonki, yanzu dai yaushe zaki zo min kinfa kwana biyu baki lek'oniba tun kan ayimin kishiya rabonki da ni kodai yanzu kin samu wacce tafini? .
dariya zinat tayi tace kirufan asiri banda wadda tafiki kuma baza'a ta6a yintaba yanzu dai kishirya gobe zan shigo garin.
cikin sauri sumayya tatashi daga kishingid'en da take tace Allah baby da gaske kike?
hmm toh nata6a yi miki irin wannan wasan? tunda nace zanzo ai zanzo yanzun haka bari kiga inje inyi visa.
cike da jin dad'i sumayya tace gaskiya naji dad'i kuma nagode sosai baby Allah yakaimu goben ni wlh ji nake kamar injawo goben tayi.
dariya zinat tayi tace baby kin cika zumud'i ko inzo da Alh jamilu.
chab wlh zinat kirufa min asiri dan ko yazo bazai samu ganinaba kinsan na fad'a miki bayan Yarima bana jin akwai wani namiji da zan amince ink'ara amince mawa tunda ya sameni kafin inyi aure ai shikenan.
dariya zinat tayi tace kedai har yanzu kina nan akan bakanki yanzu dai sai goben.
sumayya dariya tayi tace toh baby Allah yakaimu
zinat tace Ameen, nan sukayi sallama suka kashe wayar,
sumayya dad'i kawai takeji da zuwan da zinat zatayiYarima ko da suka isa india wajen 2pm motoci aka turo suka d'aukesu aka kaisu masaukinsu hotel ne aka kama musu mai kyau da tsada kowa 1 room, bayan ya yi wanka ya shirya abincin da aka kawo masane yaci sannan yakira su memartaba yashaida musu sun safka lafiya, yana gama wayar kashe wayoyinsa yayi gaba d'ayansu yakwanta dan yahuta.
bayan sallar la'asar knocking d'in da akeyi masane yasa yafarka ahankali yasafko daga saman gadon yaje yabud'e,
Dr khalil ne yashigo yana murmushi yace a'ah ranka yadad'e badai bacci kayiba?
yarima batare da yayi maganaba yawuce yashiga toilet, ganin haka yasa Dr khalil yasamu waje yazauna.bayan minti goma yarima yafito daga wanka, saida yasa kaya sannan yayi sallar la'asar.
bayan ya gama kallon Dr khalil yayi da yake ta waya da matarsa, tsaki yaja yamik'e yaje yabud'e freezer yad'auko multina sannan yakoma yazauna yabud'e yafara sha.bayan Dr khalil yagama wayar kallonsa yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace ranka yadad'e yakamata kazo muje suna nemanmu fa yanzu za'ayi meeting.
yarima saida yakur6i multina sannan yace nifa a yanzu babu inda zanje dan ban gama hutawaba.
da mamaki Dr khalil yake kallonsa yace ranka yadad'e saikace wanda yayi tafiyar mota? ta fa flight mukazo kaga ai bawata gajiya bace sosai kuma kaine shugabanmu kaga baidace ace bakajeba.
yarima kwantawa yayi saman 3 seater sannan yace nidai nagama maganata babu inda zanje yau sai dai gobe koma dai mekenan kafad'a ma Dr rohan ina buk'atar inhuta, yana fad'in haka yamaida idanuwansa yalumshe.ganin haka yasa Dr khalil yamik'e yace toh shikenan ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi.
zarah da dare kwance take ta kasa bacci ita kanta tarasa dalilin da yasa hakan daga k'arshe dai tad'auka cewa saboda yarima ya tafi yana fushi da itane.
wayarta tad'auko talalubo number d'in yarima ido tazuba ma number d'in tanaso tayi dialing ammah takasa, saida tayi kusan minti biyar sannan daga k'arshe tayi dialing.
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)